Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya
Published: 27th, July 2025 GMT
A baya-bayan nan Robert Tarjan, Ba’amurke masanin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, wanda ya taba lashe lambar yabo ta “Turing”, ya ce Sin ta kafa tsarin bunkasa ilimin kimiyya a matakin farko, a matsayin dabara ta tsawon lokaci da kasar ke baiwa fifiko, kuma hakan abu ne mai matukar ban sha’awa. Kazalika, a halin yanzu, Sin ta cimma manyan nasarori, yayin da a gaba kuma, ake sa ran ganin karin ci gaba da kasar za ta cimma.
Tarjan wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kafar CMG ta Sin, ya ce a matakan ingiza ci gaban basirar AI, Sin na da manyan damammakin takara, wadanda suka hada da dagewa wajen cimma burika na tsawon lokaci, da tsarin bayar da ilimin kimiyya da fasahohi, da fannonin aikin injiniya da lissafi, da ma yawan dalibai masu matukar sha’awar nazarin fannonin kimiyya da fasaha. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.