Jakadan Iran A MDD Ya Jaddada Kawo Karshen Takunkumin Amurka Kan Kasar Cuba
Published: 29th, October 2025 GMT
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Cuba nan take
Jakadan Iran kuma Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da aka sanya wa Cuba nan take ba tare da wani sharaɗi ba.
Irawani ya jaddada a ranar Talata, a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya da aka keɓe don tattauna ɗage takunkumin Amurka kan Cuba, cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ƙi amincewa da manufofin bangare guda na matakan tilastawa da Amurka ta daukan kan ƙasashe masu ‘yancin kai.
Jakadan Iran ya nuna cewa: Waɗannan manufofin bangare guda sun saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, sun dogara ne akan girman kai da rashin haɗin kai, suna kawo cikas ga haɗin kan ƙasa da ƙasa, suna kawo cikas ga tsarin duniya, kuma suna lalata ruhin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya. Ya jaddada cewa waɗannan matakan suna da mummunan tasiri ga ƙoƙarin inganta zaman lafiya, a yanki da kuma a duniya baki ɗaya, kuma suna zama babban cikas ga gina duniya mai karko da adalci, wanda yake da mahimmanci don cimma ci gaba mai ɗorewa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jami’ar MDD Ta Musamman A Falasdinu Ta Soki Shirin Trump Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 29, 2025 Sojojin Isra’ila Na Kai Hare-Hare Kan Gaza A Matsayin Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 29, 2025 Larijani: Dangantakar Iran da Pakistan na iya komawa babban hadin gwiwa a tsakaninsu October 29, 2025 Iraki: Al-Sudani ya kirayi Irakawa da suka kare kundin tsarin Mulki ta hanyar fitowa zabe October 29, 2025 Abiy Ahmed: Habasha na bukatar sulhu kan rikicin teku tsakaninta da Eritrea October 29, 2025 Hare-haren Isra’ila Sun Kashe Mutane fiye da 60 a Gaza October 29, 2025 Senegal ta sake gano wasu shaidu kan kisan gillar da aka yi a lokacin mulkin mallaka October 29, 2025 An bude taron ministocin cikin gida na kungiyar ECO October 28, 2025 Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku a Yammacin Kogin Jordan October 28, 2025 Hamas : Netanyahu Yana kokarin wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta October 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya Jakadan Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannun kan yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu
Kasashen Iran da Kazakhstan sun sanya hannu kan yarjeniyoyi da da dama na hadin gwiwa a tsakaninsu a wani muhimmin mataki na karfafa dangantaka a tsakaninsu.
A wani biki da shugaban Iran Massoud Pezeshkian da takwaransa na Kazakhstan, Kassym-Jomart Tokayev suka halarta, manyan jami’ai daga kasashen biyu sun rattaba kan takardun fahimtar juna 14 tsakaninsu da suka shafi sufuri da jigilar kayayyaki, al’adu, fannin shari’a, kiwon lafiya, da kuma hadin gwiwar diflomasiyya da kafofin watsa labarai.
Shugabannin sun kuma sanya hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa da ke tabbatar da alkawarinsu na zurfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu
An cimma wannan ne a yayin ziyartar da shugaban kasar Iran ya kai a Astana tare da rakiyar wata babbar tawaga.
Mr. Pezeshkian ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun nuna babban mataki kuma mai mahimmanci wajen karfafa dangantakar ƙasashen biyu.
Ya bayyana kyakkyawan fata game da kudurin Tehran da Astana na habaka ciniki da zuba jari zuwa babban mataki.
Shugaban Iran ya jaddada muhimmancin da Iran ke bai wa dangantakarta da makwabtanta.
Bayan ziyararsa zuwa Kazakhstan, shugaban Iran zai nufi kasar Turkmenistan, inda za a gudanar da taron zaman lafiya na kasa da kasa tare da halartar shugabannin kasashe da dama.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan December 11, 2025 Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci