Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki
Published: 30th, October 2025 GMT
Zhai Kun, mataimakin shugaban kungiyar nazarin yankin kudu maso gabashin Asiya na Sin, kuma farfesa a jami’ar Peking, ya bayyana cewa, tun daga sigar 1.0 zuwa 2.0 har zuwa 3.0, an samu ci gaba mai zurfi ta hanyar sabbin ka’idoji na fasahar zamani da kare muhalli, da sabunta tsarin amince da ka’idojin juna, da kara karfin hadin gwiwar samar da kayayyaki, inda ya inganta yankin ciniki daga matsayin “kara adadi” zuwa “ingantacciyar bunkasa”.
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu
A nasa bangare kuwa, ministan kimiyya da kirkira na Afirka ta Kudu, Dr. Blade Nzimande, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, ya gamsu da babban nasarar da Sin ta samu a wa’adin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 14. Ya ce, duk da kalubalen da duniya ke fuskanta, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba mai karfi ba tare da tangarda ba, kuma yana karawa tattalin arzikin duniya kwarin gwiwa.
Ya ce Afirka ta Kudu tana fatan koyi daga sabon tsarin ci gaban Sin, don karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka shafi sauyin yanayi, da tattalin arzikin dijital, da fasahar sararin samaniya da sauransu. (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA