Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya
Published: 29th, October 2025 GMT
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC October 29, 2025
Labarai COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa October 29, 2025
Manyan Labarai Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci October 29, 2025
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan kasuwar duwatsu masu daraja na ɗaukar nauyin ta’addanci —EFCC
Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya.
Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar.
Taron ya samu haɗin gwiwa tsakanin EFCC da Hukumar Bayar da Bayanai kan Harkokin Kuɗi (NFIU) tare da tallafin GIZ, wata cibiyar haɗin gwiwar Jamus.
Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 80 a Kebbi Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a KadunaOlukoyede, wanda ya bayyana takaicinsa kan halayen wasu ’yan kasuwar, ya ce akwai “ tsananin rashin kula” daga ɓangaren masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada, musamman wajen bin dokar sanin abokin hulɗa (KYC).
Ya koka kan yadda ake kin bayar da rahoton mu’amaloli masu alamun shakku, yana mai cewa hakan na kawo cikas ga yunkurin EFCC wajen yaƙi da safarar kuɗaɗen haram da kuma tallafin ta’addanci a Najeriya.
Shugaban EFCC ya yi wannan jawabi ne ta bakin Toyin Ehindero-Benson, Kwamandan Ofishin Kula da Safarar Kuɗaɗen Haram (SCUML) na shiyyar Ibadan, inda ta buƙaci mahalarta taron su koyi cikakkun ƙa’idojin da ke jagorantar ayyukan SCUML.
Ta ce hakan zai taimaka musu wajen fahimtar nauyin da ke kansu da kuma bin ƙa’idojin yaƙi da safarar kuɗaɗe da kuma hana ɗaukar nauyin ta’addanci, musamman ma a matsayinsu na manyan masu ruwa da tsaki a fannin haƙar ma’adinai.
A cewar sanarwar da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, Olukoyede ya bayyana cewa: “Halin wannan fanni na haƙar ma’adinai yana sanya shi zama muhimmin ɓangare a yaƙi da laifukan kuɗi.
“Wannan taro kuma wata dama ce ta musayar ra’ayoyi, faɗakarwa, da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da masu ruwa da tsaki.”
A nasa jawabin, Michael Etuk, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Duwatsu Masu Tsada ta Ojoo, Jihar Oyo, ya tabbatar wa EFCC cewa ’yan kasuwa da masu haƙar duwatsu a jihar za su yi duk abin da doka ta tanada domin taimaka wa gwamnati wajen ƙarfafa yaƙi da safarar kuɗaɗen haram da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci.