DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta
Published: 29th, October 2025 GMT
An rufe asusunsa na X saboda karya ƙa’idodin dandalin, kuma har yanzu DSS ba ta gurfanar da shi a kotu ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno
Habiba Abubakar mai shekaru 35 da ’yarta Adama mai shekaru 9 sun rasa rayukansu bayan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Karamar Hukumar Hawul da ke Jihar Borno.
Mai magana da yawun Rundunar ’San Sanda ta jihar, Nahum Daso, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 1:15 na rana, yayin da suke komawa gida daga gona.
Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – SanusiYa ce, “Sun fito daga gona ne kuma suna ƙoƙarin ketare wani kogi da ke kusa da kauyen Ghung. Amma saboda ƙarfi da saurin ruwan, jirgin ruwan nasu ya kife a wani wuri mai zurfi na kogin.”
A cewarsa, jami’an ’yan sanda tare da masu aikin ceto a yankin daga bisani sun gano gawarwakin su daga cikin kogin.
“Ba a ga wata alama ta tashin hankali a jikin gawarwakin ba. An ɗauki hotuna don adana bayanai kafin a kai su Asibitin Garkida da ke Karamar Hukumar Gumbi a Jihar Adamawa, domin shi ne asibitin da ya fi kusa da su,” in ji Daso.
An mika gawarwakin ga iyalansu don yin jana’izar su bisa tsarin Musulunci.
“A halin yanzu, Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan jihar da ke Maiduguri ya fara bincike kan lamarin,” in ji Daso.
Aminiya ta ruwaito cewa a watan Satumba an gano gawar wani yaro mai sayar da kaya, wanda ake kyautata zaton ya kai shekaru 12, daga cikin kogin Gamboru da ke unguwar Customs a birnin Maiduguri, babban birnin jihar.
A ’yan watannin nan dai ana samun yawan nitsewar jiragen ruwa musamman a yankin Arewa maso Gabas na ƙasar.