Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo rancen dala biliyan 2.35
Published: 30th, October 2025 GMT
Majalisar Tarayya, ta amince da buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na karɓo rancen dala biliyan 2.35 domin cike giɓin kasafin kuɗin shekarar 2025.
Dukkanin Mjalisun sun amince da buƙatar ne a ranar Laraba, bayan sun duba rahoton kwamitin karɓar basussuka na cikin gida da na waje.
Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati ACF ta mara wa gwamnatin Tinubu bayaHaka kuma, majalisar ta amince da buƙatar Tinubu na fitar da dala miliyan 500 domin samar da muhimman ayyuka kamar faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi ga ƙasar nan.
A cikin wasiƙar da ya aike wa majalisar tun a farkon watan nan, Shugaba Tinubu, ya bayyana cewa neman rancen ya zama dole domin aiwatar da kasafin kuɗin 2025.
Kasafin wanda ya ƙunshi Naira tiriliyan 9.28 na nufin cike giɓin da ake da shi a kasafin 2025.
Ya ce hakan zai taimaka wajen kauce wa kasa biyan bashi da kuma bin inganta ƙa’idojin kasuwar hada-hadar bashi ta duniya.
“Jimillar kuɗin da za a nema daga waje; dala biliyan 1.229 na sabon rance da dala biliyan 1.118 na sake biyan tsohon bashi zai kai dala biliyan 2.347,” in ji wasiƙar.
’Yan majalisa sun bayyana cewa rancen zai taimaka wa gwamnati ci gaba da aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa da kuma daidaita tattalin arziƙi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: rance dala biliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Karrama Shugaban NPA Da Lambar Yabo Ta Musamman
“An zabo Abubakar Dantsoho ne, daga cikin sauran wadanda aka karamma da lambar yabon bisa kokarin da yake ci gaba da yi, na bunkasa fannin sufurin Jiragen Ruwa na kasar wanda hakan ya sanya, aka kara samun fitar da kaya daga kasar nan, ta hanyar Tashoshin Jiragen Ruwa na kasa dIMODantsohoa tsarin NSW ta hanyar yin amfani da dabarar PCS domin janyo ra’ayin masu zuba jari daga ketare a Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar nan, da aka samar da kayan aiki na zamani, ” Inji sanarwar.
“Akawi kuma batun kara daga darajar Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar a tsakanin hukumomin Jiragen Ruwa da ke a Afirka ta Yamma wato PMAWCA da kuma zabar Dantsoho, a matsayin mataimakin shugaban kungiyar masu tafiyar da hukumomin Jiragen Ruwa na kasa da kasa wato IAPH,” A cewar sanarwar.
Hukumar ta NPA ta bayyana cewa, a karkashin shugabancin Dantsoho tare da taimakawar ministan bunkasa tattalin arziki na teku Adegboyega Oyetola, an sake zabar Nijeriya, zuwa mataki na C a karkashin kungiyar kasa da kasa ta tafiyar da harkar sufurin Jiragen Ruwa wato IMO.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA