Hare-haren Jiragen yakin Isra’ila Sun Kashe Mutane fiye da 60 a Gaza
Published: 29th, October 2025 GMT
Sama da Falasdinawa 60, ciki har da yara 22 ne suka yi shahada a jerin hare-haren jiragen yakin Isra’ila suka kai a wurare da dama a yankin Gaza A cikin sa’oin da suka gabata, A cewar majiyoyin lafiya.
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a lokaci guda kan gidaje, masallatai, da sansanonin ‘yan gudun hijira.
A Deir al-Balah, Falasdinawa uku sun yi shahada kuma wasu da dama sun jikkata lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan sansanonin mutanen da suka rasa gidajensu a gabashin Asibitin Al-Aqsa, a cewar majiyoyin lafiya na asibiti.
Sojojin mamayar Isra’ila sun kuma kai hari kan gidan iyalan Abu Sharar da ke sansanin ‘yan gudun hijira na al-Bureij, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar.
Bugu da ƙari, mutane da dama sun samu raunuka a wani harin bam da aka kai kan wani tanti da ke ɗauke da mutanen da suka rasa matsuguni a cikin makarantar Abu Hmeisa a wannan sansanin. Asibitin Al-Awda ya tabbatar da karɓar wasu mutane da suka ji rauni sakamakon harin da Isra’ila ta kai wa sansanin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Senegal ta sake gano wasu shaidu kan kisan gillar da aka yi a lokacin mulkin mallaka October 29, 2025 An bude taron ministocin cikin gida na kungiyar ECO October 28, 2025 Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku a Yammacin Kogin Jordan October 28, 2025 Hamas : Netanyahu Yana kokarin wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta October 28, 2025 China za ta dauki mataki idan takunkuman Iran sun shafi muradunta October 28, 2025 Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji Ukraine October 28, 2025 Pezeshkian: Hadin Kai A Tsakanin Kasashen Gabas Ta Tsakiya Ba Zabi Ba Ne, Amma Dole Ne October 28, 2025 Mataimakin Ministan Harkokin Waje Kan Harkokin Siyasa Na Iran Ya Ce: Iran Ba Ta Kula Da Matsin Lamba October 28, 2025 Baqa’i: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ce Ke Jagorantar Hadin Kan Iran Da Hukumar IAEA October 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kai Hare-Hare Kan Yankin Gaza A Matsayin Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Isra ila sun
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a Borno
Dakarun Sojin Rundunar Operation Haɗin Kai, sun kashe ’yan ta’adda biyu a wani samame da suka kai yankin Shettimari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga, a Jihar Borno.
Majiyoyi sun shaida cewa rundunar ta kai harin ne ƙarƙashin Operation Desert Sanity V da safiyar ranar Alhamis.
Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na Turkiyya Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a BinuwaiWata majiyar soji ta ce, “Sojojin sun tare mayaƙan a kusa da inda suka ke shirin kai hari a yankin da misalin ƙarfe 1:20 na dare.”
Ya ƙara da cewa, “Sojojin sun yi nasarar daƙile ’yan ta’addan nan take, inda suka kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere.”
Bugu da ƙari, majiyar ta ce daga baya an gano wasu bama-bamai guda biyu da kuma wani gidan harsashi guda ɗaya mai ɗauke da harsasai 23 masu ɗangon 7.62mm x 39mm da ’yan ta’addan suka watsar yayin tserewa.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Babu wanda ya mutu a cikin sojojin, sai dai daga baya tawagar sojojin sun ci gaba da aikinsu.”