An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna
Published: 29th, October 2025 GMT
Wata gamayyar malaman addinin Musulmai ƙarƙashin inuwar Concerned Ulama of Sunnah ta aika da ƙorafi zuwa ga Gwamnatin Jihar Kaduna tana zargin wasu malamai biyu da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W).
Ana zargin malaman ne da yi batancin a cikin wa’azozinsu na kafafen sada zumunta.
Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a BornoƘorafin, wanda malamai goma sha shida (16) suka sanya wa hannu, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Umar Shehu Zaria da Malam Muhammad Sani Abubakar, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hayin Na’iya, ya bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar mataki.
A cewar masu ƙorafin, ayyukan waɗannan malamai biyu “na iya janyo tashin hankali a ƙasarmu mai albarka idan aka bar su haka.”
Sun roƙi hukumomi da su gayyace su domin tattaunawa idan ya zama dole, ko kuma su dakatar da su, suna gargaɗin cewa rashin ɗaukar mataki “na iya haifar da tashin hankali da rikici wanda gwamnati ba za ta so hakan ba.”
Kungiyar ta bayyana cewa batun ya wuce na son rai, yana da alaƙa kai tsaye da muhimman ƙa’idodin addinin Musulunci.
“Akwai imani na asali cikin al’ummar Musulmi na girmamawa da kare mutuncin Annabi Muhammad (S.A.W). Shi ne asalin alheri ga kowanne Musulmi a duniya da lahira,” in ji ƙorafin”
Masu ƙorafin sun ambaci shari’ar Musulunci da maganganun manyan malamai dake nuna tsananin laifin batanci ga Annabi.
Sun kuma roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar mataki don hana rikici.
“Jihar Kaduna ta sha fama da rikice-rikicen ƙabilanci da na addini a baya, amma da taimakon Allah da jajircewar gwamnati, an shawo kan da dama daga cikin lamarin,” in ji su.
A martanin da ya bayar, Daraktan Hukumar Huldar Addinai ta Jihar Kaduna, Tahir Umar Tahir, ya tabbatar da karɓar ƙorafin kuma ya tabbatar wa malamai cewa gwamnati za ta duba shi.
“Mun karɓi ƙorafinsu a madadin Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, kuma da yardar Allah za mu duba wannan batu. Za a ɗauki matakan da suka dace don hana tashin hankali,” in ji Kwamishinan.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da tsayawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin addinai:
Tahir ya kuma roƙi shugabannin da malaman addinai da su yi hattara a cikin wa’azozinsu, yana gargaɗin su guji duk wani saƙo da zai iya haddasa rarrabuwar kai ko tashin hankali a cikin jihar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta ceto wata jaririya da ba ta wuce mako daya da haihuwa ba, da aka sayar kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi, tare da cafke mata huɗu da ake zargin su da hannu a cinikin.
Kakakin rundunar a jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa an samu labarin sayar da jaririyar ne a kauyen Ifite-Awkuzu da ke Karamar Hukumar Oti, inda rundunar ta ɗauki matakin gaggawa na cafke waɗanda ake zargin.
An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a BornoWaɗanda aka kama sun haɗa da Elizabeth Okafor mai kimanin shekara 62, Esther Nweke mai shekara 48, Ngozi Maanfa mai shekara 45, da Peace Elijah Moses, wadda ita ce mafi ƙarancin shekaru a cikin su, mai kimanin shekara 25.
Ikenga ya ce binciken da rundunar ta gudanar ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifin sayen jaririyar ba tare da an tursasa su ba, kuma ba a yi masu duka ko azabtarwa ba kafin su bayyana gaskiya.
“Jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, ba ta samu wata matsala ba,” in ji Ikenga.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ikioye Orutugu, ya bayar da umarnin a mika waɗanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin ci gaba da bincike.
Ya ce bayan kammala binciken, za a gurfanar da su a gaban kotu.