2025-10-29@13:28:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10854

«a tattalin arziki»:

    Rikici tsakanin bangarori biyu a garin Donga na Jihar Taraba, ya yi sanadin mutuwar mutum biyu a kan limancin masallacin Juma’a na garin. Bayanai sun nuna baya ga mutanen da suka mutu, wasu da dama sun jikkata kuma an lalata dukiyoyi. An ceto jaririya ’yar mako daya da haihuwa da aka sayar a Anambra An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Rikicin, kamar yadda Aminiya ta gano, ya faru ne a ranar Talata kan limancin masallacin Juma’a na garin da ke gaban fadar Sarkin Donga. Wata majiya daga garin ta shaida wa wakilinmu cewa rikicin ya samo asali ne daga sabani tsakanin kungiyoyi biyu na al’ummar Musulmi a garin kan wanda ya kamata ya zama...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta ce ta ceto wata jaririya da ba ta wuce mako daya da haihuwa ba, da aka sayar kan kuɗi Naira miliyan ɗaya da rabi, tare da cafke mata huɗu da ake zargin su da hannu a cinikin. Kakakin rundunar a jihar, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa Aminiya cewa an samu labarin sayar da jaririyar ne a kauyen Ifite-Awkuzu da ke Karamar Hukumar Oti, inda rundunar ta ɗauki matakin gaggawa na cafke waɗanda ake zargin. An kai ƙarar malamai 2 kan zargin ɓatanci ga Annabi a Kaduna Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Waɗanda aka kama sun haɗa da Elizabeth Okafor mai kimanin shekara 62, Esther Nweke mai shekara...
    Wata gamayyar malaman addinin Musulmai ƙarƙashin inuwar Concerned Ulama of Sunnah ta aika da ƙorafi zuwa ga Gwamnatin Jihar Kaduna tana zargin wasu malamai biyu da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Ana zargin malaman ne da yi batancin a cikin wa’azozinsu na kafafen sada zumunta. Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Uwa da ’yarta sun nitse a hatsarin jirgin ruwa a Borno Ƙorafin, wanda malamai goma sha shida (16) suka sanya wa hannu, ƙarƙashin jagorancin Shaikh Umar Shehu Zaria da Malam Muhammad Sani Abubakar, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Hayin Na’iya, ya bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta ɗaukar mataki. A cewar masu ƙorafin, ayyukan waɗannan malamai biyu “na...
    Mummunan cin zarafi a birnin El Fasher na kasar Sudan ya haifar da tofin Allah tsine da Allah wadai daga al’ummomin ƙasashen duniya da na cikin gida Kisan gilla da laifukan da ake aikatawa kan fararen hula a El Fasher, Arewacin Darfur, sun jawo Allah wadai daga Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin dan adam, yayin da gwamnati da hukumomin yankin ke musayar zarge-zarge game da musabbabin bala’in da kuma nauyin da ke kan al’ummar duniya. An ci gaba da Allah wadai da kasashen duniya da na cikin gida game da take hakkin da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta aikata kuma har yanzu take aikatawa kan fararen hula a El Fasher Arewacin Darfur. Kwamishinan...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa fararen hula a Sudan Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana damuwa game da rikicin makamai da ya barke a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Sudan, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula marasa laifi a birnin. A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta fitar a yammacin jiya Talata, Baqa’i ya nuna damuwa game da rikicin makamai da ya barke a El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Sudan, yana mai Allah wadai da lalata kayayyakin more rayuwa da kuma kisan fararen hula marasa laifi a birnin. Baqa’i...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da Amurka ta kakaba wa Cuba nan take Jakadan Iran kuma Wakilin Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya jaddada cewa: Dole ne a dage takunkumin da aka sanya wa Cuba nan take ba tare da wani sharaɗi ba. Ya bayyana cewa: Kawo ƙarshen waɗannan matakan ba wai kawai zai samar da sauƙi ga al’ummar Cuba ba ne, har ma zai aika da saƙo mai haske da yanke hukunci ga duniya cewa zamanin tilastawa, mulkin mallaka, da rashin adalci na tattalin arziki ya ƙare. Irawani ya jaddada a ranar Talata, a lokacin taron Majalisar Dinkin Duniya da aka keɓe don tattauna ɗage takunkumin Amurka...
    Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu ta soki shirin Trump kan Gaza tana mai jaddada cewa: “Yana daga mafi munin cin mutuncin da ta taɓa gani a rayuwarta Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta Musamman kan Kare Haƙƙin Dan Adam a Yankin Falasɗinu, Francesca Albanese, ta bayyana shirin zaman lafiya na Shugaban Amurka Donald Trump a Gaza a matsayin “mafi munin cin mutunci da na taɓa gani a rayuwarta,” tana mai tabbatar da cewa Shirin ba shi da haƙƙi na shari’a da na ɗabi’a. Albanese ta bayyana cewa: Ba ta da imani da tsarin siyasa na yanzu da ake Shirin aiwatarwa a Gaza ba, tana mai ƙarawa da cewa, “Ba za a iya gina...
    Habiba Abubakar mai shekaru 35 da ’yarta Adama mai shekaru 9 sun rasa rayukansu bayan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Karamar Hukumar Hawul da ke Jihar Borno. Mai magana da yawun Rundunar ’San Sanda ta jihar, Nahum Daso, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 1:15 na rana, yayin da suke komawa gida daga gona. Gwamnatin Kamaru za ta gurfanar da Issa Tchiroma a kotu kan zargin tayar da zaune tsaye Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sanusi Ya ce, “Sun fito daga gona ne kuma suna ƙoƙarin ketare wani kogi da ke kusa da kauyen Ghung. Amma...
    Gwamnatin kasar Kamaru ta ce za ta dauki matakin shari’a kan babban jagoran adawar kasar, Issa Tchiroma Bakary, bisa zarginsa da tayar da tarzoma bayan zaben shugaban ƙasa. Ministan cikin gida na kasar, Paul Atanga Nji, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, kamar yadda rahotannin kafafen yaɗa labarai suka nuna. Ba daidai ba ne Tinubu ya ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin mai – Sanusi DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya Ya ce hukumomin kasar sun fara tattara saƙonnin kafafen sada zumunta da bidiyo da aka bayyana a matsayin “ƙarya” da kuma masu tayar da hankali domin a gurfanar da masu wallafa su a gaban...
    Falasdinawa da dama ne suke ci gaba da yin shahada sakamakon ci gaba da kai hare-hare kan Zirin Gaza da Yahudawan Sahayoniyya ke yi An kashe fararen hula Falasdinawa da dama, wasu kuma sun jikkata yayin da sojojin mamayar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-haren sama a yankin Gaza tun jiya da daddare, wanda hakan keta yarjejeniyar tsagaita wuta ne. Majiyoyin lafiya sun ruwaito cewa adadin wadanda suka mutu ya karu zuwa 65 tun jiya da daddare har zuwa wayewar gari a yau Laraba, ciki har da 18 daga birnin Gaza da arewacin yankin Gaza, 40 daga tsakiyar yankin Gaza, da kuma 7 daga Khan Younis. Majiyoyin yankin sun ruwaito cewa jiragen yakin sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC October 29, 2025 Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October 29, 2025 Manyan Labarai Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II October 29, 2025
    Daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma ɗan kasuwa mai taimakon al’umma, Abdussalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ba da cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana kwarin gwiwa cewa shugaban na da kwarewa da hangen nesa wajen farfado da tattalin arzikin ƙasar da inganta jin daɗin jama’a. Zaura ya yi wannan kiran ne lokacin da wata tawaga daga Tinubu/Shettima Campaign Group ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa, inda ya jaddada cewa haɗin kan ’yan Nijeriya na da matuƙar muhimmanci domin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma tabbatar da matsayi irin na ƙasashen da ke...
    Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu. Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.” A watan Satumba 2025, Shugaba Tinubu ya umarci kwamiti na musamman na gwamnati da ya ɗauki matakan gaggawa don rage tsadar abinci a faɗin ƙasar nan. Duk da haka, wasu manoma na kukan cewa matakan sun jawo musu asara saboda tsadar kayan noman da suke amfani da su. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October...
    Sai dai gwamnatin Tinubu ta mayar da martani, tana cewa jam’iyyar ADC kawai tana adawa ne da nasarorin da gwamnati ke samu. Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz, ya ce: “Da farko ‘yan adawa suna ƙorafi cewa abinci ya yi tsada. Yanzu da gwamnati ta ɗauki matakai don rage tsada, sai kuma suke kuka.” A watan Satumba 2025, Shugaba Tinubu ya umarci kwamiti na musamman na gwamnati da ya ɗauki matakan gaggawa don rage tsadar abinci a faɗin ƙasar nan. Duk da haka, wasu manoma na kukan cewa matakan sun jawo musu asara saboda tsadar kayan noman da suke amfani da su. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa October...
    “’Yan majalisa suna kuma fuskantar barazana daga wasu ‘yan yankunansu da ke samun damar shiga ofisoshinsu ba tare da izini ba.” Ya ƙara da cewa idan aka kasa magance waɗannan matsalolin tsaro, hakan na iya kawo cikas ga gudanar da ayyukan majalisar kamar wakilci, sa ido, tattaunawar kasafin kuɗi da zaman majalisar, wanda zai iya shafar tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiyar ƙasa baki ɗaya. A watan Mayun shekarar 2021 ma, an taɓa samun irin wannan gargaɗi lokacin da Boko Haram ta yi shirin kai hari Majalisar Dokoki da wasu muhimman gine-ginen gwamnati a Abuja. Bayan wannan gargaɗi, an taƙaita shiga majalisar, inda masana tsaro suka buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara tsaurara matakan tsaro a muhimman wuraren gwamnati. Garba, ya yi...
    Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran Ali Larijani (SNSC) ya ce dangantakar da ke tsakanin Tehran da Islamabad tana  habaka, kuma za ta iya kaiwa matsayin babban hadin gwiwa na din-din-din. Ali Larijani, a yayin da yake yin wata ganawa da Ministan Harkokin Cikin Gida na Pakistan Syed Mohsin Naqvi a wannan Talata a birnin Tehran, ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar ƙasashen biyu a fannin tattalin arziki. Ya nuna yarjejeniyar dabarun da aka cimma a cikin kwanakin nan tsakanin Pakistan da Saudiyya, a matsayin mataki mai kyau kuma na hikima, wanda yake da tasiri matuka ga irin barazana da kasashen musulmi sue fuskata daga makiya. Larijani ya ce yanayin yankin a yau yana cike da ƙalubale daga maƙiya, wanda ke...
    Firayim Ministan Iraki Mohammed Shia al-Sudani ya jaddada cewa wajibi ne a kan al’ummar Iraki kare  ‘yancin kundin tsarin mulkin kasarsu wanda hakan ba zai yiwuwa ba sai hanyar  tsara makomar kasar ta hanyar sahihin zaben ‘yan majalisar dokoki da ke tafe. Al-Sudani ya jaddada cewa babu wani uzuri na kin kauracewa zabe da za a yarda da shi, yana mai bayyana cewa yin hakan “zai share fagen dawowar wadanda suka gaza da kuma wadanda suka ci hanci da rashawa.” Ya ce, “Muna dogaro da shiga cikin harkokin zabe cikin sani da himma a ranar 11 ga Nuwamba, ranar da za mu tsara sabuwar makomar siyasa ta Iraki.” Ya fayyace, “Muna son manufofin hikima da fifita muradun Iraki da al’ummar...
    Firayim Ministan Habasha Abiy Ahmed ya yi kira da kasashen duniya su shiga Tsakani domin yin tsakanin kasarsa da Eritrea kan batun Tekun Ja, yana mai jaddada muhimmancin kawo karshen duk wata tashin tashina a yankin Kahon Afirka. Abiy, yayin da yake jawabi ga majalisar dokoki a Addis Ababa, ya yi watsi da batun yin amfani da karfin soja amma ya jaddada cewa dole ne a saurari bukatar Habasha, kuma a warware batun ta hanyar diflomasiyya. “Bukatar Habasha ita ce samun damar shiga teku, amma ba mu da niyyar shiga yaki da Eritrea. Akasin haka, mun gamsu cewa za a iya warware wannan batu ta hanyar lumana da fahimtar juna ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba,” in ji...
    Sama da Falasdinawa 60, ciki har da yara 22 ne suka yi shahada  a jerin hare-haren jiragen yakin  Isra’ila suka kai a wurare da dama a yankin Gaza A cikin sa’oin da suka gabata, A cewar majiyoyin lafiya. Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a lokaci guda kan gidaje, masallatai, da sansanonin ‘yan gudun hijira. Wakilin Al-Mayadeen ya ruwaito cewa an kai wani harin bam a kan  gidan iyalan Abu Dalal da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat, inda aka  kashe mutane 10, ciki har da yara uku. An kuma kai hari gidan iyalan Aql da ke sansanin, wanda ya yi sanadiyyar shahadar  mutane uku da kuma jikkata da dama, yayin da Isra’ila take ci gaba da kai hari...
    Masana kayan tarihi a Senegal sun gano sabbin shaidu na kisan gillar da aka yi a lokacin mukin mallakar Faransa a kasar a shekarar 1944, a matsayin wani bangare na kokarin da gwamnati ke jagoranta na gano gaskiya game da batun kisan da sojojin Faransa suka yi a kasar da ke yammacin Afirka a lokacin da ake cikin yakin duniya na biyu. Makabartar sojojin Thiaroye, wacce ke kusa da babban birnin Dakar, a halin yanzu ita ce wurin bincike da aka yi fafakeken rami domin tono kayan tarihi da nufin gano gawarwakin sojojin da ake zargin sojojin mulkin mallaka na Faransa sun kashe su a ranar 1 ga Disamba, 1944. Lamarin ya faru ne bayan da aka kawo kusan sojoji...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Musamman Na Tattaunawa Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa A Afrika Da Kudu October 28, 2025 Daga Birnin Sin Masanan Kasar Sin Da Afirka Sun Hada Karfi Da Karfe Don Habaka Samun Wadatar Abinci Da Zamanantar Da Aikin Gona October 28, 2025 Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin October 28, 2025
    A zantawarsa da manema labarai, jagoran tafiyar Shelkh Umar Shehu Zaria wanda kuma shi ne, babban limamin Masallacin Mus’ab Ibn Umair, Sun jaddada cewa, su ba su da wani buri na daban face ganin an samu zaman lafiya, hadin kai, da mutunta juna a tsakanin mabiya addinai da jama’ar Kaduna baki daya. “Wadannan malamai guda biyu suna fakewa da malunta suna cin mutunci Manzon Allah SAW. Da’awarsu a Kaduna barazana ce ga zaman lafiya, saboda fitina a jihar Kaduna ba za ta haifar da abu mai kyau ba,” inji shi   Ofishin kula da harkokin addinai karkashin jagoranci Malam Tahir Umar Tahir, ya karɓi takardar korafin kuma ya tabbatar da cewa, zai gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar...
      A nasa bangare kuwa, ministan kimiyya da kirkira na Afirka ta Kudu, Dr. Blade Nzimande, ya bayyana ta kafar bidiyo cewa, ya gamsu da babban nasarar da Sin ta samu a wa’adin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 14. Ya ce, duk da kalubalen da duniya ke fuskanta, tattalin arzikin Sin ya samu ci gaba mai karfi ba tare da tangarda ba, kuma yana karawa tattalin arzikin duniya kwarin gwiwa.   Ya ce Afirka ta Kudu tana fatan koyi daga sabon tsarin ci gaban Sin, don karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin da suka shafi sauyin yanayi, da tattalin arzikin dijital, da fasahar sararin samaniya da sauransu. (Amina Xu) ShareTweetSendShare MASU...
    Sanarwar ta ce, wannan horo mai taken ‘Computer Appreciation Training’ an shirya shi ne ta Hukumar Fasaha da Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), a matsayin babban taron ƙarawa juna sani ga manyan jami’an gwamnati.   A jawabinsa yayin buɗe shirin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa wannan horo wata muhimmiyar hanya ce wajen cimma burin gwamnatinsa na ingantaccen aiki ta amfani da fasaha.   Ya ce, “Burin mu shi ne tabbatar da cewa kowane bangare na gwamnati yana aiki cikin tsari, inganci da sauri, kamar yadda fasaha ke bai wa duniya damar gudanar da aiki cikin sauƙi.   “Mun shiga wani zamani ne da fasaha ke sauya yadda ake gudanar da mulki – daga tsarin tsara manufofi, yanke shawara, zuwa yadda ake...
        ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Jama’a Ga Tsarin Jagoranci Na Sin October 28, 2025 Daga Birnin Sin An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas October 28, 2025 Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025
    Fitaccen marubucin nan ɗan Nijeriya wanda ya taɓa lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya ce gwamnatin Amurka ta soke bizarsa tana mai haramta masa shiga ƙasar. Farfesa Soyinka ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ya kira a Legas a ranar Talatar nan. Netanyahu ya ba da umarnin kai mummunan farmaki a Gaza Juventus ta kori kocinta Igor Tudor Ya bayyana cewa Ofishin Jakadancin Amurka ne ya sanar da shi batun ƙwace bizar a wata wasiƙa da ya aike masa. Sai dai ya sanar da cewa ba shi da masaniya kan wani mummunan laifi da ya aikata da har zai sa Amurkan ta soke bizar da ta ba shi. “Ya zama dole ne na kira...
    Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, wasu manoma uku da makiyayi daya sun samu kananan raunuka. Ya kara da cewa an tura ‘yansanda da ‘yan banga na yankin don dawo da zaman lafiya.   Kakakin rundunar ‘yansandan ya kuma ce, sun kama mutane 17 da ake zargi da hannu a rikicin, amma zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo a yankin. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kano Ta Bai Wa Mata 5,200 Tallafin Naira Miliyan 260 October 28, 2025 Labarai Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Hutun Kwanaki 2 Don Zaɓen Ƙananan Hukumomi October 28, 2025 Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October...
      Kuri’un na jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani, sun tattaro ra’ayoyin jama’a daga manyan kasashen duniya masu tasowa, da ma na kasashe masu samun saurin ci gaba. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Kusa Kammala Shirye-shiryen Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas October 28, 2025 Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 October 28, 2025
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya umarci rundunar sojin ƙasar da ta kai mummunan farmaki a Zirin Gaza, bayan ya zargi ƙungiyar Hamas da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma. Wata sanarwa da ofishin firaministan ya fitar, ta ce: “Bayan tattaunawar tsaro, Firaminista Netanyahu ya umurci rundunar soji da ta gaggauta kai hare-hare masu ƙarfi a Zirin Gaza.” Juventus ta kori kocinta Igor Tudor An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa Sanarwar na zuwa ne bayan Isra’ila ta zargi Hamas ta karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma kwanakin baya domin ba da damar kai agaji ga fararen hula da ke yankin. Tun da farko dai Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Fasahohin Sin Za Su Iya Kyautata Makomar Nahiyar Afrika October 28, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Karin Haske Kan Muhimman Shawarwarin Da Kwamitin Kolin JKS Ya Gabatar Yayin Tsara Shirin Raya Kasa Karo Na 15 October 28, 2025 Daga Birnin Sin An Yi Taron Tattaunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Amurka October 27, 2025
    Ya ce, an ɗauki wannan matakin ne don bai wa masu zaɓe a faɗin jihar damar gudanar da zaɓen da ke tafe a jihar.   Ya ƙara da bayyana cewa, Gwamna Bago ya umarci dukkan hukumomin tsaro a Jihar da su tabbatar an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari, yana mai sake tabbatar da alƙawarin gwamnatin Jihar na tabbatar da tsarin zaɓe mai aminci da kwanciyar hankali. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba October 28, 2025 Ra'ayi Riga Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani October 28, 2025 Labarai Tsohon Kwamishina...
    An bude taron ministocin cikin gida na kasashen kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO a birnin Tehran. Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Massoud Pezeshkian ne ya jagoranci bude taron wanda shi ne karo na hudu. Ministoci da manyan jami’ai daga Pakistan, Tajikistan, Turkmenistan, Jamhuriyar Azerbaijan, Afghanistan, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Turkiyya, Uzbekistan, da Jamhuriyar Musulunci ta Iran na halartar taron, tare da Sakatare Janar na ECO, Ministan Cikin Gida na Oman, da Mataimakin Ministan Cikin Gida na Iraki a matsayin baki. Mahalarta taron na tattauna batutuwan tsaro, sa ido kan iyakoki, tattalin arziki, da alaka tsakanin birane. Ya yi kira ga kasashen Tsakiyar Asiya, na Caucasus, Kudancin Asiya, Yammacin Asiya da Tekun Farisa, gami da kasashe membobin OCE, da su “yi...
    Sojojin Isra’ila sun kashe akalla Falasdinawa uku yayin da suke fadada hare-haren da suke kai wa a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye. Kamfanin dillancin labarai na Falasdinawa WAFA, wanda ya ambato majiyoyin yankin, ya ruwaito cewa sojojin mamayar sun mamaye kauyen Kafr Qud da karfin soja a ranar Talata. Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinawa ta bayyana shahidan da sunan Abdullah Muhammad Omar Jalmana, mai shekaru 27, Qais Ibrahim Muhammad al-Baytawi, mai shekaru 21, da Ahmed Azmi Arif Nashti, mai shekaru 29. Hamas ta yi Allah wadai da kisan na Isra’ila tana mai cewa kisan nasu “ya zama sabon laifi na laifukan da gwamnatin mamaya ta aikata kan mutanenmu a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye. Share 0 0 votes Article...
    Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta kori kocinta, Igor Tudor, bayan da ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Lazio, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki biyar kacal a wasanni biyar da ta buga a baya-bayan nan. A cewar wata sanarwar da kulob ɗin ya fitar a ranar Litinin, Massimiliano Brambilla, wanda shi ne kocin tawagar maza ta farko, zai jagoranci Juventus a wasan da za ta kara da Udinese a ranar Laraba. An raba wa iyalan ’yan sandan da suka mutu tallafin N31m a Jigawa Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba “Juventus FC na sanar da cewa ta sallami Igor Tudor daga matsayin kocin tawagar maza ta farko, tare da sauran jami’ansa...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa duk da jajircewar kungiyar na mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da ita, firaministan gwamnatin Isra’ila yana kokarin karya sharuddanta. Hazem Qassem, kakakin kungiyar, ya ce “Mun yi wa masu shiga tsakani bayani kan cikas din da ke hana neman gawarwakin fursunonin Isra’ila kuma mun nemi su samar mana da karin kayan aiki.” Mai magana da yawun Hamas ya kuma bayyana cewa: “Mun sanar da Alkahira game da ayyukan bincike na ‘yan Isra’ila, kuma muna ci gaba da sanar da masu shiga tsakani game da ci gaban binciken. Duk da tsagaita wuta da aka yi tsakanin gwamnatin Tel Aviv da kungiyar Hamas, sojojin Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare. Na...
    Kasar Rasha ta gargadi Faransa game da tura sojoji zuwa Ukraine don taimakawa Kyiv. Hukumar leken asiri ta Rasha (SVR) ta bankado cewa Faransa ta shirya aika Sojoji 2,000 zuwa Ukraine. Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta kira wannan yiwuwar “abin da ba za a yarda da shi ba,” tana mai gargadin hadarin dake tattare da shi. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta shawarci Paris da ta yi amfani da wadannan sojojin don kare gidajen tarihi na Faransa maimakon tura su a Ukraine. Dama a baya ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta bayyana cewa duk wani yanayi da ya shafi tura sojojin NATO a Ukraine ba abin yarda ba ne ga Rasha kuma yana iya fuskantar barazanar...
      Idan muka kwatanta da kasar Sin, sabanin yawan albarkatun da Afrika ke da su kamar na kasar noma, ita Sin kasa da kaso 9 kadai take da shi, amma kuma tana bayar da gagagrumar gudunmawa a duniya, inda take tsaye da kafarta wajen ciyar da al’ummarta, har ma ta bayar da gudunmawa ga kasashe mabukata.   To mene ne dalilin nasarar Sin a wannan bangare? Gaggarumar nasarar da Sin ta samu a bangaren aikin gona, ba wani abu ba ne illa jajircewar gwamnatin kasar da dabaru da fasahohin aikin gona da kullum ake lalubowa. Misali, ko a cikin hamada, kasar Sin ta lalubo dabarun da suka dace, inda ake noman tsirrai masu juriya dake iya ciyar da mutane da...
    Shugaba Tinubu, a cikin wasikarsa, ya ce, an yi nadin ne bisa tanadin Sashe na 18(1) na Dokar Sojojin Kasa, Cap A20, ta Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004.   Ya bukaci Majalisar Dattawa da ta yi la’akari da wannan bukatar don gaggawa kan tabbatar da daidaito mai inganci a cikin tsarin tsaron kasar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
    Rundunar ’yan sandan Jigawa ta raba tallafin Naira miliyan 31 ga iyalan jami’ai 59 da suka rasa rayukansu a bakin aiki. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan mataki na nuna irin ɗawainiyar da rundunar ‘yan sandan ke yi wajen kula da jin daɗin jami’anta da iyalansu. Majalisar Dattawa za ta tantance sabbin hafsoshin tsaro ranar Laraba Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru Aminiya ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘yan sandan Jigawa, CP Dahiru Muhammad ne ya wakilci Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, wajen raba tallafin a ƙarƙashin shirin nan na tallafa wa iyalan...
    Bugu da kari, an shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun ci gaban al’adu da dabi’a a cikin al’umma a zahirance, da kara inganta jin dadin rayuwa, da samun manyan sabbin ci gaba wajen zurfafa shirin samar da kyakkyawar kasar Sin, da kuma kara samun ci gaba wajen karfafa garkuwar tsaron kasa.   A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14 (2021-2025), an kiyasta cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin zai zarce yuan...
    Majalisar Dattawa za ta gudanar da zaman tantance manyan hafsoshin tsaron ƙasar a gobe Laraba waɗanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa kwanan nan. Shugaba Tinubu ya aike da sunayen sabbin hafsoshin zuwa majalisar ne domin tantancewa da amincewa da su, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada. Rikicin adawa da cin zaben Shugaba Paul Biya ya bazu a Kamaru ’Yan bindiga sun sa harajin N15m kan al’ummar Mazabar Sanata Tambuwal A wata wasiƙar fadar shugaban ƙasa da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman da aka gudanar a wannan Talatar, ya ce kwamitin da ke kula da harkokin tsaro zai zauna gobe domin tantance waɗanda aka naɗa. A makon jiya ne Shugaba Tinubu ya aiwatar...
    Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau takwas, zai cika shekaru 39 a watan Yuni mai zuwa. Ya ce yana jin daɗin zama a Miami bayan shekaru masu yawa da ya shafe a Barcelona da kuma lokacin da ya yi a Paris Saint-Germain. Messi ya buga wasanni 195 tare da Argentina, inda ya zura ƙwallaye 114, kuma ya taimaka musu wajen lashe manyan kofuna kamar Copa América, Finalissima, da Kofin Duniya na 2022 a Qatar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni El Classico: Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Barcelona Da Real Madrid October 26, 2025 Wasanni Tornadoes Ta Doke Pillars A Wasan Farko Na Babaganaru October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni...
    Rikici na kara bazuwa a Jamhuriyar Kamaru kwana guda bayan Kotun Kolin  ta tabbatar da Shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa mai cike da takaddama. Dan takarar jam’iyyar adawa, Issa Tchiroma Bakary, ta sake bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zaben ba, yana mai cewa “zaben ba sahihi ba ne” yana mai yin fatali da nasarar Shugaba Biya. Sanarwar sakamkon ta janyo zanga-zanga, kone-kone da fada a tsakanin jama’a da jami’an tsaro a biranen Douala da Mbouda da Bertoua da Batouri, inda ake ci gaba da samun rikice-rikice lalata dukiyoyi. Rahotanni sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kona gine-gine da farfasa abubuwa, da satar kaya a wasu manyan birane ciki har da...
    Ya ba da shawarar a mayar da wajen ayyukan al’umma kamar filin motsa jiki ko ɗakin taro maimakon a sayar shi. Kiru, ya buƙaci gwamnan jihar da ya ɗauki alhakin kura-kuran da aka tafka a wajen wannan aikin, tare da tabbatar da cewa irin wannan kuskure ba zai sake faruwa ba a nan gaba, musamman a harkokin ilimi da suka shafi jin daɗin dalibai da al’umma. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato October 28, 2025 Labarai ’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi October 28, 2025 Labarai An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi October 28, 2025
    Mazauna ƙauyukan Bazar da makwabtansu a Karamar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato, sun koka cewa ’yan bindiga sun kakaba musu harajin Naira miliyan 15 tare da barazanar kai sabbin hare-hare idan ba a biya ba. Wadannan ƙauyuka suna yankin Mazabar Sanatan Kudu ta Kudu, inda tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ke wakilta. Wani mazaunin yankin, Dauda Umar, ya shaida wa manema labarai, cewa “abin yana da matuƙar tsanani” kuma yana buƙatar gaggawar kulawar gwamnati. “Ina tabbatar muku cewa ’yan bindiga sun nemi Naira miliyan 15 daga gare mu, suka yi barazanar aikata mummunan abu idan ba mu biya ba. Ban san abin da za su yi ba kai tsaye, amma an riga an kakaba wannan haraji, wasu na...
    Al’ummar Unguwar Filin Samji da ke garin Katsina sun buƙaci hukumomi su tabbatar da adalci, bisan zargin da ake wa jami’an Hisbah da na Rundunar Tsaron Al’umma na gwamnatin jihar (C-Watch) da harbin mutane da kuma lakaɗa musu duka ba tare da dalili ba. Wata matar aure mai suna Khadija Hamisu Wada ta samu raunuka sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu mutane da dama suka ji raunuka bayan an kai musu hari da adduna, wuƙaƙe da sanduna. A cewar mazauna yankin, aƙalla mutane bakwai ne suka ji munanan raunuka a lokacin da abin ya faru. An ruwaito cewa Khadija na dauke da harsasai biyu a ƙugu, kuma likitoci sun gargadi cewa cire su da gaggawa na iya jawo mata matsalar...
    Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan Najeriya. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Haɗin kai a tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ba zaɓi ba ne, amma dole ne Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Hadin kai da hadin gwiwar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya a cikin tsarin Kungiyar Hadin Kan Tattalin Arziki (ECO) ba wani zaɓi ne na siyasa ba, a’a, wani muhimmin abu ne don cimma ci gaba, tsaro, da kwanciyar hankali a yankin. A lokacin jawabinsa a taron Ministocin harkokin cikin gida na kasashe membobin ECO na hudu, Pezeshkian ya lura cewa: Kiran wannan taron bayan dogon hutu yana nuna sha’awar kasashen membobinta na inganta hadin kai da hadin gwiwa a muhimman fannoni da ke shafar dangantakar yankuna. Ya bayyana cewa ma’aikatun...
    Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta bayyana damuwa kan yadda wasu ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a Najeriya ke cikin wadanda ake zargin suna taimakawa wajen daukar nauyin ta’addanci a sassan kasar. Hukumar ta gargaɗe su da masu hakar ma’adinai da su guji zama hanyar safarar kuɗaɗen haram ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci ta kowace hanya, tana mai jan hankalinsu da su daina harkokin da ke hana ci gaban tattalin arziki da tsaro a ƙasar. Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya faɗi haka a Ibadan, hedikwatar Jihar Oyo, yayin taron wayar da kai da horaswa na rana ɗaya da aka shirya domin masu haƙar ma’adinai da ’yan kasuwar duwatsu masu tsada a jihar. Taron ya samu haɗin...
    Mataimakin Ministan Harkokin Waje kan Harkokin Siyasa na Iran ya bayyana cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya amma ta yi watsi da duk wata tattaunawar dole da aka tilasta mata Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Harkokin Siyasa na Iran ya jaddada cewa: Iran ta yi imani da diflomasiyya, amma ta yi watsi da duk wata tattaunawa da aka tilasta mata bin duk wani ra’ayin wani bangare guda. Ya jaddada cewa: Warware takaddama cikin lumana zai yiwu ne kawai idan bangarorin biyu suna kan daidaito kuma babu wanda ke neman sanya sharuddansa. A lokacin taron kasa da kasa na hudu na nazarin Iran na zamani, a wani zama mai taken “Iran da Duniya Bayan Yakin Kwanaki 12,” Mataimakin Ministan Harkokin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tushen haɗin gwiwar Iran da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya shine dokar da Majalisar Dokoki ta zartar Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Tushen hadin gwiwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) shine dokar da Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ta zartar. A farkon taron, Baqa’i ya yi tsokaci kan sabbin abubuwan da suka faru a yankin, yana mai cewa: Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta gudanar da zaman diflomasiyya na biyu a yankin Mashhad, tare da halartar wakilan hukumomin da abin ya shafa daga larduna uku na kan iyaka, tare da wakilan kasashe makwabta. Wannan taron yana da nufin tallafawa da karfafa hadin...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren bama-bamai da dama a gabashin Zirin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila sun yi rusa bama-bamai kan gidaje da dama a gabashin Zirin Gaza da safiyar yau Talata, tare da harba manyan bindigogi a yankuna daban-daban, a matsayin ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta. Cibiyar Bayanai ta Falasdinawa ta ruwaito cewa: Tun daga wayewar gari a yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila sun rusa gidaje da gine-gine akalla guda huɗu a gabashin birnin Gaza, Al-Bureij, da Khan Younis, inda aka ji ƙarar fashewar abubuwa masu karfi . Cibiyar ta ƙara da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun buɗe wuta, ba tare da wani dalili ba a yankuna da dama na gabas da arewacin Zirin Gaza. Share 0...
    Babban hafsan hafsoshin Sojin Sudan kuma shugaban majalisar gudanar da mulkin kasar ya bayyana cewa; Rundunar sojin kasar ta bar birnin El Fasher ne domin gujewa “kisan fararen hula” da dakarun kai daukin gaggawa ke yi Shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin Soja ta Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce: shugabannin sojoji sun yanke shawarar barin birnin El Fasher da ke Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan ne, domin kare birnin da ‘yan kasar daga afkawa cikin matsalar kisan kai a hannun Rundunar Rapid Support Forces ta dakarun Kai Daukin Gaggawa. A cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu, al-Burhan, wanda ke jagorantar rundunar sojin Sudan, ya ce a wani jawabi da aka watsa ta talabijin a gidan talabijin na gwamnati:...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu October 28, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno October 28, 2025 Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025
    Jami’an tsaron hadin gwiwar sun kashe fiye da ’yan bindiga 80 da suka yi yunƙurin kutsawa Jihar Kebbi ta iyakarta da Zamfara. Rahotanni sun bayyana cewa, sojojin sama da na ƙasa sun gudanar da sumame a dajin Makuku, inda suka yi ruwan wuta kan sansanonin ’yan ta’adda, suka kuma kashe da dama daga cikinsu. Dakarun sun kuma ceto mutane biyu da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su. A wata sanarwa da Daraktan Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kebbi, Abdulrahman Zagga, ya fitar, an bayyana cewa dakarun sun yi nasarar daƙile wani mummunan hari da sama da ’yan bindiga 400 suka kai garin Ribah, inda aka yi musu mummunar ɓarna. An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Rikicin...
    An ɗage sauraron shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, matarsa Hafsat, da wasu mutum shida a ranar Litinin bayan sun kasa miƙa takardun da ake buƙata a kotu. Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da su bisa tuhume-tuhume 11 da suka shafi cin hanci, haɗa baki wajen yin laifi, da karkatar da kuɗaɗen gwamnati da suka kai miliyoyin Naira. APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa Lokacin da aka fara sauraren shari’ar, lauya mai kare gwamnati, Adeola Adedipe (SAN), ya ce sun shirya fara gabatar da shaidu, amma lauyoyin Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma suka nemi ƙarin lokaci,...
    Iran, a matsayinta na ƙasa mai wayewa da wayewa, ta kasance mai himma wajen haɓaka zaman lafiya da tsaro a duniya, in ji Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Esmail Baqaei a ranar Litinin a gefen wani biki na cika shekaru 80 da kafa Majalisar Dinkin Duniya a Tehran. A cewar Pars Today, Baqaei ya ƙara da cewa a cikin ‘yan shekarun nan, an sami manyan keta ƙa’idodi da manufofin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, waɗanda suka yaɗu a duk duniya. Ya yi gargaɗin cewa rashin kula da manufofin Majalisar Dinkin Duniya ya sanya zaman lafiya da tsaro a duniya cikin haɗari mai girma. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake jaddada buƙatar...
    Cibiyar dake kula da ilimin kasa ta kasar Jamus ( GFZ) ta sanar da cewa, girgizar kasar da ta faru a Turkiya ta kai daraja 6.1 a ma’aunin motsin karkashin kasa. Girgizar dai ta faru ne da misalin 10;48 na daren jiya a nisan kilo mita 10 karkashin kasa. An yi karar girgizar kasar a birnin Istanbul da sauran garuruwan da suke zagaye da shi. Ya zuwa yanzu dai babu wani rahoto akan asarar rayuka da girman asarar dukiyar da ta haddasa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks...
    Sakamakon da aka fitar a jiya Litinin ya bayyana cewa, Alassan Outara dan shekaru 83  ya lashe zaben a kaso 89.77 na jumillar shugaban. Mutum na biyu wanda yake bin Outara a baya shi ne tsohon ministan kasuwanci Jean-Lous Billon da kaso 3%, sai kuma mai dakin tsohon shugaban kasar Simone Gbango da ta sami kaso 2.4%. Tuni dai Billon ya taya Ouattara murnar cin zaben, bayan da ya yarda ya sha kaye. Tare da cewa  a karkashin shugabancin Ouattara kasar ta Ivory Coast ta sami ci gaban tattalin arziki, sai dai masu bin diddigin siyasar kasar suna yin suka akan wasa da tsarin mulkin kasar domin bayar da damar ci gaba da tsayawa takarar Alassan Ouarrata. A zaben da...
    Kungiyar Dakarun Kai Daukin Gaggawa ( RSF) ta kasar Sudan ta sanar da kwace iko da birnin El-Fashar, da nan ne tungarta ta karshe a yankin Darfur. Hakan dai ya haddasa matsalar dangane da ayyukan jin kai da ceto saboda yadda aka rutsa da dudun mutane a cikin birnin. A jiya Litinin ne dai rundunar ta (RSF) ta kame wani sansanin soja mai matukar muhimmanci a Arewacin babban birnin na yankin Darfur. Garin El-Fasha ne dai sansani mafi girma da sojojin kasar Sudan suke iko da shi a yankin Darfur. Wani rahoton MDD ya ambaci cewa da akwai fiye da mutane 26,000 da suke a tarwatse a cikin birnin na Darfur a tsawon shekara daya da aka dauka ana killace...
    Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara akan harkokin siyasar kasa da kasa Dr.  Ali Akbar Wilayati ya ce; Da akwai kasashe uku a cikin Asiya wadanda suke da ‘yanci da su ne Iran, China da Rasha, kuma suna taka rawa domin samar da sabon tsarin tafiyar da duniya. Dr. Wilayati ya bayyana hakan ne dai a yayin ganawarsa da jakadan China a Iran “Zong Bi Wuu” yana mai kara da cewa; Alaka a tsakanin kasashen biyu ta dade da kuma zurfi.  Har ila yau Wilayati ya ce alakar kasashen biyu ta ginu ne akan maslaha da kuma girmama juna da kuma cin gashin kai na siyasa, da hakan ya mayar da su, tare da kasar Rasha zama...
    Rikicin Jam’iyyar ADC na Jihar Kaduna ya ɗauki sabon salo, bayan da uwar jam’iyyar ta nada tsohuwar Ministar Kuɗi, Sanata Nenadi Usman, a matsayin Shugabar Hadakar Jam’iyyar a jihar. Haka kuma jam’iyyar ta nada tsohon Kwamishinan Kudi na Jihar Kaduna, Bashir Sa’idu, na hannun daman tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufa’i, a matsayin Mataimakin Shugaban Haɗakar. Da yake jawabi yayin taron manema labarai, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa (Arewa maso Yamma), Ja’afaru Sani, ya bayyana cewa manufar ADC ita ce haɗa kan shugabannin jam’iyyun adawa a Kaduna domin ƙarfafa dimokuradiyya da shigar kowa cikin harkokin siyasa. Ya ce shugabannin Haɗakar sun ƙuduri aniyar sake farfaɗo da jam’iyyar da kuma haɗa kan jama’a don kawo ƙarshen abin da ya kira “mulkin...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa October 27, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025
    An kira wani taron musamman a Amurka na tattaunawa tsakanin kasa da kasa mai taken “Kirkire-kirkire da budadden kasuwanci, da more damammakin ci gaba” a birnin Washington na Amurka. Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da ofishin jakadancin Sin dake Amurka ne suka gabatar da taron cikin hadin gwiwa. Kusan baki 100 daga Amurka da Sin, ciki har da masana kan harkokin kasa da kasa, malamai, da wakilan matasan Amurka, sun tattauna batutuwa kamar yadda Sin ke amfani da karfin kimiyya da fasaha mai dorago da kai don karfafa kirkire-kirkire a duniya, da fadada budadden kasuwancinta mai zurfi, da more damammaki ga sauran kasashe. Da wannan taron ne aka fara gudanar da jerin tarurrukan tattaunawar...
    Shugaba Alassane Ouattara, ya sake lashe zaɓen shugabancin ƙasar Ivory Coast wanda ya ba shi sabon wa’adin mulki a karo na huɗu. Ouattara mai shekaru 83, ya samu kashi 89.77 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kamar yadda hukumar zaɓe ta ƙasa ta tabbatar a ranar Litinin. Tinubu ya gana da sabbin hafsoshin tsaro An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Fiye da mutane miliyan tara ne suka cancanci kada ƙuri’a a zaben da aka gudanar a ranar Asabar, wanda aka gudanar cikin yanayi na fargaba, bayan da manyan abokan hamayyarsa biyu — tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo da tsohon shugaban Credit Suisse, Tidjane Thiam — aka hana su tsayawa takara. Sakamakon ya nuna cewa, duk da ƙarancin fitowar...
    Wani rahoto da hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin (NBS) ta fitar a yau Litinin ya nuna cewa, ribar da manyan masana’antun kasar Sin suka samu cikin watanni tara na farkon shekarar 2025 da muke ciki, ta karu da kashi 3.2 cikin dari. A cewar hukumar ta NBS, masana’antun da ke samun kudaden shiga da suka kai akalla yuan miliyan 20 (kimanin dala miliyan 2.8) a shekara-shekara, sun samu jimillar ribar da ta kai yuan tiriliyan 5.37 a cikin watanni taran. A watan Satumba, ribar da manyan masana’antun ke samu ta farfado sosai, inda ta karu da kashi 21.6 cikin dari a kan na makamancin lokacin a bara, kamar yadda hukumar ta NBS ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare...
    Da yake miƙa takardar naɗin, Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo, ya taya sabon Sarkin murna, tare da kira gare shi da ya bi dokokin gwamnati da na ƙasa wajen gudanar da mulkinsa. Ya ce gwamnatin jihar ta tabbatar da naɗin ne bayan ta binciki cancanta, da halayya, da tarihin mulki na sabon Gung Zaar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da sabbin hafsoshin tsaron Najeriya a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Sai dai babu wani cikakken bayani kan dalilin ko maudu’in wannan taron, wanda shi ne karo na farko bayan sauya manyan hafsoshin tsaron Najeriya da shugaban ƙasar ya yi. An kashe wasu makiyaya 10 a Kebbi Zanga-zanga ta ɓarke a Kamaru Sai dai wata majiya daga fadar shugaban kasar ta ce taron ba zai nasaba da ƙoƙarin da ake yi na ƙarfafa tsarin tsaro da inganta aikin rundunar sojoji a ƙasar nan ba. Tinubu yayin ganawa da sabbin hafsoshin tsaro Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Shugaba Tinubu ya tuɓe hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Christopher Musa da...
    A yau Litinin 27 ga Oktoba, kungiyar jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta ba da rahoton bayanan ayyukan jigilar kayayyakin dake bukatar kankara a watannin Yuni da Yuli da Agustan bana. Bayanan na nuna cewa, a karkashin jagorar manufofi da bukatun kasuwa, aikin jigilar kayayyakin dake bukatar kankara ya nuna samun ci gaba mai karfi tare da fadada girman kasuwa. Bayanan sun nuna cewa, jimillar da aka samu a wannan bangare a wadannan watanni 3 ta kai tan miliyan 117.3, wadda ta karu da kashi 4.72% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. A cikin watanni 3 na farko na wannan shekara, jimillar jigilar abincin dake bukatar kankara ta kai tan miliyan 309.3, wadda ta karu da...
    A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa  Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Oktoba, 2025 da gagarumin rinjaye. Rahotanni sun ce Ouatara ya samu kashi 89.77% na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga sakamakon wucin gadi da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (IEC) ta fitar dazu. Duk da cewa sakamakon zaben bai ƙare ba tukuna, amma Ouatara da ke jagorantar tun 2011 yana kan hanyarsa ta zuwa wa’adi na huɗu a kan karagar mulkin ƙasar, bayan sake zaɓensa a 2015 da 2020. A wannan Litinin, Hukumar zaɓe ta ƙasa da ƙasa (IEC) ta sanar da cewa Alassane Ouattara, mai shekaru 83, na...
    Aƙalla makiyaya goma aka kashe a wani hari da aka kai wa Fulani makiyaya a wata ruga da ke yankin Tilli a ƙaramar hukumar Bunza ta Jihar Kebbi. Majiyarmu ta ce harin wanda ya yi kama da na ramuwar gayya na zuwa ne bayan kashe wani ɗan sa-kai a yankin. An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali Zanga-zanga ta ɓarke a Kamaru Bayanai sun ce mutuwar ɗan sa-kan ce ta jawo zargin cewa Fulani ne suka yi kisan, lamarin da ya sa wasu matasa suka dunguma suka kai farmaki a sansanin Fulani, inda suka kashe mutum goma a yayin harin. Wani mazaunin yankin da ya zanta da wakilinmu ya ce, “kuskuren fahimta ce ta sa aka kai harin. “Sun...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki wajen kare tsarin cinikayya tsakanin mabanbantan sassa bisa matukar himma, tare da kasancewa cikin shirin aiki tare da dukkanin sassa, don kare martabar cudanyar mabanbantan sassa bisa gaskiya. Li, ya yi tsokacin ne cikin jawabinsa a yau Litinin, yayin taron shugabanni karo na biyar, na cikakkiyar yarjejeniyar kawance ta cinikayya cikin ‘yanci ta yankin Asiya da Fasifik ko RCEP, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Kazalika, a birnin na Kuala Lumpur, yayin da yake jawabi a dandalin taron kasashen gabashin Asiya karo na 20, Li Qiang ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da mabanbantan sassa, wajen ingiza...
    A yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci nune-nune da aka gudanar a babban gidan adana kayan tarihi na “Palace Museum”, albarkacin cika shekaru 100 da kafuwar gidan tarihin. Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi kira da a kara babbar azama wajen kare gidan tarihin, a matsayinsa na wuri dake rike da matsayin kyakkyawar ma’adanar wayewar kai ta kasar Sin. Kazalika, a dai yau din, kamfanin dab’i na al’ummar kasar Sin, ya wallafa wani littafi na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mai kunshe da cikakkun bayanai, da fashin baki kan muhimman batutuwa da aka tattaunawa kan tsaron al’umma. (Mai fassara: Saminu Alhassan) ShareTweetSendShare MASU ALAKA...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26, 2025
    Wata hukumar shige da fice da kwastam ta Amurka (ICE) ta tsare wani dan jarida mai sharhi kan harkokin siyasa, Sami Hamdi, a filin jirgin sama na San Francisco saboda sukar da ya yi wa Isra’ila a yayin wani rangadin jawabai da ya yi a Amurka. A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar CAIR ta ce an tsare Hamdi ne a filin jirgi sama na San Francisco. A ranar Lahadi CAIR ta yi kira da sake shi kuma ta zargi Trump da tsare shi saboda sukar da yake yi wa Isra’ila. Masu goyon baya da masu fafutukar kare hakkin jama’a sun ce tsare Hamdi wani lamari ne na ramuwar gayya ta siyasa ga masu sukar Isra’ila, wadanda ake hukunta su...
    Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta Ifopa faransa, ta nuna cewa kasha 84 cikin dari na ‘yan kasar basu gamsu ba da Emmanuel Macron a matsayin shugaban kasa. A cewar kuma wannan binciken da aka yi aka kuma wallafa a jaridar le Journal du Dimanche, kashi 16% ne kawai na mutanen Faransa suka “gamsu” da aikinsa a Fadar Élysée, yayin da kashi 84% suka nuna rashin gamsuwa da shi. Kiyasin farin jinin shugaban bai taba raguwa haka ba. Emmanuel Macron, wanda kwarin gwiwarsa ke ci gaba da durkushewa, yanzu ya ba wa kashi 54% na masu jefa kuri’arsa kunya a zagaye na farko na 2022. Rikice-rikicen da aka samu sakamakon rusa Majalisar Dokoki ta kasa, murabus, sannan sake nada Lecornu...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta nisanci nuna bangaranci a cikin ayyukanta musamman game da yadda Amurka da Isra’ila ke keta dokokin kasa da kasa. Da yake bayyana hakan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta zama wakiliya game da hakkokin duk kasashe, yayin da yake yabon ka’idojin kungiyar.   Ya bayyana hakan ne a lokacin da MDD ta cika shekaru 80 da kafuwarta. Mista Baghai Ya Yi Allah wadai Da ta’addancin Da Amurka Da Isra’ila Suka Yi Wa Iran A Watan Yunin Da Ya Gabata. Iran ma ta bi sahun wasu kasashe a duniya da a ranar Litinin din nan, 27 Ga...
    Majalisar tsarin mulki a jamhuriyar Kamaru ta sanar da Paul Biya mai shekara 92 a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 12 ga wata. Mista Biya ya lashe zaben da kashi 53.66% na kuri’un da aka kada, wanda hakan ya ba shi damar shugabancin kasar a wa’adin mulki na takwas. Saidai babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary, wanda ya yi ikirarin lashe zaben, ya samu kashi 35.19% na kuri’un, a cewar alkaluman da aka samu daga cibiyar. Madugun ‘yan adawar ya yi fatali da sakamakon zaben da ya danganta da abin dariya. Rahotanni sun ce tarzoma ta barke a wasu sassan kasar da suka hada da Douala da Garoua bayan sanar da nasarar ta...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025 Labarai Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote  October 27, 2025 Labarai An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga  October 27, 2025
    Sa’an nan matakin da kasar Sin ke dauka yanzu, shi ne jagorantar manyan gyare-gyare kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, ta yadda ita da dukkan kasashe masu tasowa za su samu damar inganta tsare-tsarensu na tattalin arziki, musamman ma a bangaren masana’antu. Dangane da batun, babbar darektar hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana a wajen taron dandalin tattaunawa na Abuja karo na 6, da ya gudana a kwanakin baya, cewa “Sauyawar tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya ta haifar da damammaki ga kasashen Afirka, ta fuskar janyo jari, da karfafa bangaren masana’antu.” Ban da haka, ta ce, “Huldar abota tsakanin Afirka da Sin wani misali ne na samun ci gaban da zai amfani kowa ta hanyar...
    An kammala bikin bayar da Kyautar Jaruman Indomie karo na 17, inda aka karrama matasan da suka nuna hazaƙa da jarumtaka, kuma suka zama jakadun Najeriya a fannoni daban-daban. Wannan gagarumin biki ya gudana a birnin Legas a ranar 16 ga Oktoba, 2025, ƙarƙashin shirye-shiryen kamfanin Dufil Prima Foods, masu samar da Indomie Instant Noodles, a wani ɓangare na shirin kamfanin na kyautata dangantaka da al’umma (CSR). Kamfanin ya tabbatar da bayar da kyaututtuka ga Jaruman Indomie — wani girmamawa na musamman ga matasan da suka nuna jarumta da Ƙirƙire-ƙirƙire a faɗin ƙasar. Taken bikin na bana shi ne “Jaruman da Ba a San Su ba”, inda fitattun matasa uku daga sassan Najeriya suka fito a matsayin zakaru, bayan sun...
    Rahotonni sun bayyana ɓarkewar zanga-zanga a birnin Douala, cibiyar kasuwancin Kamaru jim kadan bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar. Wasu bidiyoyi da aka yaɗa a dandalan sada zumunta sun nuna gomman mutane sun fantsama kan titunan birnin, tare da rera waƙoƙin goyon bayan Issa Tchiroma Bakary, jagoran adawar ƙasar. An rufe makarantu saboda ƙarancin man fetur a Mali Paul Biya mai shekara 92 ya lashe zaɓen Kamaru Kamfanin dillancin labaran Kamaru, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda aka lalata wani ginin majalisar birnin, bayan da masu zanga-zangar suka far masa. BBC ya ruwaito cewa, a yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar kan abin da ka iya faruwa bayan sanar da sakamakon zaɓen Kamaru, makarantu da...
    Duk makarantu a fadin ƙasar Mali da ke Yammacin Afirka za su ci gaba da kasancewa a rufe daga ranar 27 ga Oktoba zuwa 9 ga Nuwamba, sakamakon tsananin ƙarancin man fetur da ya janyo tsaikon harkokin sufuri da na yau da kullum. Ministan Ilimi na ƙasar, Amadou Sy Savane ya sanar a ranar Lahadi cewa dukkan cibiyoyin ilimi za su dakatar da ayyukansu na tsawon makonni biyu saboda ƙarancin man fetur da ake fama da shi. Paul Biya mai shekara 92 ya lashe zaɓen Kamaru Sule Lamiɗo na neman takarar Shugaban PDP na Ƙasa Amadou Sy Savane ya shaida wa gidan rediyon gwamnati na ORTM cewa an shirya sake buɗe makarantu a ranar 10 ga watan Nuwamba. Tsawon makonni...
    An naɗa Birgediya Janar Qarshi a matsayin Mataimakin Babban Kwamandan Sojojin Juyin Juya Halin Musulunci Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Pakpour, ya fitar da wata doka da ta nada Birgediya Janar Seyyed Hujjatullah Ghoraishi a matsayin mataimakinsa na harkokin daidaitawa. Birgediya Janar Ghoraishi ya taba yin aiki a matsayin Mataimakin Ministan Tsaro na Farko da Mataimakin Harkokin Shiri da Tallafi a Ma’aikatar Tsaro. An nada Birgediya Janar Mohammad Reza Naqdi, wanda a baya ya yi aiki a matsayin Mataimakin Harkokin Daidaito na IRGC, a matsayin Babban Mai Ba da Shawara ga Babban Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta IRGC. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments...
    Kobi ta ce, an samu buƙata daga wajen mutane bakwai, inda aka tantance su domin fafata neman sa’a, daga baya mutane uku suka janye suka bar mutane huɗu domin fafata neman nasara a zaɓen.   “Bayan gudanar da zaɓen, Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (Rtd) shi ne ya yi nasara.   “Za a gabatar da sakamakon nasarar da ya samu wa gwamnan domin amincewar da gabatar wa Gung-Zaar na farko takardar naɗinsa a matsayin Sarkin masarautar Zaar,” sanarwar ta shaida.   Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da al’ummar Sayawa ke zanga-zangar adawa da yunƙurin gwamnatin jihar Bauchi ta Bala Muhammad wajen naɗa musu wani a matsayin Sarkin masarautar Sayawa wato (Gung Zaar).   Masu zanga-zangar dai sun bayyana...
    Shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Sun bai wa masu shiga tsakani cikakken ‘yanci na zaɓar membobin Kwamitin Gudanar da Gaza Khalil al-Hayya, shugaban ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: ƙungiyar ta Hamas ta bai wa masu shiga tsakani ‘yancin zaɓar membobin kwamitin da za su gudanar da mulkin Gaza, wanda zai sami cikakken iko a yankin. A wata hira da aka watsa a gidan talabijin na Al- Jazeera a yammacin Lahadi, al-Hayya ya jaddada cewa; Akwai batutuwan ƙasa waɗanda ba wai Hamas kaɗai ke da alhakinsu ba, amma alhakin dukkan ƙungiyoyin ƙasa ne. Ya bayyana cewa ƙungiyar ta gudanar da tarurruka da dama da ƙungiyoyi, ciki har da Fatah. Ya ƙara da cewa abin da...
    Shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru ya sake lashe zaɓen Shugaban Ƙasar domin fara wa’adi na takwas na shekara bakwai. Kotun Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta sanar cewa Mista Paul Biya mai shekaru 92 ya samu nasara ne bayan ya samu 53.66 na kuri’un da aka jefa a yayin da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35.19. Da haka biya zai ci gaba da mulki inda zai kammala sabon wa’adin yana dan shekara 99. Zuwa ƙarshen wa’adin, Biya wanda ya shekara 43 a gadon mulki tun 1982 zai cika shekara 50 a kan mulki. A halin yanzu shi ne shugaban kasa mai ci mafi tsufa a duniya. Shi ne kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na biyu a tarihin...
    An Kammala bikini bada Kyautar Jaruman Indomie Karo Na 17, An Girmama Matasan da suka nuna hazaka Kuma wadanda suka kasance jakadun Najeriya. Wannan gagarumin biki ɗaya gudana a Lagos, Najeriya, a ranar 16 ga watan Oktoba, 2025: kamfanin Dufil Prima Foods, masu yin Indomie Instant Noodle suka shirya karkashin shirinsu na kyautata alaka da Al’umma na Kamfanin Indomie, sun tabbatar da bada Kyautuka ga Jaruman Indomie, wani mataki na daraja, wadanda suka nuna jarunta bisa ayyukan jarumtaka da sukayi, ta hanyoyi daban daban da suka kunshi kirkire-kirkire na yaran Najeriya. An gudanar da wannan taro a Legas, inda gasar karshe ta wannan shekarar, mai taken “Jaruman da ba a San Su ba” inda fitattun matasa uku ‘yan Najeriya wadanda...
    Mutane biyu ne suka yi shahada, yayin da wasu biyu suka jikkata a harin da Sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gabashin kasar Lebanon Hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata mota a garin  Hafir yammacin Ba’alabak sun yi sanadiyyar shahadan mutane biyu tare da jikkata wasu biyu na daban a jiya Lahadi, a cewar wakilin gidan talabijin na Al-Mayadeen a Baka’a. Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hare-haren ne ta hanyar jiregen saman yaki kan motar da take dauke da fararen hula lamarin da ya yi sanadiyyar shahadan ‘yan ƙasar Lebanon biyu, wasu biyu kuma sun ji Rauni. Majiyoyi sun kuma ruwaito cewa: Wani jirgin saman yakin Isra’ila mara matuki ciki ya harba makamai...
    Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International ta matsa wa Uganda lamba ta bayyana makomar masu fafutukar kare hakkin bil’adama na Kenya Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International Kenya ta ƙara matsin lamba ga hukumomin Uganda kan su saki masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam na Kenya Bob Njagi da Nicholas Oyo, waɗanda suka ɓace a babban birnin Kampala, a farkon watan Oktoba. Ana zargin gwamnatin Uganda da Rashin bayyana makomar mutanen biyu. A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau ranar Litinin, ƙungiyar ta Amnesty International ta kwatanta halin da ake ciki a Uganda a yanzu da mulkin tsohon shugaban ƙasa Idi Amin (1971-1979), wanda aka danganta shi da ɗaya daga cikin mafi munin lokutan take haƙƙin...
    Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa a Sudan ta karɓe iko da Barbi da El Fasher a daidai lokacin da ake gargaɗin jin kai Rundunar Rapid Support Forces ta Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta sanar da gwace iko da birnin El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, jim kaɗan bayan sanar da ikonta a Barbi a Arewacin Kordofan. Rahotannin cikin gida sun yi gargaɗin jin kai sun yi magana game da kisan gilla da kuma ƙaura daga wurare daban-daban, kuma matsin lamba na ƙasashen duniya yana ƙaruwa don rage lamarin da kuma sauƙaƙe hanyoyin samun agaji zuwa yammacin Sudan. Abubuwan sun ƙaru a jihohin Arewacin Darfur da Arewacin Kordofan bayan da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta...
    Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce wasu daga cikin mutanen da saba yabon tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari lokacin yake kan mulki, su ne suka fara yi masa ba’a tare da suka bayan ya sauka daga mulki. Da yake jawabi a wani taron “Lakcar Raymond Dokpesi” da Ƙungiyar Masana Hulɗa da Jama’a ta Najeriya (NIPR) ta shirya a birnin Abuja, Gwamna Sule ya ce ya shaida da idonsa yadda wasu ’yan siyasa ke yabo da fadanci a gaban Buhari, amma daga bisani su sauya baki sheƙa da zarar shugabannin sun bar mulki. Ya ce, “Tun da na zama gwamna, na ga abin da son kai da kwaɗayi ke iya haifarwa. Na ga mutane suna zaune a gaban Shugaba Buhari...
      Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matukar bakin ciki game da wannan lamarin.   Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ya yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasu da kuma dukkan al’ummar Nafada, yana addu’ar Allah ya jikan mamatan. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum October 26, 2025 Labarai “Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA” October 26, 2025 Manyan Labarai Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano October 26, 2025
    Shugaban majalisar Mohammad Baqer Qalibaf ya bayyana cewa, wasika ta hadin gwiwa da Iran, Rasha da China suka aike wa Majalisar Dinkin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan, da ke adawa da yunkurin Turai na sake dawo da takunkumi kan Iran wannan ya nuna hadin gwiwa mai karfi a tsakanin manyan kasashen uku. Ya yi wannan jawabin ne a lokacin wani zaman majalisa a Tehran a ranar Lahadi, mako guda bayan da kasashen uku suka mika wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Kwamitin  Tsaro wasikarsu, inda suka tabbatar da kawo karshen aikin kuduri mai lamba 2231, wanda ya amince da yarjejeniyar nukiliya ta 2015 wadda Amurka ta yi watsi da ita. “A cikin ‘yan kwanakin nan, mun shaida...
    Sakataren Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, ya tabbatar da cewa Hizbullah ta shirya don fuskantar isra’ila, yana mai bayyana cewa duk da cewa ba su da niyar fara yaki, amma suna shirye su kare Lebanon idan yaki ya barke. Sheikh Qassem a zantawarsa da tashar Al-Manar TV ya jaddada cewa idan aka tilasta musu yin yaki, tabbas  za su fuskanci Isra’ilawa da dukkanin karfinsu, kuma ba za su bar Isra’ila ta mamaye kudancin Lebanon ba,ko da kuwa hakan zai kai ga shahadarsu ne baki daya. Ya yi ishara da irin ayyukan wuce gona da iri da isr’ila ke yi akullum rana ta allaha  kan kasar Lebanon a kan idanun duniya, wanda hakan ya yi hannun riga da yarjejeniyar dakatar dayaki da...
    An zabi Catherine Connolly a matsayin shugabar Ireland a wani gagarumin sauyi na siyasa a Ireland, wanda hakan ke a matsayin wani lokaci na tarihi ga siyasar neman sauyi a Ireland. Connolly, ‘yar majalisa mai shekaru 68 daga Galway, ta lashe sama da kashi 64% na kuri’un da aka kada a zaben shugaban  Ireland, wanda ya ba masu nazarin siyasar yankin  mamaki matuka, ta yadda ta kayar da manyan jam’iyyun da fitattun ‘yan siyasa. Lokacin da ta kaddamar da Takara  a watan Yuli, an yi wa Connolly kallon bakuwa a yunkurinta na neman shugabancin Ireland, ‘yar majalisar dokoki mai sassaucin ra’ayi da neman sauyi, ta samu goyon bayan kananan jam’iyyun adawa kamar Social Democrats, Labour, da People Before Profit. Duk...
    Wani babban kusa na Hamas ya jaddada kudirin kungiyar na tabbatar da tsagaita wuta a Gaza, yana mai jaddada cewa Falasdinawa ba sa neman komai illa ‘yancinsu na samun cin gashin kai a duniya. Khalil Al-Haya, shugaban Hamas a Gaza, ya fadi a wata hira da aka watsa ranar Lahadi cewa bangaren Falasdinawa yana da babban kuduri tare da tabbatar da cewa ba zasu baiwa Israla wata dama ta samun hujjar dawowa da yaki a kan al’ummar Gaza ba. Ya kara da cewa, “Al’ummar duniya, wadanda suka shahara da kuma wadanda suka yi aiki a hukumance, ba za su bari Isra’ila ta sake halasta mamayarta a kan Gaza ba. Ya kara da cewa, Hamas ta yi matukar jajircewa kan yarjejeniyoyin...
    Dakarun sa kai na Jama’a a Arewacin Darfur  sun fitar da wata sanarwa a ranar Lahadi suna  musanta rahotannin kafofin watsa labarai game da faduwar birnin El Fasher a hannun Dakarun RSF, tare da bayyan hakan a matsayin farganda da kuma yakin kwakwalwa. Sanarwar ta ce, “A halin yanzu ana fuskantar wani kamfen na kafofin watsa labarai na ƙarya da nufin tayar da hankali da kuma karya zukatan mayakan, idan aka yi la’akari da cewa kwace hedikwatar rundunar na nufin faduwar birnin baki daya.” Sanarwar ta jaddada cewa “El Fasher shi ne shinge kumakatangar karfe da ta hana makiya kaiwa ga mafarkinsu. Sanarwar ta zo ne sa’o’i bayan da Rundunar RSF ta sanar da ikonta na hedkwatar sojojin sa kai...
    Duk da saukar farashin abinci a kasuwanni a sassan Najeriya, manoma na kokawa cewa sun shiga damuwa saboda asarar da suka tafka na kuɗaɗen da suka kashe wajen noma gonakinsu, lamarin da suka ce ya rage musu ƙwarin gwiwa su ci gaba da sana’ar. Wasu daga cikin manoman da wakilinmu suka zanta da su sun ce sun adana amfanin gona tun shekarar bara suna jiran farashi ya tashi, amma hakan bai faru ba, illa ƙara faduwa da farashin ya yi. A watan Satumban 2024 Gwamnatin Tarayya ta buɗe ƙofa na kwanaki 150 don shigo da hatsi kamar shinkafa, dawa, masara da alkama daga ƙasashen waje ba tare da biyan haraji ba, domin rage tsadar abinci. Amma wannan shigo da kaya...