Yemen Ta Nutsarda Wani Jirgin Ruwana HKI Saboda Sabawa Haramcin Wucewa Ta Red Sea
Published: 10th, July 2025 GMT
Labaran da suke fitowa daga kasar Yemen sunn bayyana cewa sojojin ruwan kasar sun nutsar da wani karin tankar dakon mai mallakin HKI a cikin tekun Red sea. Sojojin kasar sun bayyana cewa jigin ya sabawa Haramcin don haka sun tsutsar da ita. Sun yi haka ne don nuna goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu wadanda ake zalinta a Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jirgin yana nufin zuwa ummu Rash Rash ko Ilat kamar yadda yahudawan suke kiransa.
Sojojin kasar Yemen sun kara da cewa sun dauki wannan matakin kan jirgin ne bayan an gargade shi da ya koma amma yaki sauraro. Da wannan talilin sojojin ruwa na kasar yemen suka yi amfani da jiragen da ake sarrafasu daga nesa suka kaiwa jirgin mai suna ;ETERNITY C hare-hare sun tare da amfani da makamai masu linzami samfurin har ya nutse a cikin ruwa.
Labarin ya kara da cewa basu kashe wani ba, sai dai sun kama masu aiki a jirgin zu raka su zuwam kan tudu.
Labarin ya kammala da cewa wannan halin zai ci gaba har zuwa lokacin da HKI zata daina kissan Falasdinawa a Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HKI: Sojoji 62 Ne Su Ka Halaka A Gaza A Cikin Wannan Shekara Ta 2025
Jaridar HKI ta “Haaretz'” ta buga labarin da yake cewa: A cikin wannan shekarar ta 2025, sojojinsu da su ka halaka sun kai 62.
A cikin watannin bayan nan an sami karuwar sojojin mamayar da ‘yan gwgawarmaya suke kashewa a Gaza.
Yankin Khan Yunus dake Arewacin Gaza da HKI take riya cewa ta nike shi, sannan kuma ta kori Falasdinawa daga cikinsa, yana daga cikin wuraren da aka yi wa sojojin mamayar kwanton bauna.
Bugu da kari, har yanzu ‘yan gwgawarmayar suna ci gaba da harba makamai masu linzami daga Gaza zuwa matsugunan ‘yan share wuri zauna da suke kusa da Gaza.
A jiya ma dakarun “Sarayal-Quds” na kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da harba makamai masu linzami zuwa matsugunan da suke da Gaza.
Jaridar ta “Haaratz’ ta kuma ce, Fira ministan na HKI bai yi wa iyalan ko daya daga cikin iyalan sojojin da aka kashe a Gaza ta’aziyya ba, balle ya gana da su.
Jaridar ta kuma ce, hotunan da ake nunawa na Netanyahu yana ganawa da iyalan sojoji tsoho ne ba sabo ba ne.