IRGC: Duk Wani Wuce Gona Da Iri Na ‘Yan Sahayoniya Zai Gaggauta Rushewarsu
Published: 5th, July 2025 GMT
Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce gona da iri, zai gaggauta zuwa karshensu ne.
Sanarwar ta kuma ce: Muna tunawa ne da zagayowar cikar shekaru 42 daga wancan aikin ta’addanci, da a yanzu kwanaki kadan ne su ka wuce na kawo karshen yakin da HKI da Amurka su ka kallafa mana na tsawon kwanaki 12. Yaki ne wanda martani mai karfi da jamhuriyar musulunci ta Iran ta mayar yake kara fito da raunin da wannan kirkirarriyar kasa take da shi.
Har ila yau bayanin na dakarun kare juyin musulunci na Iran ya bayyana yadda jamhuriyar musulunci ta Iran ta yi ta kokari a fagen diplomasiyya akan batun jami’an diplomasiyyar da Isra’ila ce ta sace su ta hanyar ‘yan korenta,kuma hatta babban magatakardar MDD a 2008 ya bayyana cewa a shirye yake ya bayar da hadin kai domin ganin an warware batun,amma kuma abin takaici har zuwa yanzu wadanda su ka aikata laifin ba su fuskanci sakamakon da ya dace da su ba.
A dalilin haka dakarun kare juyin musuluncin suke kara tunatar da MDD da kuma kungiyar agaji da “Red Cross” da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu akan wannan batun. jami’an diplomasiyyar da HKI ta yi garkuwa da su sun hada janar Alhaj Ahmad Mutawassiliyan, sai Sayyid Muhsin Musawi, Taki Rastigar Mukaddam, da kuma Kazim Akawan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur.
Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki.
Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya.
“Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama. Ko da Atiku da magoya bayansa ba su yadda ba, ’yan Nijeriya suna ganin sauyin,” in ji Onanuga.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma zargi Atiku da jam’iyyar PDP da yaɗa maganganun da za su kawo tashin hankali.
Ya bayyana cewa yawancin matsalolin da ake fuskanta sun samo asali ne daga rashin kyakkyawan shugabanci tun a lokacin PDP, lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp