An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin
Published: 29th, October 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin Pei Xiaofei ya bayyana a yau cewa, yanayin ruwa da na iska a kasar ya ci gaba da ingantuwa a cikin watanni 9 na farkon bana.
A cewarsa, matsakaicin nauyin burbushin abubuwan dake cikin iska na PM2.5, wanda shi ne muhimmin ma’aunin gurbatar iska, ya tsaya kan microgram 26 kan kowane cubic mita, a cikin birane ko garuruwan Sin 339, daga watan Janairu zuwa na Satumba, wannan ya nuna cewa an samu raguwar ma’aunin da kaso 5.
Haka kuma, cikin watanni 9 na farkon bana, an samu ingantacciyar iska a kaso 87.6 na kwanakin, wanda ya karu da maki kaso 1.8 kan na bara.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa a wannan lokaci, an kasa kaso 89 na matattarar ruwa 3,641 dake karkashin kulawar kasar Sin bisa matakin inganci daga 1 zuwa III, wanda ke nuna ingancinsu, wanda ya karu da kaso 0.5 kan na makamancin lokacin a bara. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa
Wani abun lura ma a nan shi ne yadda a matsayinta na kasa mai tasowa ta farko a tarihin duniya da ta cimma nasarar samun wadata cikin lumana, Sin ta samar da wata taswira mai inganci, wadda sauran kasashe masu tasowa za su iya bi domin raya kansu cikin lumana, kuma karkashin hakan ne take ta fitar da shawarwari na ingiza ci gaban duniya bi da bi, irinsu shawarar raya jagorancin duniya da kasar ta gabatar a baya bayan nan. Shawarar da masharhanta da yawa ke ganin na da ma’anar gaske, wajen ingiza adalci, da daidaito a tsarin cudanyar mabanbantan sassan duniya.
A gani na tun da har kasar Sin ta kai ga gina tsari mai gamsarwa na raya kai bisa salon musamman mafi dacewa da yanayinta, wanda kuma yake ta kara samun karbuwa tsakanin kasashen duniya, a halin yanzu, kasar na kan wani matsayi na rarraba kwarewarta tare da sauran abokan tafiya, musamman kasashe masu tasowa. Wanda hakan kyakkyawan misali ne da dukkanin wata kasa a duniyan nan za ta iya lura da shi, yayin da take kokarin bunkasa kanta gwargwadon yanayin da take ciki.
Tabbas, ci gaban kasar Sin mai ban mamaki ya nunawa duniya cewa, kowace kasa na iya samun ci gaba ba tare da murdiya, muzgunawa wasu sassa, ko nuna karfin iko na siyasa ko tattalin arziki ba, maimakon hakan kasar Sin ta nunawa duniya cewa abu ne mai yiwuwa, a samu ci gaba bisa hadin gwiwar cimma moriya tare, ta yadda za a gudu tare a kuma tsira tare.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA