Sassauci na yi wa Maryam Sanda ba afuwa ba — Tinubu
Published: 29th, October 2025 GMT
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi sassauci wa matar nan da kotu ta yankewa hukuncin kisa bayan samunta da laifin kashe mijinta, Maryam Sanda.
Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban kasar ya janye sunan Maryam Sanda daga cikin jerin waɗanda ya yi wa afuwa a kwanakin baya.
Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin Afrika An kashe mutum 2 a rikicin limancin masallacin Juma’a a TarabaAna iya tuna cewa, a farkon watan Oktoba nan ne dai shugaba Tinubu ya yi wa wasu mutum 175 afuwa da suka haɗa da matattu da masu rayayyu.
Abin da ya fi daukar hankali a lokacin da aka sanar da afuwar shi ne ganin sunayen mutanen da suka aikata manyan laifuka, cikin wadanda aka yafewa, musamman manyan masu ta’ammali da fataucim miyagun kwayoyi, da masu kisan kai, da masu garkuwa da mutane, da masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, da gaggan masu cin hanci da rashawa.
Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba ta ce bayan tuntuba da tattaunawa da Majalisar Magabata ta Kasa da jin ta ra’ayoyin mutane a kan lamarin, Shugaba Tinubu ya ba da umarnin sake nazarin jerin sunayen mutanen da aka yi wa afuwar karkashin dokar da ta ba shi iko ta sashe na 175 (1) da (2) ta Kundin Tsarin Mulkin 1999.
Sabon jerin sunayen mutanen ya ƙunshi mutum 116, inda aka kasa su gida uku — waɗanda aka yi wa afuwa da waɗanda aka yi wa sassauci da kuma waɗanda aka yi afuwa amma ba a wanke su ba.
Mutum 50 shugaban ya cire sunayensu daga cikin waɗanda ya yi wa afuwar, ciki har da Maryam Sanda.
Sanarwar ta ambato cewa Maryam Sanda za ta ci gaba da zaman gidan yari har na tsawon shekaru shida nan gaba—jimilla shekaru 12 ke nan — maimakon ta fuskanci hukuncin kisan da aka yanke mata tun farko.
Maryam wadda aka ɗaure a shekarar 2020 yanzu haka ta yi shekaru shida, inda ake sa ran nan da shekaru shida za ta shaƙi iskar ’yanci.
Jerin sunayen ciki har da Maryam Sanda ya ƙunshi mutum 86 da aka sassautawa hukuncin da aka yanke musu, inda masu hukuncin kisa ya koma ɗaurin rai da rai sannan wasu kuma aka rage musu yawan shekarun da za su yi a gidan wakafi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Afuwa Maryam Sanda Maryam Sanda yi wa afuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
Wani dan sandan mai suna Ahmed Tukur ‘Yantumaki ya yi batan dabo yayin da yake a bakin aikinsa a Babban Ofisishin ‘Yan sanda na Karamar Hukumar Danmusa da ke Jihar Katsina.
Bayanai sun nuna cewa, a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2025 jami’in ya je bakin aiki inda ya ajiye jikkarsa da kular abincinsa a ofishinsu da ke cikin garin Danmusa sanna ya sanya hannu a kan rajistar kama aiki ta wannan rana, kuma ya nemi izni ya fita da nufin zai je ya sawo wani abu waje. Inda tun daga wannan lokaci ba’a sake ganinsa ba har kawo yanzu.
Da Aminiya ta tuntubi mahaifinsa mai suna Malam Tukur ‘Yantumaki don jin ta yadda ya samu labarin batan dansa sai ya ce, shi ma sai bayan kwana biyu da faruwar lamarin ne ‘yan sanda suka fada masa.
Malam Tukur ya ce, “’yan sandan ne da kansu suka zo har nan cikin gidana a karkashi jagorancin Babban Jami’in ‘Yan sanda na Karamar Hukumar Danmusa, DPO Isah Sule. Kuma shi ne ya fada min cewa, dana ya je aiki kwana biyu da suka wuce ya ajiye kayansa sannan ya sa hannu ya fita waje da nufin zai sawo wani abu amma ba a sake ganinsa ba.”
Ya ci gaba da cewa, “ya kuma bayyana min cewa, suna bakin kokarinsu don ganin sun gano shi don haka mu taya su da addu’a kuma mu sauke Alkur’ani. Ya kuma bayyana min cewa, sun yi ta kiran wayoyinsa amma ba sa samun, saboda duk wayoyin dana a kashe suke, sun ce, kuma duk lokacin da suka yi kokarin tirakin din layikansa sai na’urar binciken ta nuna masu ba ta iya ganin inda yake.”
Da yake wa Aminiya karin bayani yayan jami’in dan sandar da ya bata mai suna Ibrahim Tukur ya ce, “tun ranar da suka zo suka fada mana zancen batansa har yau babu wanda ya sake tuntubarmu game da zancen. A namu bangare, mun yi kokarin sanya labarin batansa a kafafen sada zumunta kuma mun samu wasu manyan don su taimaka mana su yi wa Kwamishinan ‘Yan sanda naJihar Katsina bayanin halin da ake ciki. Kuma muna nan muna kara jira mu ji bayanan da za su dawo mana das u tunda yake sun yi alkawari taimakawa.”
A cikin damuwa mahaifin dan sandan da ya bata wanda tunanin abin day a faru da dansa ya sa rashin lafiya ta kama shi yana kwance ya sheda wa Aminiya cewa, “ ina kira da babbar murya ga Gwamna Jihar Katsina Dakta Dikko Radda da Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Katsina da su tabbatar sun gano min dana kuma sun dawo min da shi cikin ‘yan’uwansa lafiya, su tuna wannan hakki ne a kansu.
“Bai yiyuwa a ce, mutum kuma jami’in dan sanda da suka ce mana ma a lokacin da ya bace yana dauke da bindigarsa kuma a tsakiyar gari, wato tsakanin ofishin ‘yan sanda zuwa masallacin Juma’a ya bace kamar wata dabba. Ba duriyarsa ba kuma wani bayani gamsasshe ballanata kuma wani nuna damuwa daga bangarensu.”
Ya kara da cewa, “ba a gano inda yake ba, babu wanda ke yi min bayani game da inda yake, a gaskiya ma babu wanda ya nuna wata damuwa sosai daga bangaren gwamnati. Shin hakan yana nufin babu wanda ya damu da shi a matsayin dan sanda kuma babu wanda ya damu da mu a matsayinmu na talakawa? Shin haka kuwa labarin zai kasance idan da a bin ya faru da daya daga cikin ‘ya’yansu ne?”
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin jami’an ‘yan sanda na Jihar Katsina, inda ta farad a kiran DPO Isah Sule na Karamar Hukumar Danmusa amma hakan ya ci tura, domin layin wayarsa baya shiga sannan kuma bai bayar da amsar sakon da aka tura masa a waya ba.
Haka kuma Mai Magana da Yawun ‘yan sandar Jihar Katsina DSP Abubakar Sadik Aliyu wanda wakilin Aminiya ya tura wa sakon kart a kwana ba tare day a maido da amsa bat un jiya, daga bisani amsa kiran waya inda ya bayyana wa wakilinmu cewa, ya yi tafiya amma zai bincika yadda lamarin yake sannan ya yi bayani.