Gwamna Lawal Ya Yi Ta’aziyyar Sarkin Katsinan Gusau
Published: 25th, July 2025 GMT
“Rasuwar Sarkin Zamfara babban rashi ne ga al’ummar jihar Zamfara, Arewa da ma ƙasar nan baki ɗaya.
“Sarkin ya sadaukar da rayuwar sa a shekarun nan 10 da ya ya yi hana mulki a matsayin Sarkin Gusau na 15, wanda ya hau a ranar 16 ga watan Maris na shekarar 2015. Ya yi mulki cikin jajircewa da sadaukarwa.
“Marigayin, kafin ya zama Sarki, ƙwararren ma’aikacin gwamnati ne, wanda har sai da ya kai matsayin Babban Sakatare a gwamnatin tsohuwar jihar Sakkwato da ta Zamfara.
“Na rasa murshidin Uba mai basira, wanda ke nuna mani hanya, tare da sauran shugabanni a jiha. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuran sa, ya sa aljanna ce ce makoma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
A Kalla Falasdinawa 10 Yunwa Ta Kashe A Gaza A Cikin Sa’o’i 24
Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata adadin falasdinawan da su ka yi shahada saboda yunwa sun kai 10.
Daga lokacin da HKI ta fara amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,adadin falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 111.
Wannan adadin yana nuni da yadda rashin abinci ya tsananta a cikin yankin na Gaza saboda yadda Isra’ila ta killace yankin ta hana a shigar da abinci a ciki.
A gefe daya, HKI tana ci gaba da kashe Falasdinawa ta hanyar yi musu kisan kiyashi, da a yau kadai fiye da mutane 80 ne su ka yi shahada. Mafi yawancin wadanda su ka yi shahada a cikin sa’oin nan na baya suna a unguwannin Tallul-Hawa, da Deir-Balah. Haka nan kuma ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a sansanin ‘yan hijira dake Mukhayyam-Shadhi.
Kungiyoyin kasa da kasa suna ta ci gaba da yin kira da a bude iyakokin Gaza domin a shigar da kayan abinci, sai dai babu faruwar hakan.
A cikin zirin Gaza dai, mutane suna faduwa suna somewa, wani lokaci mutuwa saboda yunwa, ba kuma babba babu yaro.
Mafi yawancin mutanen da suke mutuwa dai kananan yara ne, jarirai da matasa.