Duk da ce-ce-ku-ce sunan Maryam Sanda na cikin wadanda Tinubu ya yi wa afuwa
Published: 29th, October 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu, ya janye afuwar da ya yi wa wasu wadanda suka hada da masu manyan laifuka kamar kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi da sauransu.
A baya dai wasu sun yi ta suka da ce-ce-ku-ce kan sanya sunan Maryam Sanda cikin wadanda shugaba Tinubu ya yi wa afuwa.
Tinubu ya janye afuwar da ya yi wa Maryam Sanda da masu manyan laifuka Super Falcons ta samu gurbin buga Kofin AfrikaDuk da maganganun mutane sunan Maryam Sanda na cikin sabon jerin sunayen wadanda aka bari, bayan cire wasu.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar a ranar Laraba cewa an cire sunan aƙalla mutum 50 daga tsohon jerin sunayen da aka fitar bayan ce-ce-ku-cen jama’a.
“Bayan martanin jama’a, Shugaba Tinubu ya umarci a cire sunayen waɗanda aka samu da manyan laifuka kamar garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, da fataucin mutane daga jerin waɗanda aka yi wa afuwa,” in ji Onanuga.
Ya ƙara da cewa an ɗauki wannan mataki ne “don mutunta ra’ayoyin jama’a, inganta haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro, da tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa da al’umma baki ɗaya.”
Tsohon jerin sunayen da aka fitar ya haifar da cece-kuce a tsakanin jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam.
Sun bayyana matakin a matsayin amfani da ikon shugaban ƙasa ta hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan barazana ce ga tsarin shari’a.
Sun yi gargaɗin cewa sakin waɗanda suka aikata manyan laifuka zai iya ƙarfafa aikata laifi da kuma rage wa doka tasiri.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Afuwa Maryam Sanda manyan laifuka Maryam Sanda
এছাড়াও পড়ুন:
An kai hari gidan jami’in ɗan sanda a Yobe
Wasu mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari gidan babban Jami’in kula da ofishin ‘yan sandan na Tattaɓa, ASP Mohammed Modu, da ke yankin Bara a ƙaramar hukumar Gulani, Jihar Yobe.
Kamar yadda rahoton Jami’an tsaro ke nunawa cewa, da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar daren ranar 9 ga Disamba, maharan suka mamaye gidaje uku na jami’in, suka sace babur ɗinsa na Haojue da kekuna uku da mota ƙirar Golf 3, da sauran kayansa kafin su ƙona gidaje uku da motar Honda Civic.
Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin mota Manchester United ta shiga zawarcin Sergio RamosAn yi zargin cewa, wani mai kai rahoto ne ga ‘yan ƙungiyar da ke cikin al’ummar wannan yankin ya bada rahoton Jami’in ga waɗannan maharan.
Jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru kuma sun tattara bayanai game da ɓarnar, ba tare da an samu rahoton asarar rayuka ba.
An shawarci jami’in da ya yi taka-tsantsan yayin da ake ƙara tsaurara sa ido da sintiri a yankin don hana sake kai hari a yankin.