Aminiya:
2025-07-12@20:10:59 GMT

Sanatan Abuja ta sauya sheƙa zuwa ADC

Published: 12th, July 2025 GMT

Sanata Ireti Kingibe, wacce ke wakiltar Babban Birnin Tarayya, ta fice daga jam’iyyar LP zuwa ADC.

Da ta ke magana da ’yan jarida a Abuja, ta ce wannan matakin nata wani shiri ne na tunkarar babban zaɓen 2027.

Abin da ya faru tsakani na da DSS bayan kama ni — Ɗan Bello DSS ta saki Ɗan Bello bayan ta kama shi a Kano

“Ni cikakkiyar mamba ce ta ADC yanzu,” inji ta.

Da aka tambaye ta ko tana da ƙwarin gwiwa game da shugabancin ADC da haɗin gwiwar da suke ƙoƙarin ginawa, ta ce jam’iyyar na ci gaba da samun tagomashi.

Tace kowace tafiya a sannu ake binta wanda daga bisani ta ke girma.

Wasu sun nuna damuwa cewa wannan sauya sheƙar na iya sawa ta rasa kujerarta a Majalisar Dattawa.

Amma Kingibe, ta ce jam’iyyar LP yanzu ta kasu gida biyu, wanda hakan ya sa ta bar jam’iyyar bisa ga kundin tsarin mulkin ƙasa.

Ta ce: “Ina roƙonku ku karanta kundin tsarin mulki. Akwai rarrabuwar kawuna a jam’iyyar LP, kuma wannan shi ne cikakken sharaɗi da kundin tsarin mulki ya bayar na yadda mutum zai iya sauya sheƙa ba tare da hukunci ba.”

“Idan kuna so na ci gaba da zama a jam’iyyar LP, wacce daga cikin ɓangarorin biyun kuke so na zauna a ciki?

“Har INEC sai da ta samu sakamakon zaɓe daga ɓangarori biyu na LP, kodayake ba su amince da kowane ba.”

Ta ƙara da cewa: “Ko da babu irin wannan rabuwar kan, kun taɓa ganin an tilasta wa wani barin kujerarsa?

“Amma ni ina bin doka. Da babu rabuwar kawuna a LP, da ba zan sauya sheƙa ba. Amma yanzu akwai, shi ya sa kundin tsarin mulki ya ba ni dama. Kuma na zaɓi ADC.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sauya Sheƙa kundin tsarin jam iyyar LP

এছাড়াও পড়ুন:

Jihohi 10 Sun Kinkimo Bashin Naira Biliyan 417 Duk Da Karin Samun Kudaden Shiga

Kididdigar ta nuna cewa maimakon amfani da wannan kudaden shigar don rage basussuka, wasu jihohi suna kara amso bashin. Jihar Ribas ta zama ta farko a jerin jihohin da adadin bashin cikin gida na naira biliyan 364.39 a wata uku na farkon 2025, mafi girma tsakanin jihohi 10.

Basukan Jihar Inugu sun tashi daga naira biliyan 82.48 a farkon wata uku na 2024 zuwa naira biliyan 188.42 a farkon wata uku na 2025, wanda ke nuna karuwa na naira biliyan 105.95 ko kashi 128.4 cikin dari.

Jihar Neja ta biyo baya da karuwar naira biliyan 57.68 a kowanne shekara, daga naira biliyan 86.07 zuwa naira biliyan 143.75, wanda shi ne karuwa na kashi 67 cikin 100.

Jihar Taraba ta nunka bashin cikin gida har sau biyu daga naira biliyan 32.64 zuwa naira biliyan 82.93, wanda hakan ke nuni da karuwar naira biliyan 50.29 ko kashi 154.1 cikin dari a kowace shekara.

Jihar Bauchi ta kara bashinta daga naira biliyan 108.39 zuwa naira biliyan 142.40, wanda ya nuna karuwar kashi 31.4 cikin dari a kowanne shekara.

Jihar Benuwai ta samu karin naira biliyan 13.09 a kowanne shekara, daga naira biliyan 116.73 zuwa naira biliyan 129.82, wanda ke nuna karuwar kashi 11.2 cikin dari.

Jihar Gombe ta kara bashinta ya tashi daga naira biliyan 70.81 zuwa naira biliyan 83.66b a kowanne shekara, wanda ya karu da naira biliyan 12.85 ko kashi 18.1 cikin dari.

Jihar Edo, wacce ke da bashi na naira biliyan 72.38 a farkon wata uku na 2024, ya karu zuwa naira biliyan 82.40 a farkon watanni ukun na 2025, karin naira biliyan 10.02 ko kuma kashi 13.8 cikin 100.

Jihar Kwara ta kara bashinta daga naira biliyan 59.07 zuwa naira biliyan 60.10 a kowanne shekara, karuwa ta naira biliyan 1.03 ko kashi 1.7 cikin dari.

Jihar Nasarawa, ta karawa bashita daga naira biliyan 23.76 zuwa naira biliyan 24.73bn a kowanne shekara, wanda ke nuna karin naira miliyan 968 ko kashi 4.1 cikin dari.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Gabatar Da Matsayin Jihar A Zaman Nazarin Kundin Tsarin Mulki
  • Sanatar Abuja ta sauya sheƙa zuwa ADC
  • Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • Muna tunanin sayar da matatun man Najeriya — NNPCL
  • Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa
  • Jihohi 10 Sun Kinkimo Bashin Naira Biliyan 417 Duk Da Karin Samun Kudaden Shiga
  • An Koka Kan Yadda Tsafi Da Jariran Da Aka Haifa Da Tsagaggen Lebe Ke Karuwa
  • Hadarin Da Ke Kunshe Da Jin Bangare Daya Na Labari
  • Shirin Sabunta Fata Na Tinubu Yana Samar da Damarmakin Cigaba — Minista