Yawan Cire Haraji Ya Sa Albashinmu Babu Albarka – SSANU
Published: 15th, March 2025 GMT
Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi ta nuna rashin jin dadinta da wasu manufofi na Gwamnatin tarayya musamman ma irin nau’oin harajin da ake cirewa duk wata ya maida albashinsu ya kasance tamkar miyar da babu Gishiri bare Maggi ko kuma Daddawa, shi yasa karin da aka yi na mafi karancin albashi na Naira 70,000 ya zama tamkar tafiyar Kura ne inda take yin Gaba ta kuma koma Baya.
Wannan bayanin ya fito ne bayan da aka kammala taron kwamitin zartarwa na kungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi na 50 wanda aka yiu a Jami’ar Gwamnatin tarayya ta Otuoke, Jihar Bayelsa, inda kungiyar ta nuna damuwarta kan manyan lamurra wadanda suke damuwar jin dadin ‘yan kungiyarta,kamar yadda ake samun toge a albashi inda bai kaiwa yadda ake tsammani ko sabawa da ganin hakan, akawus – alawus wadanda aka ki biya, yadda wasu Malamai mata ake neman cin mutuncinsu ta hanyar neman yin fasikanci da su, lalacewar ko rashin abubuwan jin dadin rayuwa a Jami’oi inda wadansu sun gama lalacewa gaba daya.
A takardar jawabin bayan kammala taron wadda take dauke da sa hannun Shugaban kungiyar na kasa Komrade Mohammed Haruna Ibrahim, “mambobin kwamitin zartarwar kungiyar sun nuna rashin jin dadinsu kan abinda suka kira da yawan nau’oin harajin da ake cire masu kowane wata abin ya yi yawa.Kamar yawan albashinka dai dai da yadda za a cire ma haraji mai gwabi (PAYE)Uwa Uba kuma ga karuwr harajin (VAT)wanda babu irin bayanin da za ayi wanda zai gamsar da ita kungiya bare mambobinta.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
Gwamnan Jihar Filato, Barr. Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa babu wata ƙaramar hukuma a cikin jihar da ƴan ta’adda ko ƴan bindiga ke da iko da ita. Ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ƴan jarida da aka gudanar a sabon gidan gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a ranar Talata.
Gwamna Mutfwang ya ce gwamnatinsa ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar tsaro, musamman ta hanyar farfaɗo da rundunar tsaron cikin gida ta jihar wato Operation Rainbow, domin tallafa wa sauran hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ana Ci Gaba Da Alhinin Mutuwar Malam Adamu Fika Sojoji Sun Ƙi Karɓar Cin Hancin Miliyan 13 Daga Ƴan Ta’adda A FilatoYa ƙara da cewa, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an dawo da zaman lafiya a sassan jihar da rikice-rikicen ƙabilanci ko na addini suka taɓa. Ya ce gwamnati na aiki tare da hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya domin tabbatar da fahimtar juna da daidaiton al’umma.
Gwamnan ya sake jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya. Ya ce kafa ƴansandan jiha zai bai wa gwamnatocin jihohi damar yin tsari da ɗaukar matakan da suka dace da yanayin tsaron yankunansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp