Ma’aikatar Cinikayya Ta Sin Ta Yi Karin Haske Game Da Soke Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Sin
Published: 5th, July 2025 GMT
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu, dangane da soke takunkumin tattalin arziki da cinikayya da kasar Amurka ta kakabawa kasar Sin.
Kakakin ya ce, bayan tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a birnin London na kasar Burtaniya, cikin ’yan kwanakin nan, bangarorin biyu sun aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ranar 5 ga watan Yuni, tare da inganta ayyukan da abin ya shafa bisa sakamakon da suka cimma a taron tattaunawar tattalin arziki da cinikayya na Geneva.
Da kyar bangarorin biyu suka cimma matsaya daya tare da kulla “tsarin London”, don haka ya kamata a bi hanyar yin shawarwari, maimakon kalubalanta ko tilastawa wani. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
Daga Yusuf Zubairu Kauru
Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa.
Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda ‘yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.
A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada ‘ya’yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da ƙangin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.
Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai ɗauki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, waɗanda su ne ginshiƙin samar da abinci a yankin.
Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da ƙaruwar matsalar rashin abinci da yawaitar ƙaura daga yankin.
“Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala,” in ji wani manomi a yankin.
Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda ƙasar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al’ummar Kauru ba wurin binne su ba.