Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Masu Neman Karbar Kayan Agaji A Gaza
Published: 4th, July 2025 GMT
Sojojin mamayar Isra’ila sun mayar da cibiyoyin bada agaji zuwa filin yakin kashe Falasdinawa a Zirin Gaza
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da mayar da cibiyoyin bayar da agajin jin kai zuwa wani mummunan tarko na aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa, wanda hare-haren baya-bayan nan da suka kai kan fararen hula sunka yi sanadiyar hasarar rayuka da dama tare da jikkata wasu masu yawa.
Jiragen yakin gwamnatin mamayar Isra’ila da kuma amfaniu da manyan bindigogi suna barin wuta kan mai uwa da wabi kan Falasdinawa da suka taru domin karbar kayan jin kai. Gwamnatin mamayar Isra’ila ta bullo da wannan sabon hanya ce domin kashe Falasdinawa a matsayin tarko ga Falasdinawa, kuma ba ta sha yin ci gaba da wannan ta’asa domin babu mai iya hana ta ko tofin yin Allah wadai da ita.
Wani magidanci da ya dawo daga karbar agaji da ‘ya’yansa biyu a Khan Yunus, ya fuskanci bude wuta inda dansa guda ya yi shahada dayan kuma yana nan rai kwai-kwai mutum kwai-kwai.
A cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida da tsaron kasa a zirin Gaza ta fitar, ta jaddada cewa: Daruruwan Falasdinawa ne suka yi shahada sakamakon harsashin sojojin mamayar Isra’ila a wuraren bada agajin jin kai zuwa yanzu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba
Dangane da gamsuwa kan nasarorin da Sin ta samu a bangaren raya harkokin mata, kaso 72.8 na masu bayar da amsa a nazarin daga kasashe maso tasowa, sun yaba da kokarin Sin na horar da mata sana’o’i da tallafawa raya harkokin da suka shafe su. Game da nasarorin da aka samu a kasar Sin wajen shigar mata cikin harkokin raya tattalin arziki da zaman takewa da al’adu, da ma gudunmuwar kasar ga raya harkokin mata a duniya, wadanda suka bayar da amsa daga nahiyoyin Afrika da Asia da kudancin Amurka, sun bayyana gamsuwa matuka.
Kafar yada labarai ta CGTN da jami’ar Renmin ta Sin ne suka gudanar da nazarin wanda ya shafi muhimman kasashe masu ci gaba da ma kasashe masu tasowa. Sun gudanar da nazarin ne ta hannun cibiyar bincike kan harkokin kasa da kasa a sabon zamani. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA