Hadiman gwamnan Kano sun haura 300 bayan naɗa wasu sabbi 19
Published: 5th, July 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin wasu sabbin hadimai 19 da za su yi aiki a matsayin Manyan Mataimaka na Musamman domin ƙara inganta aikin gwamnati a jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Yanzu adadin hadiman da ke aiki da Gwamna Abba sun zarce mutum 300.
Hadiman sun haɗa da Masu Ba da Shawara na Musamman, Manyan Mataimaka na Musamman, Mataimaka na Musamman da kuma Masu Taimaka Masa.
Gwamnan ya fara naɗa hadimansa ne a ranar 16 ga watan Yunin 2023, inda ya naɗa mutum 14 ciki har da Manyan Mataimaka bakwai, Mataimaka na Musamman uku da Masu Taimaka Masa guda huɗu.
Daga baya, a ranar 18 ga watan Yuli, 2023, ya sake naɗa ƙarin mutum 15 a matsayin Masu Ba da Shawara na Musamman.
A ranar 7 ga watan Agusta, 2023, ya sake naɗa mutum 52, wanda ya kai jimillar hadimansa zuwa 81 a wancan lokaci.
A ranar 2 ga watan Satumba, 2023, ya sake naɗa ƙarin mutum 115; waɗanda suka haɗa da Masu Ba da Shawara 14, Manyan Mataimaka 57 da Masu Ɗaukar Rahoto na Musamman 44.
Hakazalika, a ranar 27 ga watan Satumba, ya sake ƙara mutum 94, wanda ya adadin ya kai zuwa 290.
Bayan haka, a ranar 29 ga watan Satumba, 2023, ya ƙara naɗa mutum 106; ciki har da Manyan Mataimaka 63, Mataimaka na Musamman 41 da wasu 12.
Yanzu kuma, ya sake naɗa mutum 19, wanda adadin hadimansa ya haura 300.
Daga cikin sabbin waɗanda ya bai wa muƙamai akwai Hon. Sunusi Kata Madobi da aka naɗa a matsayin Mataimaki na Musamman Kan Harkar Gidan Rediyo na I domin maye gurbin marigayi Abdullahi Tanka.
Mika’ilu Shu’aibu (Ghari) ya zama Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Hisbah, yayin da Muhktar Abdullahi Shuwaki (Ghari) ya zama Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Filaye.
Injiniya Sagir Lawan Waziri (Ghari) ya samu muƙamin Mataimaki na Musamman Kan Hakkokin Al’umma (Sashen Ayyuka).
An naɗa Najeef Abdulsalam a matsayin Mataimaki na Musamman Kan Masu Sana’o’i Maza, sai kuma Huwaila Iguda da aka naɗa a matsayin Mataimakiya ta Musamman Kan Masu Sana’o’i Mata.
Naziru Hamidu Bako ya zama Mataimaki na Musamman Kan Hukumar KAROTA, sai Usman Abbas Sunusi da zai riƙe matsayin Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Taruka na II.
Injiniya Usman Kofar Naisa zai kasance Mataimaki na Musamman Kan Filin Wasanni na Mahaha, yayin da Danladi Alhassan Mai-Bulala ya zama Mataimaki na Musamman Kan Wayar da Kai II.
Abdulkhadir Umar Kwankwaso ya samu muƙamin Mataimaki na Musamman Kan Harkar Ilimi (Abuja), sai kuma Balarabe Aminu Yusuf wanda aka daga darajarsa zuwa Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Gida III (Gidan Gwamnati).
Shukurana Garba Langel ya zama Mataimaki na Musamman Kan Wayar da Kai (Kano ta Arewa), sai Mustapha Ma’aruf Diso da aka naɗa Mataimaki na Musamman Kan Harkar Kiwon Lafiya A Matakin Farko (Primary Healthcare).
Garba Yahaya Labour ya zama Mataimaki na Musamman Kan Harkokin Sufuri na I, yayin da Humaira Sharif ta zama Mataimakiya ta Musamman Kan Wayar da Kan Mata.
Muttaka Sani Gaya, ya samu muƙamin Mataimaki na Musamman Kan Ƙungiyoyin Masu Goyon Bayan Gwamnati na III, Gausu Nuhu Wali ya zama Mataimaki na Musamman Kan Mawaƙan Gargajiya, sai kuma Hadiza Sale (Baby) da aka naɗa a matsayin Mataimakiya ta Musamman Kan Tsaftar Muhalli.
Gwamnatin Kano ta yi fatan sabbin hadiman za su yi amfani da ƙwarewarsu da kishinsu wajen taimakawa wajen cimma burin gwamnatin na mayar da hankali kan ci gaban jama’a da shugabanci na gari.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnan Kano Mataimaki na Musamman Kan Harkokin ya zama Mataimaki na Musamman Kan a matsayin Mataimaki Manyan Mataimaka ya sake naɗa da aka naɗa naɗa mutum
এছাড়াও পড়ুন:
Kamaru: Jam’iyyun adawa sun ayyana Bakary a matsayin wanda ya lashe zaɓe
Jam’iyyun adawa a ƙasar Jamhuriyar Kamaru sun ayyana Issa Bakary Tchiroma a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasar da gagarumin rinjaye.
Gamayyar jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin fararen hula na Union for Change ta ce sakamakon da suka tattara daga fadin ƙasar da ƙasashen waje ya nuna Bakary ya samu kashi 60 zuwa 80 cikin ɗari na ƙuri’u a rumfunan zaɓe da dama.
Sun buƙaci Shugaba Paul Biya, wanda ke neman wa’adin mulki na takwas a zaɓen da ya gaggauta miƙa saƙon taya murna ga Issa Bakary Tchiroma.
“Muna kira ga shugaban ƙasa mai barin gado da ya gaggauta taya sabon shugaban ƙasa murna,” in ji ƙungiyar,” in ji wata sanarwa da shugabannin ƙungiyar, Anicet Ekane da Djeukam Tchameni, suka fitar a birnin Douala.
Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph“’Yan Kamaru sun yanke shawara. Sakamakon da muke karɓowa daga sassan ƙasar da ma ƙetare ya nuna a sarari cewa, ɗan takarar talakawa, Issa Tchiroma Bakary, ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Oktoba 2025,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta zargi jam’iyyar mai mulki ta CPDM da ƙoƙarin amfani da “tsohuwar hanyar maguɗi,” amma ta ce duk da haka Bakary ya yi mata “mummunar kaye mara misaltuwa,”
Union for Change 2025 ta kuma roƙi hukumomin gwamnati da jami’an tsaro da su mutunta zabin al’umma da zaman lafiya, tare da kira ga ’yan ƙasa da su ci gaba da kasancewa cikin shiri domin kare zaɓinsu.”
Bakary, wanda tsohon minista ne a gwamnatin shugaba Paul Biya, an zaɓe shi a watan Satumba a matsayin “ɗan takarar haɗin kai na jama’a.”
Ƙungiyar, wadda rahotanni ke cewa ta ƙunshi fiye da ƙungiyoyi 50 na siyasa da na fararen hula, ta ce manufarta ita ce haɗa ɓangarorin adawa domin yin aiki tare wajen sauyin siyasa da sake gina ƙasa.
“Ƙungiyar Talakawa ce, wadda take buɗe ƙoa ga kowa — ɗan ƙasa ko ƙungiya, ciki har da waɗanda ’yan takararsu aka hana shiga zaɓen shugaban ƙasa ba bisa ƙa’ida ba,” in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta bayyana kanta a matsayin sabuwar ƙarfi na farfaɗo da dimokuraɗiyya, tana mai alƙawarin sake gina Kamaru a cikin lokacin canji na shekaru uku zuwa biyar.
A lokacin da ake rubuta wannan rahoto, Hukumar Ƙoli ta Ƙasar ba ta fitar da sakamakon hukuma ba, lamarin da ake ganin zai iya ƙara ɗaga zullumin siyasa a kwanaki masu zuwa.