Trump ya rushe kafar watsa labarai ta VOA
Published: 16th, March 2025 GMT
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA.
Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna.
Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani.
Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya.
Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin Amurka kan me hakan ke nufi, sannan babu wanda zai iya fahimtar ko an rufe kafofin baki ɗaya ke nan.
Shugaban ƙungiyar ’yan jarida a Amurka, William McCarren ya ce wannan ba abin alheri ba ne ga duniya da kuma aikin jarida baki ɗaya, musamman a wannan zamani da ake yaƙi da labaran bogi.
Tuni dai Shugaba Trump ya naɗa ’yar jarida Kari Lake a matsayin daraktar hukumar da za ta kula da rushe waɗannan hukumomi, waɗanda ya zarga da yaɗa labaran nuna masa ƙiyayya.
Sama da shekaru 80 ke nan da kafa VOA wadda ke yaɗa shirye-shiyenta cikin harsuna 40, ta rediyo da talabijin da intanet da shafukan zumunta na zamani.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, ɗaya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan ƙasar.
Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi — shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ke iya haifarwa a rayuwar talaka?
NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki” DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin ArewaA kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan