Mai shekara 70 ya kashe ƙanwarsa kan gadon gona a Jigawa
Published: 4th, July 2025 GMT
Wani mummunan lamari na kisan gilla ya afku a ƙauyen Galadanchi da ke Ƙaramar hukumar Dutse a Jihar Jigawa.
Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan filin gado.
Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a BornoCikin wata sanarwa da kakakin rundunar y’an sandan jihar, SP Lawan Adam Shi’isu ya fitar ya ce tsohon mai suna Adamu Yakubu – ɗan asalin ƙauyen Galadanchi ne wanda ya samu saɓani da ƙanwarsa mai suna Hannatu Hashimu, mai shekara 45, kan rabon gadon wata gona da suka gada.
Bayanan binciken farko da ’yan sanda suka fitar, ya nuna cewa wanda ake zargin ya jefi ƙanwar tasa da sanda ne a lokacin da suka yi zazzafar gardama a tsakaninsu kan rabon gadon.
Rikicin dai ya fara ne kamar da rashin jituwar musayar kalamai, amma ya rikiɗe zuwa tashin hankali.
Inda tsohon da ake zargin ya kai wa ƙanwar tasa duka da sanda, wanda ya yi sanadin mutuwar Hannatu Hashimu. Kamar yadda bayanan ’yan sanda ya nuna.
”Marigayiyar ta fita daga gidan a fusace, ta koma gidan aurenta, da zuwanta kuma ta faɗi ta suma, nan take aka garzaya da ita asibiti inda likitocin Babban Asibitin Dutse suka tabbatar da mutuwarta”, cewar ’yan sandan.
Rundunar ’yan sandan sun kama tsohon da ake zargin, inda yanzu haka suke gudanar da bincike.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Juventus ta ɗauki tsohon kociyan Italiya, Luciano Spalleti
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta naɗa Luciano Spalletti a matsayin sabon kociya bayan sallamar Igor Tudor da ta yi a farkon makon nan.
Juventus ta ƙulla yarjejeniya da tsohon kociyan na Inter Milan da Roma da Udinese da Zenit St Petersburg da kuma tawagar ƙasar Italiya, har zuwa ƙarshen wannan kakar, yayin da take fatan samu gurbin zuwa gasar Kofin Zakarun Turai ta Champions League ta baɗi.
Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – ZulumSpalletti, shi ne kociyan da ya jagoranci Napoli wajen lashe gasar Serie A a 2023, wadda ita ce karon farko cikin shekaru 33, inda a yanzu ake fatan zai ƙara daidaita Juventus da ke fama da rashin katabus da matsalolin kuɗi tun daga 2022.
Spalletti, wanda aka sani da ƙwarewa wajen gina ƙungiya mai ƙarfi, ya dawo horaswa bayan gazawar da ya yi a matsayin kociyan Italiya a gasar Euro 2024, da kuma shan kashi a hannun Norway yayin wasan farko na neman tikitin Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Zuwa yanzu dai Juventus tana matsayi na bakwai a gasar Serie A da tazarar maki shida tsakaninta da Napoli da ke saman tebur, inda wasan farko da Spalletti mai shekaru 66 zai ja ragama shi ne da Cremonese.