A bana ake bikin cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ana kuma daf da gudanar da sabon zagayen taron jagororin Sin da EU. Sakamakon hakan, jerin ayyukan cudanya a matsayin koli tsakanin sassan biyu na kara jan hankali.

A baya-bayan nan, an gudanar da dandalin tattaunawa na manyan jami’ai tsakanin Sin da EU karo na 13 a birnin Brussels na kasar Belgium.

Kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da shugabannin EU, tare da ziyartar kasashen Jamus da Faransa. Bangaren Sin ya jaddada cewa, bunkasar tafarkin ci gaban alaka tsakanin Sin da EU ya nuna kyakkyawar dangantakar sassan biyu maimakon adawa da juna, kuma hadin gwiwarsu shi ne tushen cimma nasara tsakaninsu. Kazalika, ya yi kira ga Sin da EU da su hada karfi waje guda don samarwa duniya wani yanayi na tabbaci.

Ya ce, matsayin alakar Sin da EU na manyan karfi biyu, kuma manyan kasuwanni biyu, kana manyan wayewar kai biyu, ya shaida damar musaya da hadin gwiwa, ba gare su kadai ba, har ma da dukkanin duniya baki daya. Jimillar karfin tattalin arzikin Sin da EU ya haura daya bisa ukun na duniya baki daya, kana darajar yawan cinikayyarsu ta haura daya bisa hudun ta duniya baki daya. Sassan biyu na rike da manufar cudanyar mabambantan sassa, suna goyon bayan cinikayya marar shinge, da wanzar da tattaunawa da tsare-tsaren gudanarwa kan muhimman batutuwa, irinsu sauyin yanayi da fasahohin AI. A halin da ake ciki, rikicin siyasar yankuna na kara tsananta, an kuma shiga yakin haraji da na cinikayya. Sin da Turai na da nauyi da hakki, da ikon hada hannu waje guda don kare adalci, da nuna adawa da cin zali daga bangare guda, da nuna kin jinin baiwa kasuwa kariya. Kamar dai yadda Sin ta bayyana, idan Sin da Turai sun wanzar da tattaunawa da hadin gwiwa, zai yi wuya a kai ga yin fito-na-fito tsakanin wasu sassa. Kazalika, idan Sin da Turai sun zabi bude kofa, da hadin gwiwar cimma moriya tare, hakan zai sauya salon dunkulewar tattalin arzikin duniya. Idan Sin da Turai sun hada hannu wajen aiwatar da manufar cudanyar mabambantan sassa, duniya ba za ta tsuduma cikin yanayi na hargitsi ba. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Sin da Turai

এছাড়াও পড়ুন:

An sa zare tsakanin ‘yan Kannywood da Alhikima

Tauraron Kannywood kuma mai sayar da maganin gargajiya, Abdullahi Alhikima ya magantu bayan da wasu ‘yan Kannywood suka caccake shi kan kalaman da ya yi a kansu.

Aminiya ta rawaito cewa hatsaniyar ta samo asali ne bayan fitattun ‘yan Kannywood da suka hada da Abdul M Sharif, Nura M Inuwa, Abubakar Bashir Maishadda, Sadik Sani Sadik, da sauransu suka kai wa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar ziyarar goyon baya.

Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba

Wannan ya tunzura Alhikma kasancewar wasu daga cikin wadanda suka je mubayi’ar ‘ya’yan kungiyar YBN ne a baya, da kuma 13/13 ta ubangidansa, mawaki Rarara.

A cikin wadanda Alhikima ya caccaka har da Shugaban Hukumar Fina-finai ta Ƙasa, Ali Nuhu.

Sai dai a kan hakan ne kuma wasu ke hasashen lallai ta tabbata alaƙa ta yi tsami tsakanin Alin da Rarara, wadanda a da suke abokai.

To sai dai Alhikman ya yi mi’ara koma baya, inda a ranar Laraba ya fito yana bayar da haƙuri, a cikin wani bidiyo da ya karade soshiyal midiya.

“Ina amfani da wannan dama domin janye kalamaina, na kuma bayar da hakuri ga ‘yan masana’antar Kannywood. Na yi wasu maganganu kuma zan janye bisa dalilai guda uku.

“Na farko maganar da na yi wasu na ganin ciyaman Alhaji Dauda Kahutu Rarara shi ne ya saka ni na yi wannan maganar. Ina ba da hakuri domin barranta shi da ita, domin ni na yi ta. Domin ya kira ni ya kuma nuna min kuskuren da ke cikin maganganuna. Kuma dama cikar dan adam shi ne idan shugabanka ya ce ka yi daidai ka karbi daidai ne. Idan shugabanka ya ce kayi kuskure ka karba.

“Haka kuma akwai abokiyar aikina Aishatul Humaira ta zaunar da ni ta gwada min kurakuran da ke cikin maganar da na yi, musamman a kan mai girma MD, Ali Nuhu. Wanda uba ne a wurinta a masana’antar. Hallau a cikin masana’antar tana da aminai maza da mata wanda suke da alaka ta mutunci da mutunta juna.”

Sai dai Alhikma ya yi togaciya a ban hakurin nasa, in da ya ce iya ‘yan Kannywood zai bai wa hakuri ban da wadanda ya kira da ‘yan shisshigi’.

Ita ma dai Aishatul Humairan ta bai wa ‘yan Kannywood din hakuri duk da ba da yawunta Alhikima ya tayar da hazon ba,  musamman Ali Nuhu, wanda ta ce uba ne a gare ta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Da Ghana Za Su Karfafa Hadin Gwiwarsu
  • Kayayyakin Sin Na Kara Samun Karbuwa A Kasuwar Duniya
  • NUC Da Shugabannin Makarantu Sun Yi Kira A Sanya Tsarin Kere-kere A Jami’o’in Nijeriya
  • Sin Na Fatan Yin Tafiya Bai Daya Tare Da Amurka 
  • Han Zheng Ya Halarci Bikin Bude Dandalin Tattaunawa Kan Zaman Lafiya Na Duniya Karo Na 13
  • An sa zare tsakanin ‘yan Kannywood da Alhikima
  • Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya
  • Rasha Ta Jaddada Aniyarta Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • JMI Ta Bukaci Kungiyar Majalisun Dokoki Ta Duniya Su Kori HKI Daga Cikinta