Ayatullahi Khatami Ya Ce Hukuncin Da Ya Cancanci Trump Da Netanyahu Shi Ne Kisa Saboda Zubar Da Jinin Bil’Adama
Published: 4th, July 2025 GMT
Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehra mya bayyana cewa: Hukuncin shari’a da ya hau kan Trumpm da Netanyahu shi ne kisa
Limamin da ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran a yau ya bayyana cewa: Amurka da karen da suka horar sun yi barazana ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma wannan wauta ce.
Hujjatul-Islam Ahmad Khatami a cikin hudubar sallar juma’ar a birnin Tehran, yayin da yake ishara da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kai harin wuce gona da iri kan kasar Iran ya ce: martani da dakarun Iran suka mayar kan gwamnatin yahudawan sahayoniyya abu ne da ke gwada karfinsu na mayar da martini kan dukj wani mai girman kai da dagawa.
AYatullahi Hatami ya kara da cewa: Son kasa da kare Musulunci so ne ga Allah. Kuma kishin kasa wani bangare ne na Imani, don haka ya karfafa al’umma kan Shirin kare kasarsu da kimar daular Musulunci daga duk wani dan mamaya mai kiyayyaya da kyawawan dabi’un addini.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da bayar da rancen kudi ga hukumar gidaje ta jihar domin gina gidaje 52 a Dutse.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya fitar, ya bayyana cewa gidajen za su kunshi masu dakuna uku da kuma dakuna biyu kowanne.
Ya ce aikin zai kasance a gaban tsohuwar unguwar majalisar dokoki, kusa da hanyar wucewa ta Jami’ar Tarayya da je Dutse, a matsayin wani shiri na asusun gina gidaje karkashin ma’aikatar gidaje, ci gaban birane da tsare-tsaren yankuna, ta hannun hukumar gidaje ta jihar.
Alhaji Sagir ya bayyana cewa, wannan mataki na nuna kudirin gwamnati wajen magance matsalar gidaje a babban birnin jihar, kara habaka ci gaban birane, tare da samar da ayyukan yi ga matasan jihar.
Ya ce an tsara wannan asusu ne domin tabbatar da dorewa, ta yadda za a ci gaba da zuba jari a ayyukan samar da gidaje masu araha a fadin jihar.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana da kudirin ci gaba da inganta rayuwar al’ummarta, ta hanyar ayyuka masu amfani da jama’a, da ke inganta walwala, karfafa tattalin arziki, da tallafa wa matasa.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gyara da inganta gidan baki guda biyu (Malam Adamu Chiroma House da kuma Senator Francis Ella House) da ke cikin G9 Quarters a Dutse, da kudin sama da naira miliyan 219.7.
Ya ce aikin zai haɗa da cikakken gyara da inganta gine-ginen, gyaran hanyoyin ruwa da kuma girka tankokin ruwa ga kowanne daga cikin gidajen biyu.
Ya ce hakan na da nufin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai dorewa a wuraren.
Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, amincewar da aka yi da wannan kwangila na nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kula da dukiyar jama’a da kuma tabbatar da cewa gine-ginen gwamnati suna cikin yanayi mai kyau da nagarta.