HausaTv:
2025-07-03@03:12:24 GMT

Kofar JMI A Bude Take Don Tattaunawa Da Kasashen Turai

Published: 16th, March 2025 GMT

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar JMIa bude yake ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiyaAsabar a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Netherlands Caspar Veldkamp a jiya Asabar.

Ministan ya kara da cewa dangantakar diblomasiyya tsakanin Dutch da Iran tsohuwar dangantaka ce. Sannan Iran tana da nufin fadada shi.

A Nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Netherlands yay aba da yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake bunkasa. Sannan dangane da tsabirin kasar Iran guda uku, Abu Musa, Tumbe kucek da Bozorg wadanda iran take takaddama da UAE dangane da mallakarsu, ya ce abu ne wadanda kasashen biyu suke iya warwarewa a tsakaninsu. Banda haka yace dokokin kasa da kasa ma suna iya warware wannan sabanin da ke tsakaninsu.

 

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare

Firai ministan kasar Iraki Muhammad Shia assudani ya bayyana cewa kasarsa ta shigar da karar HKI a gaban kwamitin tsaro na MDD saboda keta hurumin sararin samaniyar kasar don kaiwa kasar Iran hare-hare.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sudani yana fadar haka, ya kuma kara da cewa HKI ba tare da neman izinin gwamnatin kasar ba a cikin yakin kwanaki 12 da JMI ta shiga sararin samaniyar kasar daga nan kuma ta kai hare-hare kan sansanonin sojojin da kuma cibiyoyin fararen hula daga kasar ta Iraki. Duk ba tare da amincewar kasar ba.

Firai ministan ya yi allawadai da hare-haren ya kuma bukaci a huklunta HKI kan hakan. Y ace kasar Iraki bata da garkuwan sararin samania isassu wadanda zasu kare ta daga shigowar kasar ta Iraki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kayayyakin Sin Sun Kara Baiwa Masu Sayayya Na Kasa Da Kasa Damar Samun Zabi
  • Firaministan Sin Zai Halarci Taron Shugabannin Kasashen BRICS Na 17 A Brazil Da Kuma Ziyarar Aiki A Masar
  • Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya
  • Aragchi: Iran Ba zata Taba Daina Tace Makamashin Uranium A Cikin Gida Ba
  • Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare
  • Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila
  • Iran Ta Ce Babu Batun Tattaunawa Duk Tare Da Amurkawa Sun Ce Za’a Yi
  • Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya
  • Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA
  • Iran Ta Bawo Mayakan Huthi Fasahar Kera Makamai Masu Linzami Daga Cikin Ruwa