Shugaban Kasar Iran Ya Gabatar Da Jawabio A Taron Kolin Kungiyar ECO Musamman Kan Harin Da Kasarsa Ta Fuskanta
Published: 4th, July 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin kasarsa sun koya wa ‘yan sahayoniyya masu wuce gona da iri babban darasi
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a jawabin da ya gabatar a taron kolin kungiyar Hadin Gwiwar Tattalin Arziki ta ECO da aka gudanar a kasar Azarbaijan a yau Juma’a, ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran bisa doka mai lamba 51 na yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya sun kare al’ummar Iran da mutuncin kasar da cikakken ikonta a yakin da aka yi a baya-bayan nan, kuma sun koyar da masu wuce gona da iri darasi mai girma da kuma dakile yaduwar yaki a wannan yanki.
A yayin taron koli karo na 17 na kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO da aka gudanar a yammacin yau Juma’a, Pezeshkian ya yi Allah wadai da harin da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ta kai kan kasar Iran, yana mai cewa: Wannan gwamnatin ta fara ne da keta haddin ka’idoji da dokokin kasa da kasa da suka hada da Mataki na 2 sakin layi na 4 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, sannan yakin ci gaba da taimakon sojojin Amurka masu dauke da dabi’ar zalunci kan Iran.
Shugaban Iran ya kara da cewa: A cikin kwanaki 12 na hare-haren wuce gona da irin, an aiwatar da wasu munanan laifuka zalunci kan sojojin da ba sa kan aikinsu da malaman jami’a da talakawan kasa da cibiyoyin makamashin nukiliya na zaman lafiya da suke karkashin kulawar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, da kuma kayayyakin more rayuwa.”
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin dimbin hasarar rayukan bil’adama da zaluncin yahudawan sahayoniyya ya janyo kan al’ummar Iran, shugaban ya ce: A bisa ka’ida ta 51 na kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, sojojin kasar Iran sun taka rawa wajen kare halaltacciyar kasar Iran, ikon da amincin kasa, da cikakken ‘yancin kasa tare da koyar da maharan darasi mai tsauri, da kuma hana yaduwar wannan yanki a yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare
Firai ministan kasar Iraki Muhammad Shia assudani ya bayyana cewa kasarsa ta shigar da karar HKI a gaban kwamitin tsaro na MDD saboda keta hurumin sararin samaniyar kasar don kaiwa kasar Iran hare-hare.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sudani yana fadar haka, ya kuma kara da cewa HKI ba tare da neman izinin gwamnatin kasar ba a cikin yakin kwanaki 12 da JMI ta shiga sararin samaniyar kasar daga nan kuma ta kai hare-hare kan sansanonin sojojin da kuma cibiyoyin fararen hula daga kasar ta Iraki. Duk ba tare da amincewar kasar ba.
Firai ministan ya yi allawadai da hare-haren ya kuma bukaci a huklunta HKI kan hakan. Y ace kasar Iraki bata da garkuwan sararin samania isassu wadanda zasu kare ta daga shigowar kasar ta Iraki.