Shugaban kasar Iran ya gana da fira ministan kasar Pakistan

Shugaban kasar Masoud Pezehkian ya gana da fira                             ministan Pakistan Shehbaz Sharif a gefen zaman taron kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO da Jamhuriyar Azabaijan ta karbi bakunci.

Fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yaba da irin rawar da shugaban kasar Iran ya taka a lokacin da yahudawan sahayuniyya suka kai wa Iran hari tare da tabbatar da goyon bayan Pakistan ga Iran da kuma hada kai da hadin gwiwa da Iran don samar da zaman lafiya a yankin.

Sanarwar da ofishin fira ministan Pakistan ya fitar ta ce: shugaba Masoud Pezehkian ya gana da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif a gefen zaman taron kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO da Jamhuriyar Azarbaijan ta dauki nauyi.

Shugaban kasar ta Iran ya isa birnin Khankandi na jamhuriyar Azarbaijan ne a yau Juma’a a domin halartar taron koli na kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO karo na 17.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: fira ministan Pakistan Shugaban kasar

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Ya Rattaba Hannu Kan Daftarin Dakatar Da

Hadin Gwiwa Da Hukumar IAEA

Shugaban kasar Iran ya rattaba hannu kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, bisa wata doka da Majalisar Shawarar Musulunci ta kafa kwanan nan

Sanannen abu ne cewa: Wannan doka ta zo ne bayan hare-haren da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, a daidai lokacin da Iran ke shirin tunkarar tattaunawar nukiliya karo na shida da Amurka!

Har ila yau, an san cewa shawarar ba ta zama ficewa daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi ba, a’a, ta dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ce ta IAEA har sai an cika wasu sharudda, musamman tabbatar da tsaron cibiyoyin makamashin nukiliya da masana kimiyya na Iran.

Harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, cin amanar diflomasiyya ce, da yarjejeniyoyin kasa da kasa, da dokoki. kuma wata mummunar yaudara ce da Trump ya cimma da hadi baki da Netanyahu don tauye hakkin Iran don kai harin. Da wannan ne Trump, wanda Netanyahu da jiga-jigan ‘yan sahayonyiya suka tunzura shi a Amurka, ya dauki matakin yin mummunar illa ga kima da martabar Amurka a duk duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kwamitin AU: Kasar Sin Aminiya Ce Da Za A Iya Dogaro Da Ita
  • Shugaban Kasar Iran Ya Gabatar Da Jawabio A Taron Kolin Kungiyar ECO Musamman Kan Harin Da Kasarsa Ta Fuskanta
  • Shugaban Kasar Iran Ya Rattaba Hannu Kan Daftarin Dakatar Da
  • Amurka Ta Kakabawa JMI Sabbin Takunkuman Tattalin A Jiya Alhamis
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Harin Kan Cibiyar Makamashin Nukiliya Cin Amanar Diflomasiyya Ce
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Irin Aniyar Da Gwamantinsa Ta Kudurta Wajen Kare Tsaron Kasa Da Al’ummarta
  • Rasha Ta Jaddada Aniyarta Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
  • Aragchi: Iran Ba zata Taba Daina Tace Makamashin Uranium A Cikin Gida Ba
  • Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare