Wasu sarakunan gargajiya na ta’ammali da ƙwayoyi — Obasanjo
Published: 16th, March 2025 GMT
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan.
A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya.
“A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo.
“Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.”
Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar gargajiya domin tana taka rawar gani a ci gaban ƙasa.
Har ila yau, ya gargaɗi shugabanni cewa idan ba su magance matsalolin da jama’a ke fuskanta ba, hakan na iya haifar da rikici a nan gaba.
“Idan gwamnati ba ta saurari kokensu ba—musamman matasa da suka fusata—to nan gaba abubuwa ba za su yi kyau ba,” in ji shi.
“Waɗanda suka hana a samu sauyi cikin lumana, za su gamu da sauyi ta hanyar tashin hankali.”
Obasanjo ya ƙara da cewa idan shugabannin Afirka suka yi watsi da wannan gargaɗi, hakan na iya haddasa rikici a nahiyar gaba ɗaya.
“Yin watsi da wannan gargaɗi kamar yin rawa ne lokacin da gidanka ke ci da wuta,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gargadi Miyagun ƙwayoyi Najeriya Sarakunan Gargajiya
এছাড়াও পড়ুন:
Boko Haram Sun Hallaka ‘Yan Zaman Makoki 7, Sun Jikkata Wasu A Borno
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne.
Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin.
A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp