Leadership News Hausa:
2025-11-02@21:15:11 GMT

Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu

Published: 16th, March 2025 GMT

Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu

“…The composition and functioning of the legislatibe council, howeber, pointed to the fact that, it was nothing more than a mere rubber-stamping institution…”.
(Fagge & Alabi, 2007: 5b).

Wadancan kalamai na sama cikin harshen Turanci, na yin nuni ne da cewa, “yan majalisun Nijeriya a wancan lokaci da Turawan Birtaniya ke mulkarmu, ba su kasance komai ba, face “yan-abi-yarima ne cikin harkokin zaman majalisar.

Duk abinda aka yanke a majalisar, kawai sai dai su sanya-hannu ne akai. Ba su da ikon tabbatar da wani kudiri, koko yin watsi da shi. Tun da, hatta mafi yawan adadin mutanen da ke cikin zauren na majalisar, za a samu cewa, gwamna ne ya zabe su da hannunsa, kamar yadda a rubutun baya aka faiyace irin adadinsu dalla-dalla.

Batun rashin iko, ko karancinsa, shi ne babban abinda ya mamaye harkokin “yan majalisun na kasa gabanin Nijeriya ta kai ga samun “yancin-kai. Sai dai, a kan samu wasu “yan canje-canje ne daga lokaci zuwa lokaci, sakamakon mabanbantan kundin tsarin mulkin da Turawan suka gabatar mana da su gabanin kai wa ga samun yancin-kai. Tulin labaran “yan majalisun na da auki ainun, kawai za mu yi kokarin matsawa gaba ne cikin hanzari, don kai wa ga yadda lamuran majalisar ke wakana a yau, wanda shi ne babban abinda muke son yin doguwar tattaunawa akai sannu a hankali.

“Yan Majalisunmu A Shekarar 1900
Ya tabbata, bayan samun “yancin-kai a wannan Kasa (cikin Shekarar 19b0), “yan majalisun namu, sun kai ga fara samun “yancin gudanar da aiyukansu, sama da irin yadda suka kasance a baya. Tsarin mulki irin na shugaban kasa daban, da shugaban gwamnati (tsarin mulkin firaminista) daban, aka fara dabbakawa a wannan kasa bayan samun mulkin kai. A karkashin tsarin mulkin, za a ga irin aikace-aikacen da wadannan ‘yan majalisun namu na lokacin suka gudanar, kafin juyin mulkin Soja na farko da aka fara yi a kasar, cikin Shekarar 19bb, Shekaru shida (b) kacal, bayan samun yancin-kai. Ke nan, irin ayyukan da suka gudanar cikin majalisar, zai zamto ne a tsakanin Shekarar 1900 da Shekarar 1900.

Ga wasu daga irin ayyukan da bangaren “yan majalisun suka gudanar kamar haka;

i- Kafa Gwamnati: “yan majalisun ne suka taka rawa wajen zabar firaminista Abubakar Tafawa Balewa a matsayin shugaban gwamnati, tare da yunkurin fasalta tsarin gwamnatin dimukradiyya.

ii- Ci gaban bangaren dokoki: “yan majalisun, sun samar da dokoki kyawawa, musamman wadanda suka shafi ci gaban tattalin arzikin kasa, ilimi tare da samun cikakken ikon gudanarwa a cikin lardunan kasar da ake da su.
iii- Kyautata Wakilci A Gwamnatin Hadaka Da Na Larduna: tsarin, ya ba da dama ga jagororin gwamnati (firimiyoyi) na lardunan arewa da yamma da na gabashin kasar, na su shigo cikin lamuran gudanar gwamnati dumu-dumu, don a dama da Canji

iv- Canjin Mirginawar Tsarin Mulki Na Kasa: “yan majalisun, sun taka rawa muhimmiya, wajen dawowar tsarin mulkin dake nuna lamuran Kasar, na gudana karkashin ikon Sarauniyar Birtaniya ne, zuwa ga wata jamhuriya mai zaman kanta cikin Shekarar 19b3, wadda ikonta ya sabbawa Dr Nnamdi Azikiwe zama shugaban kasar Nijeriya na farko.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yan majalisun na tsarin mulkin

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare