An fara tuhumar tsohon ɗan ƙwallon Arsenal, Thomas Partey da laifuka biyar da suka haɗa da fyaɗe da kuma cin zarafi, an bayar da rahoton cewa ya aikata laifukan ne a tsakanin shekarar 2021-2022, cewar ‘yansandan Birtaniyya.

Daga cikin laifukan akwai fyaɗe akan wasu mata uku waɗanda ake tuhumarsa da cin zarafinsu ta hanyar tursasawa kan mace ta farko da ta biyu sai kuma laifin lalata da mace ta uku.

‘Yansanda a ƙasar Birtaniya sun ce ya kamata Thomas ya bayyana a Kotun Majistare ta Westminster a ranar 5 ga watan Agusta, tuhumar ta biyo bayan binciken da jami’an tsaro suka gudanar, wanda ya fara a watan Fabrairun 2022 bayan da ‘yansanda sun samu rahoton fyaɗen.

Partey dai ya bar Arsenal bayan kwantiraginsa ya ƙare, kuma an ce ƙungiyoyin da suka haɗa da Juventus da Barcelona da kuma Fenerbahce suna zawarcinsa, ɗan wasan na Ghana ya kasance a Emirates na tsawon shekaru biyar bayan an siyo shi daga Atletico Madrid, kuma ya buga wa ƙasarsa wasanni da dama.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Arsenal Zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Atiku, Obi, El-Rufai, Amaechi Da Wasu Sun Halarci Taron ADC Na jam’iyyar Haɗaka

Wasu manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa sun hallara a Cibiyar Yar’Adua da ke Abuja a yau Laraba da rana don taron ƙaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a wani mataki na shiryawa zaɓen shekarar 2027. Taron ya samu halartar manyan fitattun ’yan takara da tsofaffin gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasa.

Cikin waɗanda suka halarta akwai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na LP; tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; da tsohon Ministan Sufuri kuma gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi. Haka kuma, Solomon Dalung, Dino Melaye, Dele Momodu, Sanata Gabriel Suswam, da Sanata Ireti Kingibe sun samu halarta. Emeka Ihedioha da Air Marshal Sadique Abubakar (rtd.) suma sun bayyana.

David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC Ana Sa Ran Samun Bunkasuwar Dangantakar Sin Da Kungiyar SADC

A yayin taron, an sanar da cewa haɗakar jam’iyyun adawa ta ɗauki jam’iyyar ADC a hukumance a matsayin dandalin siyasa da za ta yi amfani da shi don ƙalubalantar jam’iyyar APC a 2027. An bayyana tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, a matsayin shugaban riko na ƙasa. Ya fice daga jam’iyyar PDP domin jagorantar sabon tsarin siyasar.

An kuma nada tsohon gwamnan Osun kuma jigon APC, Rauf Aregbesola, a matsayin sakataren riko na ƙasa, alamar yiwuwar sauyin tunani da haɗewar ƙarfi daga jam’iyyu daban-daban. Ana sa ran David Mark da sauran shugabanni za su fara ƙaddamar da sabuwar tafiyar siyasar, yayin da taron ke ci gaba a lokacin haɗa wannan rahoto.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bude Mafiya Yawan Tashoshin Jiragen Sama A Iran Bayan Tsaida Yaki
  • Makusantan Gwamnatin Buhari da suka shiga haɗakar ADC
  • Bayan Taron Haɗaka, Hankali Wike Ya Tashi — ADC
  • Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota
  • Buhari Ba Shi Da Lafiya, Amma Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
  • Buhari Ba Shi Da Lafiya, Yana Samun Sauƙi A Birtaniya — Garba Shehu
  • Atiku, Obi, El-Rufai, Amaechi Da Wasu Sun Halarci Taron ADC Na jam’iyyar Haɗaka
  • Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba
  • Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Kwana 60 Da Hamas – Trump