Ma’aikatan MDD Masu Kula Da Ayyukan Makamashin Nukliya Na Kasar Iran Su Fice daga Kasar
Published: 5th, July 2025 GMT
Hukumar IAEA mai kula da ayyukan makamashin nukliya a kasar Iran ta bada sanarwan cewa ma’aikatan hukumar sun fice daga kasar a jiya Jumma’a bayan da gwamnatin kasar ta jingine aiki da ita, bayan hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa cibiyoyin nuklliya na kasar da ke Fordo, Natanz da kuma Esfahan a yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar.
Hukumar ta bada sanarwan cewa ma’aikatan hukumar a Iran suna cikin kasar a lokacin yakin kwanaki 12 kan Iran, kuma a jiya sun bar Tehran zuwa Vienna bayan da gwamnatin kasar ta jingine aiki da ita, kuma tuni sun isa birnin Vienna inda cibiyar hukumar take.
A ranar Alhamis da ta gabata ne ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragch ya bayyana cewa daga yanzun kuma hukumar zata yi mu’a mala da majalisar tsaron kasa, kan duk wani abu da ya shafi shirin makamashin nukliya na kasar.
Banda haka yace kasar Iran har yanzun bata fice daga yarjeniyar NPT ta hana yaduawar makamashin nukliya ba. Amma hukumar ta bayyana cewa Tehran bata shaida mata a hukumance kan cewa ta jingine aiki da ita ba.
Bayan yakin kwanaki 12, wato a ranar 25 ga watan yunin da ya gabata ne majalisar dokokin kasar Iran ta amince da jingine aiki da hukumar ta IAEA tare da zargin shugabanta Rafael Grossi da zama wanda ya ingiza yakin kwanaki 12 a kan kasar. Sannan yana mika bayanan da ya tattara a iran dangane da shirinta na makamashin nukliya ta zaman lafiya ga HKI.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukliya yakin kwanaki 12
এছাড়াও পড়ুন:
Aragchi Ya Musanta Zargin Da Jamus Take Watsawa Dangane sa Shirin Nukliyar Kasar
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi watsi da labarin da ministan harkokin wajen kasar Jamus ya watsa dangane da shirin Nukliyar kasarsa ya kuma kara da cewa labarin jabu ne.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X . Ya kuma yi watsi da zancen ministan harkokin wajen kasar Jamus wanda yake cewa, jinginar da aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya wato IAEA wanda JMI ta yi, ya na nuna cewa ba wanda zai bincika ayyukanta na makamashin nukliya ba, kuma ta rufe kofar tattaunawa Kenan.
Aragchi ya bayyana cewa wannan ba haka bane, saboda shirin nukliyar kasar Iran a halin yanzu ya na karkashin majalisar koli ta tsaron kasar Iran ne, don haka ita ce zata fayyece yadda huldar shirin zai kasance tare da hukumar IAEA. Sannan Iran bata fice daga yarjeniyar NPT ba.
Kasar Jamus dai tana goyon bayan hare=hare da HKI da AMurka suka kaiwa JMI a yakin kwanaki 12, dagan cikin harda hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar. Ya ce aiki ne da bai dace ba wacce JKI ta yi madadin kasashen yamma.