Hasashen Samun Ruwan Sama A 2025: Shawarwarin Da Kwararru Suka Bai Wa Manoma
Published: 16th, March 2025 GMT
Saboda haka ne, hukumar ta shawarci manoman da ke da ra’ayin noma a kakar noman ta bana da su tabbatar sun tuntube ta, ko kuma tuntubar sauran hukumomin da ke hasashen yanayi, domin sanin lokacin da ya ya fi dacewa su yi shuka.
Hukumar ta yi hasashen cewa, jihohin Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Filato, Bauchi, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Neja, Kwara, Kogi, Abuja, Ekiti da kuma Ondo, za su fuskanci daukewar ruwan sama da wuri, inda aka kwatanta da na dogon zango da aka samu a daminar bara.
Haka zalika, hukumar ta yi hasashen cewa; za a samu jinkirin ruwan sama a wasu sasssan jihohin Kaduna, Nasarawa, Benuwe, Legas, Kwara, Taraba, Oyo, Ogun, Kuros Riba, Delta, Akwa Ibom, Ebonyi, Anambra da kuma Enugu.
A cewar Hukumar, mai yiwuwa kakar daminar ta bana ta kasance gajera a wasu sassan Jihohin Borno da Yobe, sabanin yadda aka saba gani.
Hukumar ta yi hasashen cewa, mai yiwuwa kakar daminar ta bana, ta yi tsawo a Jihohin Legas da Nasarawa, sabanin yadda aka saba samu.
Hukumar ta yi hasashen cewa, daga watan Mayu zuwa na Yuni, za a samu ruwan sama kamar da baakin kwarya, wanda kuma mai yiwuwa, a samu afkuwar ambaliyar ruwa a wasu biranen da ke kusa da rafuka a kasar.
Kazalika, daga watan Afirilu zuwa na Mayu, yankunan Saki, Iseyin, Ogbomoso, Atisbo, Orelope, Itesiwaju, Olorunsgo, Kajola, Iwajowa da kuma Oro Ire da ke cikin Jihar Oyo, an yi hasashen samun karancin ruwan sama, wanda zai iya kai wa har tsawon kwana 15, bayan saukar ruwan saman.
Bugu da kari, Hukumar ta yi hasashen cewa; a wasu jihohin da ke Arewacin kasar nan, daga watan Yuni zuwa Yuli har zuwa watan Agustan 2025, za a samu karancin ruwan sama, wanda zai kai har tsawon kwana 21, inda kuma a Jihohin Ekiti, Osun, Ondo, Ogun, Edo, Ebonyi, Anambra, Imo, Abia, Kuros Riba, Delta, Bayelsa da kuma Akwa Ibom, za a samu ruwan sama na tsaka-tsaki da zai kai kwana 15.
Daga tsakanin kwana 27 zuwa 40, za su shige ba tare da wani batun hasashe samun sauyin yanayi ba, haka za a fuskanci rani kadan a yankin Kudu Maso Gabas daga ranar 22 na 2025.
Saboda haka ne, kwararru a fannin aikin noma suka shawarci manoman kasar nan, musamman wadanda ke jihohin da ke tsakiyar kasar, da su tabbar da sun yi shuka da Irin da ke jurewa kowanne irin yanayi, musamman domin kauce wa fuskantar matsalar rashin samun saukar ruwan sama a kan lokaci a kakar noman ta 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Hukumar ta yi hasashen cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp