Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya”, inda suka samu ra’ayin bai daya na gudanar da hadin gwiwa.

A tattaunawar da ya yi da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, Hassan Diab ya bayyana cewa, fahimtar kasar Sin yana da matukar muhimmanci, domin kasar na bude kofarta ga duniya.

A cikin ‘yan shekarun nan, an samu rashin fahimta, shakku har ma da suka game da ci gaban da kasar Sin ta samu cikin lumana, da tasirinta a duniya. Dangane da haka, Diab ya ce, duk wadannan ba za su hana kasar Sin samun ci gaba a fagen duniya ba. Ya ce, wadanda ba sa son ganin yadda kasar Sin ke kara cimma nasara, suna bukatar karfafa hulda da jama’ar kasar don kara fahimtar kasar. Kuma ya zama dole su amince da gaskiyar cewa kasar Sin ta bunkasa har ta zamanto babbar kasa a duniya a matakai da yawa, kuma kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a yayin tabbatar da bunkasuwar kasashe daban daban a duniya. Ya kara da cewa, kamata ya yi su yarda tare da fahimtar hakan cikin natsuwa tare da gina wata gadar tuntubar juna da Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

“Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai

Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa na shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma sauran al’ummun duniya.

Kowa ya san yankin Taiwan wani bangare ne da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, kuma wannan shi ne matsaya daya da al’ummun Sinawa da yawansu ya kai biliyan 1.4 ciki har da jama’ar yankin Taiwan da yawansu ya kai miliyan 23 suka dauka, wanda kuma ra’ayi ne daya tilo da kasashen duniya suka cimma matsaya a kai.

Sanawar Alkahira da sanarwar Potsdam da dai sauran takardun shari’a sun aza ingantaccen tubali ga dokar kasa da kasa dake bayyana cewa, Taiwan yankin jamhuriyyar jama’ar kasar Sin ne da ba za a iya ware shi ba. Ban da wannan kuma, MDD ta zartas da kuduri mai lamba 2758 a shekarar 1971, inda matakin ya sake nanata kasancewar Taiwan a matsayin wani yanki na kasar Sin. Kuma, karkashin jagorancin wannan kuduri, yawancin kasashe sun katse hulda da mahukuntan yankin Taiwan, inda suka amince da halastaccen matsayin gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin kawai a duniya. Hakan ya sa, ra’ayin kasancewar kasar Sin daya tak a duniya ya samu amincewa daga al’ummun duniya, kuma ya zama ka’idar tushe ta huldar kasa da kasa.

Yunkurin da wasu mutane kamar su Lai ke yi kamar tururuwa ce a gaban giwa, watau karamar alhaki ce da ba ta isa komai ba. (MINA)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Nauru: Ci Gaban Sin Darasi Ne Ga Nauru Da Duniya Baki Daya
  • Kyautar ‘Jakadan Abota’ Na Kasar China Ya Shiga hannun Iran
  • Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
  • “Sin Daya Tak A Duniya”, Matsaya Ce Da Al’ummun Duniya Suka Kafe Kai Da Fata a Kai
  • Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa
  • Rikicin Masarautar Kano Ya Kara Zafafa
  • HKI Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kudancin Kasar Lebanon
  • Akwai Bukatar Hada Kai Da Aiki Tare Tsakanin Hukumomin Tsaro
  • An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing
  • Shiri Na Shekaru Biyar Biyar: Sirrin Tabbatar Da Ci Gaban Kasar Sin