Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka
Published: 16th, March 2025 GMT
A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar.
Hakan na ƙunshe cikin wata ’yar taƙaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar.
Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasuSakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi Ebrahim Rasool da kasancewa “ɗan siyasar wariyar launin fata mai ƙyamar Amurka,” lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin diflomasiyya da ya kunno kai tsakanin Washington da Pretoria.
A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Shugaba Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa Amurka ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Afirka ta Kudu, sakamakon zarginta da ƙwace gonakin fararen fata na ƙasar.
Wannan dalili ne ya sa shugaba Trump ya sanar da cewa duk wani manomi da aka kwace wa gona, kuma yake fatan koma wa Amurka to zai samu izinin zama ɗan ƙasar cikin sauƙi.
Afirka ta Kudu ta yi martaniMatakin da Amurka ta ɗauka na korar jakadan Afirka ta Kudu “abin takaici ne,” kamar yadda ofishin shugaban ƙasar ya bayyana a ranar Asabar, yana mai kira ga “gyara diflomasiyya” tsakanin ƙasashen biyu.
“Fadar shugaban kasa ta kura da abin takaici na korar jakadan Afirka ta Kudu a Amurka, Mista Ebrahim Rasool,” in ji sanarwar da Fadar Shugaban Afirka ta Kudu ta fitar.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Muna shirin kai farmaki a Nijeriya — Ma’aikatar Yaƙin Amurka
A yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ke zargin gwamnatin Nijeriya da watsi da batun kisan Kiristoci a ƙasar, Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta bayyana cewa ta fara shirin kai farmaki a Nijeriya.
Sakataren Ma’aikatar, Pete Hegseth, ne ya tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, yana mai cewa ma’aikatarsa “na shirye-shiryen ɗaukar mataki” bayan umarnin da Trump ya bayar.
Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya“Muna shirye-shirye don ɗaukar mataki a Nijeriya. Idan gwamnatin Nijeriya ba ta kare Kiristoci ba, za mu kai hari, mu kawar da ‘yan ta’addan Musulmai da ke aikata wannan ta’asar,” in ji Hegseth.
Trump dai ya yi wannan barazanar ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, inda ya ce Amurka za ta dakatar da duk tallafin da take bai wa Nijeriya, kuma tana iya “shiga ƙasar da ƙarfin soji domin share ‘yan ta’addan da ke kashe Kiristoci.”
“Idan gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk wata tallafi, kuma mai yiwuwa ta shiga wannan ƙasar, ta cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’addan Musulmai masu zafin kishin addini,” in ji Trump.
Ya kuma gargaɗi gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta ɗaukar mataki, yana cewa idan Amurka ta kai farmaki “za ta yi shi cikin sauri, da tsananin ƙarfi, da gamsuwa.”
Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan Trump ya mayar da Nijeriya cikin jerin ƙasashen da za a sanyawa ido, yana zargin cewa “ana yi wa Kiristoci kisan gilla” a hannun ƙungiyoyin Musulmi masu tsattsauran ra’ayi.
Sai dai a martanin da ya mayar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Nijeriya tana nan daram a matsayin ƙasa mai dimokuraɗiyya wadda kundin tsarin mulkinta ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan addinai.
“Tun daga shekarar 2023, gwamnatinmu tana gudanar da tattaunawa sosai da shugabannin addinai na Kiristanci da Musulunci, tare da ci gaba da magance matsalolin tsaro da ke shafar ‘yan ƙasa daga addinai da yankuna daban-daban,” in ji Tinubu.
A cewar mai ba wa Tinubun shawara na musamman kan yaɗa manufofi, Daniel Bwala, za a yi ganawa tsakanin Shugaba Tinubu da Shugaba Trump “a cikin kwanaki kaɗan masu zuwa” domin tattaunawa da warware wannan saɓanin fahimta.