Aminiya:
2025-07-05@14:17:27 GMT

Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano

Published: 5th, July 2025 GMT

Al’ummar yankin Bachirawa a Jihar Kano sun yi ta maza sun cafke wasu matasa biyu da ake zargi da ƙwace waya a unguwar a yayin da ɓata-garin suke tsaka da ƙwacen.

Matasan dai sun tare wata mata ce a unguwar suka ƙwace mata waya, wanda hakan ya sa mutanen yankin suka yi kansu tare da kama su.

An samu nasarar karɓe wayar da suka amsa tare da ƙwace makaman da aka samu a hannunsu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da haka bayan al’ummar sun miƙa waɗannan matasa ofishin ’yan sanda a ranar Juma’a.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bachirawa

এছাড়াও পড়ুন:

Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya jajanta wa mutanen da ambaliya da guguwa suka shafa a ƙananan hukumomin Damboa da Askira-Uba.

A cikin kwanakin da suka gabata, ruwan sama mai yawa ya haifar da ambaliya a ƙauyukan Wovi da Gumsuri na Damboa.

Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu

Wannan ambaliya ta yi sanadin mutuwar mata biyu, kuma ta lalata gidaje da raba mutane da muhallansu.

A wani ɓangare kuma, guguwa mai ƙarfi ta afka wa garin Rumirgo da ke Askira-Uba, inda ta lalata gidaje da dukiyoyin jama’a.

Dauda Iliya, mai bayar da shawara na musamman ga Gwamna Zulum kan harkokin yaɗa labarai, ya fitar da sanarwa, inda ya ce abin da ya faru abin tausayi ne da baƙin ciki.

Gwamna Zulum ya ce: “Na yi baƙi ciki da ambaliyar da ta faru a Wovi wadda ta yi sanadin mutuwar mata biyu, da kuma lalata gidaje a Gumsuri.

“Haka kuma abin ya yi muni a Rumirgo inda guguwa ta lalata gidaje. Muna addu’a Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma mayar wa waɗanda suka rasa dukiyarsu da mafificin alheri.”

Gwamnan ya umarci Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA), da ta tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.

Ya kuma tabbatar wa mutanen yankin cewa gwamnati za ta taimaka musu.

Zulum ya ce: “Na riga na umarci hukumar SEMA da ta kai kayan agaji zuwa Gumsuri da Wovi cikin gaggawa. Haka kuma, an riga an tura kayan agaji zuwa Rumirgo.”

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa tana ƙoƙari wajen daƙile irin wannan iftila’i a gaba, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa kula da bin dokoki don kaucewa irin wannan yanayi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kama Matashin Da Ya Yi Garkuwa Da Abokinsa Tare Da Karbar Kudin Fansa
  • Abba Ya Yi Sabbin Naɗe-naɗe A Jihar Kano
  • ’Yansanda Sun Kama ’Yan Bindiga 17 Tare Da Kashe 3 A Abuja
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga Tare Da Kwato Makamai A Jihar Filato
  • ’Yansanda Sun Ceto Ɗan Ghana, Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3
  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
  • Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Irin Aniyar Da Gwamantinsa Ta Kudurta Wajen Kare Tsaron Kasa Da Al’ummarta
  • Rukunin Ƴan APC A Kano Sun Nemi A Rushe Jagorancin Jam’iyyar A Jihar
  • Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba