Cikar FRCN Shekaru 63: An Bukaci Gwamnonin Jihohin Arewa Su Tabbatar Da Dorewar Gidan Rediyon
Published: 16th, March 2025 GMT
An yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya da su tabbatar da dorewar tashar Rediyon Nigeria (FRCN) Kaduna a matsayin abim tunawa da marigayi Firimiyan tsohuwar jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, ya bari.
Masu sauraron tashar sun yi wannan kira a cikin bayanai daban-daban yayin da suke tsokaci kan bikin cika shekaru 63 da kafuwar gidan rediyon a watan Maris na shekarar 1962.
Sun bayyana godiyarsu ga rawar da FRCN Kaduna ya taka tsawon shekaru duk da kalubalen aiki, wanda suka bukaci mahukunta su magance.
A sakon taya murna daban da suka aiko, Sanata Salisu Musa Matori, da Alhaji Umar Dembo, da Alhaji Umar Iya Gulak, da Alhaji Garba Baba da Alhaji Muhammad Damak Abubakar, sun jinjinawa gidan rediyon bisa bajintar da ya nuna, inda suka jaddada bukatar Gwamnatin Tarayya ta cika alkawuran da ta dauka na farfado da tashar.
Jami’in hulɗa da jama’a na Kungiyar Manoma ta Najeriya, Alhaji Muhammad Magaji, ya nuna matukar jin dadinsa kan yadda tashar ke tallafawa harkokin noma, zaman lafiya, hadin kai, da cigaban kasa. Yana mai kira da a cigaba da wannan yunkuri don cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Daga Suleiman Kaura.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Shekaru 63
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Okpebholo a Matsayin Zaɓaɓɓen Gwamnan Edo
“Mun yi watsi da ƙarar saboda babu ingantacciyar hujja a cikinta. Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yanke,” in ji Mai Shari’a Garba.
Wannan hukunci ya tabbatar da cewa Sanata Okpebholo na jam’iyyar APC ne, halastaccen wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Edo na shekarar 2024.
PDP ta zargi cewa an yi maguɗi a zaɓen, inda ta nemi a soke sakamakon.
Amma kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da kotun ɗaukaka ƙara suka yi watsi da ƙorafinta, wanda ya sa suka kai ƙarar zuwa Kotun Ƙoli.
Da wannan hukunci, an rufe duk wata shari’a da ta shafi zaɓen gwamnan Jihar Edo.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp