Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da cewa: Ta gabatar da martani mai kyau ga shawarar dakatar da bude wuta tsakaninta da gwamnatin mamayar Isra’ila

Kungiyar Hamas ta sanar da kammala tuntubarta tare da gabatar da kyakkyawar amsa ga sabuwar shawarar neman dakatar da bude wuta, inda ta bayyana shirinta na nan take na yin shawarwari kan tsarin aiwatarwa.

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Falastinu ta Hamas ta sanar a yammacin jiya Juma’a cewa ta kammala shawarwarin cikin gida da kuma tuntubar wasu bangarori da dakarun Falasdinawa dangane da sabuwar shawara da masu shiga tsakani suka gabatar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Falasdinu a zirin Gaza.

Kungiyar ta yi nuni da cewa ta mika martanin ta ga ‘yan uwanta da ke shiga tsakani, inda ta tabbatar da cewa martanin yana da kyau. Ta sake nanata cewa a shirye take ta gaggauta shiga wani zagaye na tattaunawa kan hanyoyin aiwatar da wannan tsarin.

A cikin wannan mahallin, kafofin watsa labaru na haramtacciyar kasar Isra’ila sun ba da rahoton cewa, an sami wasu muhimman sauye-sauye a daftarin na Witkoff, wanda dukkansu ke goyon bayan Hamas.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m

Wani gidan shan kofi a birnin Dubai ya fara sayar da kofi guda na haɗaɗɗen kofi a kan kusan Dala 1,000, wato kimanin Naira miliyan 1.5, wanda da haka ya zama mafi tsada a duniya.

Gidan shan kofin mai suna Julith Café — da ke cikin unguwar masana’antu da ya zama sabuwar cibiyar masu son kofi, shi ne ya ƙaddamar da wannan sabon nau’in abin sha mai daraja.

Ana sa ran gidan shan kofi ɗin zai fara ba da wannan abin sha ga mutane kimanin 400 kacal, ciki har da wani ɗan adadi da aka tanadar wa dangin gidan sarautar Dubai.

Wani daga cikin masu mallakar gidan, Serkan Sagsoz, ya ce sun zaɓi Dubai ne saboda “birni ne da  ya dace da irin jarin da ke nuna ƙawa da kuma salo.

“Mun ga Dubai a matsayin wuri mafi dacewa don wannan kasuwanci. Wannan birni ne da ke son abubuwan da suka bambanta,” in ji Sagsoz.

’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi

Kofin kofi ɗin, wanda ake sayarwa a kan Dirhami 3,600 (kimanin 980), an yi shi ne daga ’ya’yan kofi na musamman da ake kira Nido 7 Geisha ,daga ƙasar Panama — waɗanda aka saya a gasa ta duniya bayan tashin rububin mai tsanani tsakanin masu saye.

Kamfanin Julith Café ya ce ya biya kimanin Dirhami miliyan 2.2 (dala 600,000) don sayen kilo 20 na waɗannan ’ya’yan kofi, abin da ya kafa sabon tarihin farashi mafi tsada da aka taɓa sayen kofi a duniya.

Sagsoz ya bayyana cewa kofi ɗin yana da ƙamshi da ɗanɗano na musamman. “Yana da ƙamshin furanni farare irin na jasmine, ɗanɗanon lemo da bergamot, har da ɗanɗano irin na apricot da peach. Kamar zuma yake — laushi kuma mai daɗi sosai.”

A bara, wani gidan kofi mai suna Roasters ya kafa tarihin Guinness na kofin kofi mafi tsada a duniya a Dubai, inda ya sayar da shi a kan Dirhami 2,500, amma yanzu Julith Café ta karya wannan tarihin.

Wasu mazauna Dubai sun ce duk da abin mamaki ne, amma abin ba baƙo ba ne a garin da aka sani da abubuwan alfarma.

“Abin mamaki ne amma ai wannan Dubai ce,” in ji wata mazauniya mai suna Ines.

“Ai akwai masu kuɗi, wannan wani sabon abin alfahari ne kawai,” in ji wata mai suna Maeva.

Ana sa ran gidan shan kofi ɗin zai fara ba da wannan abin sha ga mutane kimanin 400 kacal, ciki har da wani ɗan adadi da aka tanadar wa dangin gidan sarautar Dubai.

Shin idan kuna da kudin za ku saya?

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Rikicin PDP Ya Ƙara Ta’azzara Yayin Da Ɓangarori Ke Dakatar Da Juna
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
  • Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta
  • M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa
  • Ƙungiyar Rays Heaven ta Ƙarfafa Wayar da Kai kan Lafiyar Kwakwalwa a Kaduna