Al’ummar Iran Ba Zasu Amince Da Ci Gaba Da Zaman Tattaunawa Da Amurka Ba Saboda Fushin Da Suke Ciki Na Kai Musu Hari
Published: 5th, July 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Babu wanda ko da a kuskure ya yi magana a kan tattaunawa da Amurka saboda tsananin fushin da al’ummar Iran ta yi
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya ce dangane da tattaunawar da aka yi da Amurka, “A halin yanzu al’ummar Iran suna cikin fushi matuka, ta yadda babu wanda ya isa ya yi magana kan batun gudanar da zaman tattaunawa da Amurka ko harkar diflomasiyya.
A cikin wata hira da gidan talabijin na Sky News, yayin da yake mayar da martani kan wata tambaya kan shirin nukiliyar Iran biyo bayan harin wuce gona da iri da Amurkawa da ‘yan sahayoniyya suka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, Baqa’i ya ce: “Sun yi imani da farko dole ne su fahimci abin da ya faru, kwarai abin da ya faru shi ne wani danyen aikin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi aikata kan kasar Iran, sannan kuma Amurka, kan ‘yancin kan kasar Iran da kuma ikon kasar.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mujallar “Foreign Policy”Ta Amurka: Isra’ila Ba Ta Yi Nasara A Yaki Da Iran Ba
Jaridun kasar Amurka sun bayyana cewa; Isra’ila ta kasa cimma manufofin da ta ayyana a yaki da Iran, sannan kuma ta kara zama saniyar ware a duniya.
Mujallar “Foreign Policy” ta yi ishara da sakamakon yakin da take cewa, ya zamarwa Amurka da kawarta Isra’ila juyewar reshe da mujiya,domin harin da su ka kai wa Shirin Iran na Nukiliya bai iya kawo karshensa baki daya,maimakon haka ma sai ya jazawa Tel Aviv asarar mai yawa da kuma karfafa kishin kasa a tsakanin Iraniyawa.”
Har ila yau, rahoton mujallar ta “”Foreign Policy” ya ci gaba da cewa; Asarar da aka yi a Isra’ila, tana firgitarwa”,amma a cikin Iran babu cikakken bayani akan girman barnar da aka yi- da hakan yake a matsayin tsaka mai yuwa ta fuskar muhimman manufofin da Isra’ilan ta so cimmawa da kuma kawarta Amurka.”
Bugu da kari mujallar ta “Foreign Policy” ta ce; Babu wanda yake gaskata abinda Isra’ila take fada na cewa ta rusa Shirin makamashin Nukiliyar Iran,domin hukumomin leken asiri na turai suna cewa, dukkanin sanadarorin kera makaman Nukiliya suna nan kalau ba abinda ya same su.”
Wani sashe na rahoton ya ce; HKI ba ta iya samar da kandagarko na Nukiliya a yakinta da Iran ba,maimakon hakan ma, abu ne mai yiyuwa harin da Isra’ilan da Amurka su ka kai wa Iran ya ba ta karfin gwiwar yin tunanin samar da makamin Nukiliya” a fadar wannan mujalla.
Iran dai ta sha bayyana cewa; Shirinta na sulhu ne, ba kuma wanda yake da hakkin hana ta cin moriyar alfanu mai yawa dake cikin fasahar makamashin Nukiliya.
Rahoton ya kuma ce; gwamnatin Amurka ta fake da dalilai na karya wajen kai wa Iran hari.