Abin Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (8)
Published: 5th, July 2025 GMT
Wacce irin gudunmwa kafofin samun ilimi suke badawa ta yadda za a samu hanyar kara ilimi
A kokarin da ake yi na yadda za a samar da dama wadda kowa zai iya samun ilimi mai kuma inganci,ta kuma kafofin sadarwa na zamani. Hanyoyin koyo da kafofin sadarwa na zamani,kamar digirin da ake yi saboda yin karatun digiri ta kafar sadarwa ta zamani,da kuma a kasnce kamar ana cikin aji ne,saboda a ba dalibai wata dama wadanda kuma suka kasance daga wuraren da suka bambanta, manufa anan itace yadda suka zo daga wurare daban daban.
Alal misali,yadda aka samu tafarkin tsarin ilimi ta kafar sadarwa ta zamani,musamman ma digiri,wanda hakan ya ba dalibai dama su kammala iliminsu ba tare da bata lokaci ba,ba tare da rasa ingancin abin ba.Su wadannan tsare tsaren karatun suna taimakawa manya wadanda suke yin aiki,Iyaye,da kuma sauran al’umma wadanda suke da zummar ganin sun samu shiga tafarkin samun aikiand.Ta bada dama ga wadanda suke son samun damar yin karatu,ta hakan ne za su iya samun damar mallakar takardun sheda na digiri,a cin lokaci ba mai tsawo ba,wato kamar shi irin zabin yaba da dama abin bay a tsaya kan lamarin kashe kudade masu yawa ba, ya samu damar inganta ko samun ilimi mai zurfi wanda hakan wani mataki ne na samun daidaituwar bambancin da ake da shi yadda ake samun bambance- bambance na ilimi a a kasashen duniya.
Bugu da kari ire-iren su nayoyin kara karatu na kafafen sadarwa na zamani,suna taimakawa masu koyo su samu taimakon kasashen waje ko samun damar yadda za su gana da tsararrakinsu a duniya,kai harma su samu damar wani lokaci da zasu damar tattaunawa wadda zata taimaka masu.Irin ita damar idan aka same ta,tana tabbatar da kamar yadda shi ilimi wanda bai da wata iya da za ace kar ya wuce ta,bunkasa ilimi wata dama ce wadda kowa yake son cimmawa. Idan har aka samu damar yin amfani da fasaha, hakan yana bada muhimmaiyar dama ta samun samar da daidaituwar ilimin da ake da shi tsakanin wannan kasa da waccan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido.
An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje.
Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar da ingantaccen kulawa.
A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta dauki nauyin kula da lafiyar ido ga mutum sama da 500 daga Birnin Kano da sauran kananan hukumomi.
Shugaban kula da lafiya am matakin farko na ƙaramar hukumar, Alhaji Lawan Jafar, ya ce wadanda lalurar su ba ta tsananta ba za a ba su shawarwarin kula da lafiyar su, da magunguna, wa su ma har da tabarau, yayin da wadanda ta su ta tsananta kuma za a musu tiyata.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna godiya tare da yi wa gwamnati addu’a don samun nasara.
Shugaban tawagar likitocin, Dr. Kamal Saleh, ya tabbatar da cewa shirin ya samu nasara sosai.
Daga Khadijah Aliyu