Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
Published: 5th, July 2025 GMT
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp.এছাড়াও পড়ুন:
Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar Nijeriya
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sake fuskantar wani mummunan sakamako inda ta koma matsayi na 20, wato ƙarshen teburin gasar Firimiyar Nijeriya ta NPFL.
Wannan koma baya na zuwa ne bayan ta sha kashi a hannun Enyimba United a wasan mako na 11, wanda aka buga a filin wasa na Enyimba International Stadium da ke birnin Aba a Jihar Abia.
An rantsar da Samia Suluhu Hassan a wa’adin mulki na biyu a Tanzaniya An kashe ’yan bindiga 19 yayin wani hari a KanoƊan wasan Enyimba, Bassey John, ne ya fara zura ƙwallo a ragar Pillars a minti na 27, kafin Edidiong ya ƙara ta biyu mintuna kaɗan kafin a tafi hutun rabin lokaci, lamarin da ya nuna ƙarara cewa masu masaukin baƙi sun fi ƙarfin Pillars a wasan.
Sakamakon ya bai wa Enyimba damar hawa zuwa matsayi na 6 a teburin gasar da maki 16 daga wasanni 11, yayin da Sai Masu Gida suka sake komawa matsayi na 20, wato a ƙarshen teburin.
Wannan na nuni da cewa ƙungiyar ta Kano Pillars tana cikin tsaka mai wuya a wannan kakar wasan.