Kasar Iran Ta Jaddada Wajabcin Hukunta Gwamnatin Mamayar Isra’ila Dangane Da Ta’addancinta Kan Iran
Published: 5th, July 2025 GMT
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa Ta’addancin yahudawan sahayoniyya kan Iran laifi ne na yaki da ya zama wajibi duniya ta yi mata hukunci a kai
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi kira da a dorawa mahukuntan yahudawan sahayoniyya alhakin munanan laifukan da suka aikata a kan al’ummar Iran, musamman a lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare a birnin Tehran fadar mulkin kasar da sauran garuruwan kasar ta Iran.
A wani sakon da ya wallafa a dandalin X a yau Asabar, Baqa’i ya ce, “Harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a asibitoci da kurkukun Evin a ranar 24 ga Yunin wannan shekara ta 2025, wanda ya yi sanadin shahadar fararen hula da ma’aikata da kuma masu shigewa da yawansu ya kai mutane 79, yana cikin laifukan yaki da kuma keta dokar jin kai ta kasa da kasa.”
Ya yi nuni da cewa, harin ya afku ne a daidai lokacin da iyalan fursunonin ke taruwa domin ziyartar ‘yan uwansu, kuma sun makale a karkashin baraguzan ginin inda suka yi shahada sakamakon harin wuce gona da iri na jirgin saman yakin gwamnatin mamayar Isra’ila.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
Ya ce Sin tana maraba da kamfanonin dake fuskantar kalubale su tuntubi ma’aikatar ko hukumomi masu ruwa da tsaki, yana cewa, ma’aikatar za ta nazarci ainihin abubuwan dake faruwa da kuma bayar da damar fitar da kayayyaki ga wadanda suka cancanta. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA