Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila
Published: 21st, June 2025 GMT
Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv.
Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500.
Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci.
Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran.
2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyya Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa IbomMakamin ya faɗo kan cibiyar ne kafin wayewar garin ranar Lahadi, amma babu wanda ya ji rauni domin cibiyar ba kowa a cikinta a lokacin.
Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ziyarci wurin, inda ya ce, “wannan harin ne dalilin da ya sa Isra’ila ba za a taɓa barin Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.”
Idan ba a manta ba, Isra’ila ce ta fara kai hari kan Iran a ranar 13 ga Yuni, bisa hujjar cewa abokiyar gabar tata tana dab da ƙera makaman nukiliya.
Iran, wadda ta dage cewa shirin nukiliyarta don dalilai na zaman lafiya ne kawai, ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa a kan Isra’ila.
Hare-haren Isra’ila sun yi sanadiyar mutuwar wasu manyan masana kimiyyar nukiliya na Iran, da manyan shugabannin sojojin Iran, da fararen hula tare da lalata gidaje da tashoshin nukiliya da ababen more rayuwa.
Duk da cewa yawancin binciken cibiyar Weizmann sun danganci fannin gas magunguna da ilimin kimiyya ne, amma tana kuma da alaka da tsaro.
A watan Oktoba na 2024, ta sanar da haɗin gwiwa da babban kamfanin tsaro na Isra’ila, Elbit, kan “kayayyakin da aka samo daga halittu don aikace-aikacen tsaro.”
Cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, tana da ƙungiyoyin bincike 286, masana kimiyya ma’aikata 191, da daruruwan dalibai.
Iran ta sanar a ranar Juma’a cewa ba za ta tattauna makomar shirin nukiliyarta ba yayin da take fama da hare-hare daga Isra’ila.
Duk ƙoƙarin ƙasashen Turai na jan hankalin Tehran zuwa tattaunawa bai nuna alamun nasara ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
An sallami ƙarin ma’aikata 639 a tashar Muryar Amurka
Hukumar da ke kula da kafar yaɗa labarai ta Muryar Amurka (VOA) ta sallami ƙarin ’yan jarida da sauran ma’aikata 639 a ranar Juma’a.
Hukumar Kula da Harkokin Watsa Labarai ta Duniya ta Amurka (USAGM) ta bayyana cewa kawo yanzu an sallami ma’aikata 1,400 a wani bangare na shirin Shugaban Amurka Donald Trump na rage ma’aikata a hukumar zuwa mafi ƙarancin adadi kamar yadda doka ta tanada.
Hakan na nufin an kori mutum takwas a cikin kowane ma’aikata 10 da ke VOA a wata uku da suka gabata, a sakamakon wannan matakin Hukumar USAGM ta ɗauka.
Babbar Mashawarciya ga Hukumar, Kari Lake, ta bayyana cewa, “An aika wa ma’aikata 639 a VOA da USAGM da takardun kora a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da ya kamata a yi tun da daɗewa don kawar da dimbin ma’aikata cima-zaune da kuma rashin riƙon amana a hukumar,” in ji sanarwar da ta fitar.
Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila 2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyyaLake ta kuma tabbatar da cewa hukumar ta kasance “cike da jami’an da ba sa aiki komai, nuna son kai, da ɓarnatar da dukiya.”
Ta bayyana cewa wannan mataki na nufin USAGM yanzu tana aiki kusa da mafi ƙarancin ma’aikata 81 da doka ta tanada.
Ma’aikata 250 kuma za su ci gaba da zama a Ofishin Watsa Labarai na Cuba (OCB), wanda ke watsa labarai zuwa ƙasar Cuba mai mulkin kwaminisanci.
An lura cewa babu ko ɗaya daga cikin ma’aikata 33 na OCB da aka kora.
Wannan mataki mai yiwuwa alama ce ta kusan kawo ƙarshen wannan shahararren gidan rediyo VOA wanda miliyoyin mutane ke saurara tsawon shekara 50 a faɗin duniya.
VOA, wadda aka kafa a 1942 don yaƙar farfagandar Nazi, tana watsa shirye-shirye a kusan harsuna 50 kuma ta mutane miliyan 360 ke sauraron shirye-shiryenta a mako, a faɗin duniya.
A watan Mayu aka kori ma’aikatan kwangila kusan 600 na VOA.
Wasu ’yan jam’iyyar Republican a baya sun zargi tashar da sauran kafofin yaɗa labarai masu samun tallafin gwamnati da nuna son kai ga masu ra’ayin mazan jiya, suna masu kira da a rufe tashar a matsayin wani ɓangare na rage kashe kuɗin gwamnati.
Wata tashar USAGM, Radio Free Asia, wadda tuni aka rage ma’aikatanta sosai, ta sanar a cikin wani sakon imel ga ma’aikata a ranar Juma’a cewa tana aiwatar da karin hutun tilas a sassa daban-daban.
Ana ci gaba da shari’o’i daban-daban kan lamarin korar ma’aikatan na USAGM.