Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Rasha Don Daukaka Amincewar Juna Ta Fuskar Siyasa Da Karfafa Muradun Juna
Published: 21st, June 2025 GMT
Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Rasha don ci gaba da daukaka amincewa da juna a fannin siyasa da karfafa dankon zumunci na cin moriyar juna.
Ding ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
A nasa bangaren, Putin ya ce, duk da matsaloli da kalubalen da ake fuskanta daga waje, dangantakar Rasha da Sin ta samu ci gaba a dukkan fannoni, kuma ta kai matsayin kolin da ba a taba kaiwa irinsa ba.
Ya bayyana kudirin kasar Rasha na kara karfafa hadin gwiwa a aikace tare da kasar Sin, da yin aiki tare don samar da makoma mai kyau ga kasashen biyu da ma duniya baki daya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yar shekara 17 daga Yobe ta lashe Gasar Turanci ta Duniya
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya.
Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a Gasar ‘UK Global Finals’, sakamakon fintinkau da ta yi wa takwarorinta na ƙasashe daban-daban da ke jin harshen Ingilishi a duniya.
Wannan nasara ta lashe wannan babbar gasa da Nafisa ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a mahaifarta, Jihar Yobe. Nafisa ta wakilci Najeriya ne daga Kwalejin Tulip International College (NTIC), Jihar Yobe.
A wani jawabi da ya gabatar jim kaɗan da sanarwar lashe gasar, wani ɗan uwan Nafisa, Malam Hassan Salihu, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Yobe da Makarantar NTIC bisa irin gudunmawar da suna bayar har ya kai ga samun nasarar ’yar uwarsa a wannan babbar gasa ta duniya. Ya ƙara da yaba wa shugabannin kwalejin bisa ga yadda suke gudanar da karatuttukansu da hakan ne ta kai ga nasarar.
Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje Sanata Buba ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi kyauta“Tabbas wannan nasara da Nafisa ta samu da taimakon Allah (SWT) ne,” in ji shi, kuma nasarar wata babbar shaida ce ga abin da matasan Najeriya za su iya cimma idan aka ba su dama da goyon baya.
“Alal haƙiƙa wannan nasara da Nafisa ta samu ya zama abin farin ciki da alfahari ga duk al’ummar jiharmu ta Yobe da ma ƙasa baki daya,” in ji Malam Hassan.