Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan Iran
Published: 22nd, June 2025 GMT
Amurka ta sanar da kaddamar da manyan hare-hare kan wasu muhimman cibiyoyin nukiliya a kasar Iran.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an kai hare-hare kan wasu cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran, inda ya yi barazanar kai wasu hare-haren idan har Iran ba ta nemi yi sasanci ba.
Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban Iran Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a BornoA wata sanarwar da Trump ya fitar a jawabin da ya yi a talabijin yana ikirarin sun tarwatsa cibiyar, ya ce “hare-haren na soji babbar nasara ce.
Trump ya ce Amurka ta kai hare-haren ne a yankunan Natanz and Isfahan na cibiyar nukiliyar Fordo wurin da Iran ke aikin shirin bunkasa makamashinta na Uranium da ke can karkashin kasa.
A cikin jawabinsa Trump ya ce ko dai Iran ta nemi zaman lafiya ko kuma ta fuskanci mummunan bala’in fiye da wanda aka gani a kwanaki takwas da suka gabata.
“Amurka za ta sake kai wa Iran hari idan har ba ta nemi yin sulhu ba,” a cewar Trump.
Gwamnatin Iran ta tabbatar da hare-haren amma ta ce babu wani lahani da suka yi wa cibiyoyin nukiliyarta, sannan kuma ta musanta ikirarin cewa an tarwatsa cibiyoyin.
Hukumar makamashi ta Iran ta ce hare-haren na rashin hankali ne da suka saba wa dokokin duniya, kuma hukumar ta ce hare-haren ba za su hana Iran ci gaba da cimma muradin ta ba na samar da makamin nukiliya.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya la’anci hare-haren na Amurka yana mai cewa kasarsa za ta yi duk mai yiwuwa domin tana da hakkin kare ’yancinta.
Shi dai Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya taya Trump murna kan hare-haren, yana mai cewa “da karfin gaske da adalci na Amurka zai canza tarihi.”
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da hare-haren na Amurka, inda Antonio Guterres ya ce babbar bazarana ce ga zaman lafiyar duniya kuma mataki ne mai hatsari na kara rura wutar yaki, haka ma kasashe aminan Iran irinsu Cuba da Venezuela sun yi Allah-wadai da hare-haren.
Tun a ranar 13 ga watan Yuni ne Isra’ila ta ƙaddamar da hari kan Iran, tana mai cewa ta yi hakan ne domin kawar da shirin Iran na mallakar makamin nukiliya, bayan Firaiminista Benjamin Netanyahu ya yi iƙirarin cewa Iran na dab da mallakar makamin.
A matsayin martani, Iran ta ƙaddamar da hare-haren ɗaruruwan makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa kan Isra’ila, inda ƙasashen biyu suka ci gaba da musayar wuta ta sama, tsawon sama da mako ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Benjamin Netanyahu da hare haren hare haren na da hare hare
এছাড়াও পড়ুন:
Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji kan Najeriya matuƙar gwamnatin ƙasar ba ta dakatar da kisan da ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi ke yi wa Kiristoci ba.
A yammacin jiya Asabar ne Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta Pentagon da ta soma tsara yadda za a kai hari Nijeriya bayan da ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka a shirye ta ke ta aike da sojoji da manyan makamai cikin Najeriya don bai wa Kiristocin kariya.
Barazanar shugaban na Amurka na zuwa ne kwana guda bayan ya yi iƙirarin cewa an kashe Kiristoci aƙalla 3,100 a Nijeriya ba tare da ya bayyana takamaimai inda ya samu waɗannan alƙaluma ba.
“Muddin gwamnatin Nijeriya ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da dukkan tallafin da take bai wa Nijeriya nan-take, kuma mai yiwuwa za ta shiga wannan ƙasƙantacciyar ƙasar, cike da ƙarfin gwiwa domin kawar da ’yan ta’adda masu kaifin kishin Musulunci waɗanda ke yin wannan ta’asa,” in ji Trump.