Yau Alhamis, an bude bikin baje kolin kayayyakin kasar Sin da kasashen kudancin Asiya wato CSAE karo na 9, tare da taron cinikayyar kayayyakin shige da fice na Kunming na Sin karo na 29, wanda za a gudanar tsawon kwanaki 6, a cibiyar baje kolin kasa da kasa na tabkin Dianchi na birnin Kunming a lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin.

Baje kolin CSAE na bana ya kunshi mahalarta daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa da kasa guda 73, da fiye da kamfanoni 2500 da ke baje kolinsu, kana da halartar dukkan kasashen kudancin Asiya da kudu maso gabashin Asiya.

Baje kolin na wannan karo na ci gaba da amfani da taken “Yin hadin gwiwa da samun ci gaba tare”. Sannan rumfunan nune-nunen guda 16 sun nuna fasahohin masana’antun samar da kayayyaki na zamani, da makamashi mai tsafta, da aikin gona na zamani da dai sauran fannoni wadanda suke samun damar yin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen kudancin Asiya da na kudu maso gabashin Asiya.

An yi nasarar gudanar da baje kolin CSAE sau 8 a baya, inda sama da kamfanoni 20,000 na gida da na waje suka halarci baje kolin, kuma jimillar kudin kwangilolin da aka daddale ta zarce dalar Amurka biliyan 110.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Sakkwato Za Ta Kashe fiye da Naira Miliyan 200 Wajen Gyara Tashar Talabijin Ta Kasa NTA

Majalisar zartaswar jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da kashe kudade wajen ayyuka a sassa daban daban nufin tabbatar da amana da aka dora wa gwamnati.

 

Da yake karin haske ga manema labarai yayin taron da ya saba gudanarwa, kwamishinan yada labarai Alh. Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta amince da bayar da kwangilar gina dakin kwanan dalibai mai hawa daya a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, da za a kasha naira miliyan dari hudu da tamanin da bakwai.

 

Alhaji Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta kuma amince da gyaran sashen da aka kona na gidan talabijin ta Najeriya NTA Sokoto wanda kudinsa ya kai naira miliyan dari biyu da casa’in.

 

Danchadi, wanda ke tare da Kwamishinan Muhalli, Hon. Nura Dalhatu Tangaza, da kwamishinan ilimi mai zurfi, Farfesa Hamza Isa Maishanu, ya ce majalisar ta amince da naira miliyan dari tara da tamanin da biyar domin gyara titin Forces Avenue a wani yunkuri na sake fasalin hanyoyin jihar a jihar.

 

An kuma amince da naira miliyan dari biyu da ashirin da takwas don maye gurbin bututun ruwa dake karkashin kasa a kan hanyar Sultan Atiku-Aliyu Jedo don magance matsalar magudanar ruwa da ambaliyar ruwa.

 

Kwamishinan ya ci gaba da cewa, an ware naira miliyan dari da ashirin da biyu domin saye da rarraba itatuwa a fadin jihar da nufin yaki da kwararowar hamada da sauyin yanayi.

 

A bangaren addini kuma an amince da wasu naira miliyan dari da ashirin da biyu domin gyaran masallacin Juma’a na Minannata haka kuma an tsara kammala aikin nan da watanni shida tare da sauran amincewa.

 

NASIR MALALI

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15
  • Ƴan matan Najeriya Sun Lashe Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka
  • Gwamnan Neja Ya Bada Umarnin Sake Bude Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, Lapai.
  • Gwamnan Jihar Kwara Ya Hori Sabbin Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima Akan Kishin Kasa
  • Gwamnatin Sakkwato Za Ta Kashe fiye da Naira Miliyan 200 Wajen Gyara Tashar Talabijin Ta Kasa NTA
  • Dangote Ya Ɗauki Nauyin Bikin Baje Kolin Gidajen Afrika Da Mahalarta Ƙasashe 21
  • Babban Jami’in MDD: Kokarin Sin A Fannin Samun Ci Gaba Mai Dorewa Na Da Matukar Alfanu Ga Yanayin Duniya
  • Sauya Sheƙa: Sanatoci Biyu APC Ke Buƙata Wajen Samun Kashi Biyu Cikin Uku A Majalisar Dattawa
  • Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere
  • 2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa