Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-07-31@20:08:50 GMT

Hukumar Raya Arewa maso Yamma Ta Kai Ziyara Jihar Jigawa

Published: 8th, March 2025 GMT

Hukumar Raya Arewa maso Yamma Ta Kai Ziyara Jihar Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta ja hankalin shugabannin Hukumar Raya Arewa Maso Yamma  da su yi aiki bisa gaskiya da rikon amana domin samun goyon bayan gwamnonin shiyyar.

Gwamna Umar Namadi ya yi kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin hukumar karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada a gidan gwamnati da ke Dutse.

Ya ce, Hukumar Raya Arewa maso Yamma, ita ce mafi girma a cikin shiyyoyin kasar nan, a don haka bai kamata a fuskanci wasu matsaloli  ba daga gareta.

Namadi ya bukace su da su mai da hankali da jajircewa, tare da yin aiki da abubuwan da gwamnoni suka sa gaba domin samun nasara.

Tun da farko, Shugaban Hukumar, Alhaji Lawal Sama’ila Yakawada ya ce sun je ziyarar ce da nufin gabatar da kansu a hukumance da kuma neman tallafi da karfafa gwiwar gwamnati.

A cewarsa, an kafa hukumar ne da amincewar gwamnonin yankin, don haka ya zama wajibi a nemi goyon bayansu.

“Jihar Jigawa jiha cceda ke noma tare da jajircewa, don haka mun ga ya dace mu fara zuwa nan bayan mun ziyarci shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, domin samun goyon baya,” in ji Samaila

Alhaji Sama’ila Yakawada ya ce tuni hukumar ta samu bayanai kan bangarorin hadin gwiwa da jihar Jigawa domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewa.

Ya bayyana Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma a matsayin hukumar da ta fi kowacce hukuma a sauran ayyuka da jihohi bakwai, inda ya ce akwai kalubale da dama.

Shugaban, ya yabawa Gwamna Umar Namadi, bisa kokarinsa na yakar matsalolin da suka addabi al’umma, tun kafin ya hau kujerar gwamnan jihar Jigawa, kamar yadda  bayanai suka nuna.

 

Usman Muhammad Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati

Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati.

Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar.

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri  Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno

Bakori, wanda shi ne Kwamishinan Harkokin Noma na jihar, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa makarantu biyu masu zaman kansu ne kacal a faɗin jihar ke da cikakkiyar rajista da hukumomin da suka dace.

“Jihar Katsina na da makaruntun gaba da sakanadare na gwamnati huɗu da ke bayar da takardar shaidar difloma da koyarwa, sai kuma ƙarin 39 masu zaman kansu.

“Sai dai bincikenmu ya bankaɗo biyu ne kacal a cikin 39 suke da cikakkiyar rajista da hukumomi.”

Kwamishinan, ya kuma ce shida daga cikinsu na buƙatar gyare-gyare domin kammala rajistar, yayin da 22 ke aiki ba tare da rajistar ba.

“Ƙarƙashin sabon tsarin da muka ɗauka yanzu, ya zamo dole makarantun da ke bayar da takardar shaidar digiri su yi rajista da Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).

“Masu difloma kuma da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha (NBTE), sai masu koyarwa da Hukumar Kula da Kwalejin Ilimi ta Ƙasa (NCCE).

Bakori, ya jaddada cewa, duk makarantar da ta saɓa wa wannan tsarin, a shirye gwamnatin take ta rufe ta.

Sai dai ya yi wa ɗaliban da ke makarantun albishir ɗin cewa gwamnatin za ta tabbatar ta sauya musu makaranta zuwa masu rajista daga waɗanda ba su da su, idan buƙatar rufe su ta taso.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah
  • Kwara Ta Kwashe Mabarata Daga Titunan Jihar Su 94
  • Kwamatin Tantance Ayyukan Kananan Hukumomi Na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Isa Sule Tankarkar
  • Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
  • Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu
  • Shugaban SUBEB Yayi Alkawarin Bayar Da Tallafin Ilimi A Jihar Nasarawa
  • Gwamna Namadi Ya Naɗa Shugabannin Hukumar Hisbah Ta Jihar Jigawa
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Na Da Kwamitoci 30 Da Ke Sa Ido Kan Ma’aikatun Gwamnati
  • Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
  • ’Yan sa-kai aƙalla 100 da jami’an tsaro 30 sun mutu a bakin aiki a Katsina —Gwamnati