Aminiya:
2025-11-05@08:43:01 GMT

An yi ma’aikatan ƙananan hukumomin Gombe ƙarin albashin N5,000

Published: 21st, June 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da biyan ƙarin albashin Naira 5,000 ga ma’aikatan ƙananan hukumomi da Hukumar Ilimi ta Ƙananan Hukumomi (LGEA).

Ƙarin albashin zai fara aiki ne daga albashin watan Yuni na shekarar 2025

Wata sanarwa da Jibrin Yusuf ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Ahmed Abdullahi, ta ce cimma matsayar ne a wani taro na musamman da aka gudanar a ranar Talata.

Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikata tare da wakilan ƙungiyoyin kwadago da wasu manyan jami’an gwamnati.

Najeriya ta tura sojoji domin samar da zaman lafiya a Gambia Ministan Harkokin Wajen Iran ya isa taron Kungiyar OIC a Turkiyya

Ta ce an amince da ƙatin Naira 5,000 ga ma’aikatan har sai an kammala aikin tantancewa da ake gudanarwa a halin yanzu.

Shugaban Ma’aikata ya umarci Ma’aikatar Kuɗi daCi-gaban Tattalin Arziki da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace don ganin an aiwatar da wannan karin cikin lokaci.

Duk da wannan ƙarin, binciken da wakilinmu ya gudanar ya gano cewa har yanzu ma’aikatan ƙananan hukumomi 11 na jihar ba su fara cin gajiyar ƙarin albashi da aka yi ba.

Mataimakin Gwamnan Jihar, Dokta Manassah Jatau, tare da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago (NLC) reshen jihar, Yusuf Bello, sun amince cewa idan kuɗaɗen shiga sun ƙaru, za a fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 70,000 ga ma’aikata.

A yayin bikin Ranar Ma’aikata da aka gudanar kwanan nan, Yusuf Bello ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta fara aiwatar da biyan mafi karancin albashi ga ma’aikatan kananan hukumomi cikin gaggawa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ƙananan Hukumomi Ƙarin Albashi

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Kano Ya Yaba Da Matakin Da Sojoji Suka Dauka kan Matsalar Tsaron Tsanyawa

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar.

Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin da Babban Hafsan Runduna ta 1, wato GOC 1 Division da ke Kaduna, Major Janar Abubakar Sadiq Muhammad Wase, ya kai masa ziyara a Gidan Gwamnati Kano.

Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa da yadda sojoji ke gudanar da aikinsu cikin kwarewau, jajircewa da kishin kasa, tare da bayar da tabbacin ci gaba da hadin kai tsakanin gwamnati da hukumomin tsaro. Ya kuma gode wa Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu, bisa nada manyan hafsoshi masu kwarewa da suka himmatu wajen yaki da rashin tsaro.

Da yake jawabi, Janar Wase ya ce ya zo Kano ne domin duba yanayin tsaro a Shanono da Tsanyawa, inda aka yi hare-hare a kwanakin baya.

A cikin matakan tallafi, Gwamna Yusuf ya bayyana ba da gudummawar motocin Hilux guda 10 da babura 60 ga Rundunar Hadin Gwiwa da ke aikin tsaro a yankunan da abin ya shafa.

Abdullahi Jalaluddeen/Kano

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Matan 500 Za Su Amfana da Gwajin Cutuka Kyauta a Jihar Gombe
  • Gwamnatin Nasarawa Za Ta Gina Gadar Sama Da Ta Kasa A Mararraba
  • Gwamnan Kano Ya Yaba Da Matakin Da Sojoji Suka Dauka kan Matsalar Tsaron Tsanyawa
  • Tinubu na neman majalisa ta amince masa ya ciyo sabon bashin Tiriliyan 1.150
  • Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Fasahar Sadarwa da Tattalin Arzikin na Zamani
  • Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno
  • Abba ya umarci a riƙa gudanar da taron tsaro a ƙananan hukumomin Kano
  • ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo
  • Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa