Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna
Published: 19th, June 2025 GMT
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu na ziyarar aiki a cikin Jihar Kaduna.
Shugaba Tinubu na ziyarar ne domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar, Uba Sani ya aiwatar a tsawon shekara biyu da ya yi yana mulkin jihar.
Za a dawo da dukkan Alhazai gida ranar 28 ga Yuni – NAHCON Kotu ta ba da belin Natasha kan N50m kan zargin bata sunan AkpabioWasu daga cikin ayyukan da shugaban ya ƙaddamar sun haɗa da: asibitin ƙwararru mai gadaje 300 da gwamnatin jihar ta gina don bunƙasa harkokin lafiya.
Daga nan kuma shugaban ya ƙaddamar da cibiyar koyar da sana’o’i, da kuma motocin sufuri masu amfani da iskar gas ta CNG guda 100.
A cikin waɗanda suka yi wa Shugaba Tinubu rakiya sun haɗa da: Mataikamin Shugaban ƙasa na musamman kan harkokin siyasa, Sanata Ibrahim Masara, da mai taimaka wa shugaban kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin da wasu manyan jami’an gwamnati.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
এছাড়াও পড়ুন:
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’uSauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka dakatar ba sa halartar tarukan jam’iyyar.
An dakatar da su na tsawon wata ɗaya, sannan aka miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar PDP domin gudanar da bincike.
Waɗanda aka dakatar ’yan tsagin Wike ne, kuma sun raba ƙafa a rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaɓen 2023.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne, wata Babbar Kotu a Babban Birnin Tarayya, ta dakatar da PDP daga shirin gudanar da babban taronta da aka tsara yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron ba.
Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun ce rashin jituwa a PDO shi ne babban dalilin da ya sa aka kai ƙarar taron’ kotu.