An kashe matar aure, manomi ya jikkata a wani sabon hari a Kaduna
Published: 22nd, June 2025 GMT
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wasu ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.
A yayin harin, wata matar aure ta rasu, yayin da wani manomi ya samu rauni.
’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba SaniHarin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na daren ranar Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025, a ƙauyen Ungwan Sarkin Hausa da ke Rimau.
Ana zargin maharan sun gudu da shanun da suka sato daga Ƙaramar Hukumar Kauru.
A lokacin harin, sun kashe wata mata mai suna Misis Alheri Danzaria.
Sun kuma sace wasu mutum biyu, amma daga baya suka sake su.
Hari na biyu ya faru ne da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 a ƙauyen Kallah.
A nan ne suka harbi wani manomi mai suna Mista Iliya Barde, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gona.
An garzaya da shi asibiti inda yake samun kulawar likitoci.
Shugaban gundumar Kufana, Mista Stephen Maikori, ya ce hare-haren da ake yawan kai wa sun haddasa tsoro da damuwa a tsakanin mazauna yankin.
Ya buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa wajen ƙara tsaro a yankin.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ya ce zai bincika lamarin sannan ya bayar da amsa, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto bai yi ƙarin haske ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: hari Ƙauyuka matar aure
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato
Manoma a Jihar Sakkwato sun koka game da takin da gwamnatin jihar ta ce za ta raba musu don noman damina cewa bai kai hannunsu ba.
Duk da cewa an ƙaddamar da rabon takin kusan mako guda da ya gabata.
Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murnaGwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da shirin sayar da takin zamani da magungunan noma a farashi mai rahusa a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa domin bunƙasa harkar noma a daminar 2025.
Sama da buhu dubu 105 na NPK da UREA aka sayar a farashi mai rangwame.
Hakazalika, an sayi maganin kashe ƙwari da keken noma don raba wa manoma.
Sai dai manoma da dama sun ce wannan taki ba na noman damina ba ne, kuma har yanzu ba a fara rabawa ba.
Umar Yusuf, wani tsohon manomi daga Tangaza, ya ce gwamnati ta ƙaddamar da sayar da takin ne bayan damina ta kusa ƙarewa.
Kabiru Muhammad daga Kware, wanda ke da gonaki guda biyar, ya ce yana buƙatar taki amma ba a samun shi a kan lokaci.
Ya ce shirin ba ya zuwa hannun manoman gaskiya saboda ba a tsara shi yadda ya dace ba.
Muhammad Sale daga Illela ya ce ba wani manomi mai gona da ke jiran takin gwamnati, saboda duk shekara sai an makara wajen rabon taki.
Ya ce idan gwamnati ba za ta samar da taki cikin tsari ba, gara ta daina sayen shi gaba ɗaya, ta mayar da kuɗin zuwa wani aikin da zai amfani talaka da jihar.