Aminiya:
2025-08-06@06:42:54 GMT

An sallami ƙarin ma’aikata 639 a tashar Muryar Amurka

Published: 21st, June 2025 GMT

Hukumar da ke kula da kafar yaɗa labarai ta Muryar Amurka (VOA) ta sallami ƙarin ’yan jarida da sauran ma’aikata 639 a ranar Juma’a.

Hukumar Kula da Harkokin Watsa Labarai ta Duniya ta Amurka (USAGM) ta bayyana cewa kawo yanzu an sallami ma’aikata 1,400 a wani bangare na shirin Shugaban Amurka Donald Trump na rage ma’aikata a hukumar zuwa mafi ƙarancin adadi kamar yadda doka ta tanada.

Hakan na nufin an kori mutum takwas a cikin kowane ma’aikata 10 da ke VOA a wata uku da suka gabata, a sakamakon wannan matakin Hukumar USAGM ta ɗauka.

Babbar Mashawarciya ga Hukumar, Kari Lake, ta bayyana cewa, “An aika wa ma’aikata 639 a VOA da USAGM da takardun kora a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da ya kamata a yi tun da daɗewa don kawar da dimbin ma’aikata cima-zaune da kuma rashin riƙon amana a hukumar,” in ji sanarwar da ta fitar.

Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila 2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyya

Lake ta kuma tabbatar da cewa hukumar ta kasance “cike da jami’an da ba sa aiki komai, nuna son kai, da ɓarnatar da dukiya.”

Ta bayyana cewa wannan mataki na nufin USAGM yanzu tana aiki kusa da mafi ƙarancin ma’aikata 81 da doka ta tanada.

Ma’aikata 250 kuma za su ci gaba da zama a Ofishin Watsa Labarai na Cuba (OCB), wanda ke watsa labarai zuwa ƙasar Cuba mai mulkin kwaminisanci.

An lura cewa babu ko ɗaya daga cikin ma’aikata 33 na OCB da aka kora.

Wannan mataki mai yiwuwa alama ce ta kusan kawo ƙarshen wannan shahararren gidan rediyo VOA wanda miliyoyin mutane ke saurara tsawon shekara 50 a faɗin duniya.

VOA, wadda aka kafa a 1942 don yaƙar farfagandar Nazi, tana watsa shirye-shirye a kusan harsuna 50 kuma ta mutane miliyan 360 ke sauraron shirye-shiryenta a mako, a faɗin duniya.

A watan Mayu aka kori ma’aikatan kwangila kusan 600 na VOA.

Wasu ’yan jam’iyyar Republican a baya sun zargi tashar da sauran kafofin yaɗa labarai masu samun tallafin gwamnati da nuna son kai ga masu ra’ayin mazan jiya, suna masu kira da a rufe tashar a matsayin wani ɓangare na rage kashe kuɗin gwamnati.

Wata tashar USAGM, Radio Free Asia, wadda tuni aka rage ma’aikatanta sosai, ta sanar a cikin wani sakon imel ga ma’aikata a ranar Juma’a cewa tana aiwatar da karin hutun tilas a sassa daban-daban.

Ana ci gaba da shari’o’i daban-daban kan lamarin korar ma’aikatan na USAGM.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: koran ma aikata

এছাড়াও পড়ুন:

Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina

Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun riga mu gidan gaskiya a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda ya janyo ruftawar ginin gidansu a ƙauyen Dankama da ke Karamar Hukumar Kaita a Jihar Katsina.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na dare a ranar Litinin yayin da waɗanda ajalin ya katsewa hanzari ke tsaka da barci.

Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri

Bayanai sun ce wasu mutum huɗu waɗanda su ma lamarin ya rutsa da su an gaggauta miƙa su asibiti domin samun kulawa.

Magidancin da aka yi wa wannan babban rashi, Muhammad Sani Garba, yayin ganawa da manema labarai ya ce ba ya gida lokacin da tsautsayin ya auku.

“Wannan tsautsayi ya rutsa da mutum goma, amma abin baƙin ciki, shida daga cikinsu sun rasu. A halin yanzu, mutum huɗu suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi.

“Na ɗauki wannan a matsayin ƙaddara daga Ubangiji. Allah Ya jiƙansu, Ya sanya su a Aljannar Firdausi,” a cewarsa.

Daraktar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA), Hajiya Binta Dangani, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ma’aikatan hukumar sun ziyarci wurin da lamarin ya faru domin tantance halin da ake ciki da ɗaukar matakin gaggawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi
  • Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina
  • Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa
  • An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa
  • Gwamna Yusuf Ya Raba takardun daukar Aiki Ga Sabbin Ma’aikatan Gona Su 1 ,038
  • Gwamna AbdulRazaq Ya Amince Da Naira Biliyan 20 Don Gyaran Gine-ginen Makarantu A Kwara
  • Iran Ta Ce Ba Wani Ma’aikacin Hukumar IAEA A Kasar A Halin Yanzu
  • Gwamnatin Sakkwato Za Ta Kashe fiye da Naira Miliyan 200 Wajen Gyara Tashar Talabijin Ta Kasa NTA
  • Gwamna Abdulrazaq Ya Duba Titi Mai Tsawo Kilomita 49
  • Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura